← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 49

Sashe 20

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun safiyar ranar litinin dady yasamu sakon da yake Jira daga South Korea suna neman su domin yin interview anan reshen su dake Denmark dan haka dady yasa hannu akan Abdullah ne zaiyi tafiyar wayewar garin talata kennan zai bi jirgin Lagos domin ta Lagos zai zasu tashi , yakasance Abdullah cikin uzuri yake har gurin magriba da Kyar ya samu bayan sallar ishai ya tafi gurin Aisha shi da salis yaya yusif ne ya fito yake masa baya ai tana can gidan aunty Maryam Abdullah ya duba agogon sa yana da sauran lokacin ,yayi sallama da Yaya yusif suka wuce.

Tun yamma taje gidan aunty Maryam ita kuma tarike ta sai ta kwana dan haka sallar ishai kadai tayi ta nade a gado har ta fara bacci Aunty Maryam ta taba ta taje inji Abdullah ta Mike tana kallon aunty Maryam sannan ta dubi agogo tara saura kwata sannan ta Mike a hankali ta canza kayan jikinta .

Da sallama tashiga falon bakin yana tsaye daidai kofar da zata sadashi da ita hannayensa rungume a kirjinsa ya langwabar da kai a jikin bango ,bata ji amsawar tasa ba Amman ta lura da yanayin kallon da yake binta dashi ta dauke idanunta dan tarigada tasaba da wannan mayataccen kallon nasa a hankali yazo daf da ita ya zauna suka hada Ido ya gane har tafara bacci ,ya lumshe idanunshi yana mai tabbatar wa kansa muddin yasameta zai ji dadin rayuwa da ita ya fada a kasan ransa komai nata bata cika daukarsa me wuya ba , hasalima ita ba komai yada meta ba,duka Bai fi rabin awa da mintina da idar da sallar ishai ba Amman har tayi bacci takan sauka kawa rayuwar ta akan abubuwa da dama ,hakan yasa take sake shiga ransa Sosai da sosai , yanayin kallon yake mata yasa kirjinta yarinka bugawa , Abdullah yakira sunanta yace Aisha I love you ,I really love you please tell me do you love me? ........

