← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 49

Sashe 15

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tayi murmushin karfin hali ok irin rayuwar da zamuyi kennan idan muyi aure ina son haka muddin zamu kasance matsayin miji da mata I said get out in my site "yasake fada cikin tsawa tsawa .
Tasake yin murmushi sannan ta juya tana juya masa mazaunai ta fice Abdullah yaja tsaki stupid girl kawai "ya fada sannan yabi bayanta ya sanyawa kofar key ya shige ciki ya duba agogon sa shadaya har ta wuce ya raya aransa duk inda zuciyarsa take tana can jikin Inna ,ta dade da yin bacci ba irin faiza ba, tsaki ya ja ya shige toilet ya sakarwa kansa shower ya gama ya dauro alwala don yanzu babban burinsa ya fuskanci ubangiji da matsalar sa ko zai samu saukin damuwar sa".

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 9

Part uku ne acikin gidan na dady ne daga dan gaba sai na Abdullah sannan na mami daga can barin ita da su teema a hade sai dai su teema suna sama yayin da mami ke kasa sai Kuma ragowar BQ na masu aiki gidan ,gida ne da aka shimfida shi tamkar baa son ciwon naira ba"dan tun daga dakunan masu gadi gidan "farkon shigowa zaka gane masu gadin suna hutawa da jin dadi parts din Mami kawai aka daura sama na su teema "dan haka in dai kana saman balcony zaka iya hange kowane part na cikin gidan da duk mai shigowa tundaga get saboda haka duk wani shige da fitan Abdullah akan idon faiza yake tun zuwan ta gidan ta gama karantar yadda Abdullah ke da matsayi acikin gida .kmr da wasa taji teema na cewa ai mami tace tayi wa dady maganar aurenku da bros shine dalilin kafa idanunta akan al'amarin har zuwa yau da taga shigar Abdullah part din dady tsammaninta maganar sukayi shine dalilin dayasa ta binsa part dinsa .

Kissa da iya kwantar da kai idan mutun yanason abu, wannan sai dai mutun yayi cos wajen su faiza tamkar zata yiwa mami sujjada wajen biyayya hakan ya dada birge mami har yasa tasaki jikita sosai da yarinyar yawan ci duk wata cima ta Abdullah faiza tasani Kuma tare da ita ake shirya komai mami ta bayar da umarnin a dinga koya mata "mami da kanta takira Abdullah ta dada tabbatar masa da maganar auren su da faiza bbu fashi iya tunanin mami aure be bai damu Abdullah ba shi yasa baya wani damuwa da zance faiza" Amman tasan komai dai abin sa idan an daura masa ita bazai ki zama da ita ba .

Faiza ta tsinci kanta da dana sanin fitar da maitar ta fili akan Abdullah dan haka tashirya masa text na ban hakuri gashi sati daya sukayi da mama hafsa sai gashi har ta