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page13

Tayi shr batace komai,tashiga wani yanayi na daban, tarasa gane kanta meke shinrin farawa da rayuwata ta furta haka acikin ranta , Abdullah nasan ruguzamata zuciya da wayan nan idanun nashi masu frigita ta ZUCIYAR duk wanda aka kalla dasu, ta takasa amincewa da farinciki take ciki ko tashin hankali a lokacin guda km taji kamar ta tambaye shi ko zai iya amsa mata tambayoyin da suke cunkushe akasan ranta masu neman tarwatsa mata zuciya da tsantsar jiki "da idanu take binsa da kallo tanason taganu ko shima yashiga makamancin halin datake ciki " shima ita yake kallo ,yayi murmushin daman yasan bazata iya furta Kalmar daya nema daga gunta ba " , acikin zuciyarsa ya furta" OH" ni Abdullah tawa tasamini nashiga one chance , ya zuba mata manya idanunshi yace gobe zanyi tafiya ta dago dara daran idannuta ta kalleshi yasake yin murmushi yace a kallonki nagane tambayar ki , Aisha ni bazan yarda da wannan shr naki ba idan munyi aure kidinga kinmin magana ba gaskiya ya fada har da turo baki batasan sanda murmushin kufce mata ba shima dariya yayi Amman nasan abinda zan dinga miki zaki dinga yimin magana sosai ,ni kadai nasan abun.
Tasake yin murmushi yana kallonta kaunata na sake huda masa zuciyarsa, yadan gyara murya cikin natsuwa yace Aisha zanje interview a Denmark gobe zamu wuce Lagos ta can zamu tashi nan da kwana uku zan zauna interview Aisha kiyimin addu'a samun nasara ,dady ya zabi da inje in zauna masa ,har inajin tsoro Kar inyi disappointing dinsa ya fada yana kallon kwayar idanunta yanason tace wani abu ta fahimce abinda shr nasa yake nufi ta dan girgiza kai sannan ahankali tace zakayi nasara ya dan kalleta yace meyasa kika ce haka tace nasan zakayi nasara in Allah yaso "ya lumshe idanunshi yana mai jin tsanyi na ratsa kowani sashi na gangar jikinsa ko ba komai yau tazo masa da abubuwa masu mahimmanci daga gareta yace to Allah yasa Aisha bbu igiyar aurena akanki Amman ina da matukar kishi most especially akanki sati biyu kawai zanyi Aisha dan Allah kada kibari wani yashiga tsakaninmu Kar ki Amince da duk wani abu da zai bata tsakanimu a yanzu haka nasan ni ba wani zaunanne ne a ranki ba Amman ina sa ran idan muyi aure zaki soni , Aisha inajin tamkar in tafi dake idan muje can a daura mana aure Aisha ina son Allah yabani ikon Yi miki abunda zaisa ki so ni idan muyi aure .
Yadda yake maganar ya dada sa kirjinta yacigaba da bugawa..
. wuraren daban daban na halittar jikinta ke bude suna karfan sakoninsa" a zuciyarta tanason ta furta masa koda kalma daya ce mai mahimmanci da zai tafi dashi Amman hakan ya gagareta sai binshi take da shanyayun idanunta yayinda take sake kashewa Abdullah jiki , Abdullah ya dubi agogon hannushi karfe goma ta shige yace wai Kar aunty tayi fushi dani pas ten Aisha ta Mike cikin sanyi jiki uhmm har sauri kike ki tafi kibarni ko, ta sunkuyar da kai shima ya Mike yace akwai zanen company da guest house da zanyi acan shine Nike ganin zai tsayar dani har tsawon sati biyu ban da haka da next week zan juyo "tsaitin datake tsaye nan ya tsaya suna kallon juya ,ya suke hannuwanshi duka acikin aljihun wandonsa kara step uku yayi zuwa inda take har suna jin bugun zuciyoyinsu ya xuba mata idanunshi shidai yana son ta har bai san yadda zai misalta ba ,ita din wata sashi ce ta zuciyarsa yasake tsareta da Ido yace Aisha me zaki bani zan tafi ?
Tayi shr takasa cewa komai ,yace to ke me kike so daga gareni ?ta girgiza kai yayi murmushin yace gobe salis zai kawo sako har da Nasu yaya yusif dukansu ,ta kalleshi tana tunanin shi baya gajiya da kyauta ne ,ta tuna kyautar kudin da yayi mata ba a kai sati guda ba har tsoro suka bata da sauri ta rufe ledar ta wurga su bayan akwatin kayanta har zuwa yau bata kuma bi ta kansu ba. hakan nan bbu wanda yasan dasu yanayinta ya kalla ya gane tana son Yi masa godiya ne kawai ya share ta yacigaba yasake duba agogo yace let me go Aisha please say something for me wanda zai yimin rakiyya da ragemin yawan kewarki da zanyi har tsawon sati biyu ya zuba mata idanunshi yace I'm gona miss you Aisha please ya maimaita kusan sau uku kicemin wani abu mana ..... still tana tsaye kmr an sassakata ,yaga alamun bata da niyar yin magana yace ba zaki gaya min komai ba ko haka kike son na tafi ya furta hakan yana mai langwabar da kai to muje har gaban aunty nace ta roke ki kigayamin abinda zai dinga tayani bacci , ahankali yake matso ta tana ja da baya har ta mannu da bangon dakin yayin da zuciyarta ke dokawa tana harbawa gabadaya jikinta yagama mutuwa murus kafafuwa sungaza tsayuwa akaran kansu da Kyar ta iya tattaro dukan wani kuzarin dake jikinta ta furta I will Miss you too........ Hade da lumshe idanunta tana jin wani tsanyi na ratsa sansar jikinta yasake motsata sosai ya tsaya kawai yana kallon bakinta da yadda ya hudu ya furta Kalmar sai yaji kmr ya daura bakinsa akan nata mai abin sha'awa ya zuba bakin Ido yana mai cizan lip's dinshi gefenshi ta bi zata wuce dan baza iya jurewa kallon dayake binta da shi ba,ya kamo tafin hannunta cikin nasa ya matsesu gam wani shock suka alokaci guda yana musu yawo ajikinsu sakamakon haduwar da tafin hannyensu ,kokarin cire hannunta takeyi daga nasa batare da sun kalli juna ba sausauta rikon ta yayi ta zame hannunta ta saya dai dai bakin kofar ciki tana kallonsa yadda yake kallonta ne yasa tarinka jin wani abu atare da ita nan da nan ta juya ta shige dan bata son irin abun da tafara ji a game dashi din bata San iya lokacin da ya bata kafin yatafi ba, .

Tafiyar Abdullah da kwana shida maminsa tadawo Nigeria to abinda ta tarar ya maseefar gigitata domin dady yagama zartar da komai na batun auran Abdullah abin ya daure mata kai tana can dady na nan yana shirin yiwa Abdullah aure batare da itama an tuntubeta ba "tsawon kwanankin dayawa da dady ke nuna mata me za'ajira tunda Abdullah din yadamu da yarinyar kuma ta kowani bangaren yarinyar tayi illa daya gareta shine su din bawa wasu bane "ya nuna mata wannan ba wani abu bane tunda Abdullah yana son yarinyar bbu abunda zai gagara"mami tace Amman auren farko daza'atabayi a gidan nan yadace ace Yar manyan mutane zai aura koma ba haka ba a samu wacce akasan halinta ciki da waje ba irin wannan ba dan ni halin danaji daga bakin mutane batamin amatsayin matar da Abdullah zai aura.

Dady yayi murmushin to ke bakisan mutum da shi da kansa bai san yadda halinsa yake ba sai mutane sun fada ,to duk yadda dady ya bullo mata sai tace ba haka ba ,akarshe yace shi kam yariga ya gama magana ,in Allah yaso Abdullah bashi da wata mata sai zabin ransa sai kuma idan bangaren yarinyar ne suka ki.
Ran mami in yayi dubu to ya baci kwata-kwata a wannan taki jinin yadda dady yake mata musamman akan Abdullah Dr sagir ta fara sa aka nemo mata ta tunhumeshi akan maganar yarinyar da Abdullah yake nema iya abunda yasani shi ya fada mata to shi din yana da sauran kima a idon mami "Amman salis kuwa fata fata tayi masa ta kuma rantse akan idan har ta kamashi yana da hannu a hadin Abdullah da yarinyar nan to ya kawo karshen aikinsa . domin wannan karon bada salis Abdullah yayi tafiyar ba tare da security din dady sukayi RK da Immanuel shima (SS)ne na dady hatta part din Abdullah mami da kanta taje bbu wani abu data samu na game da yarinyar .
Chapter 20 · 0% Book details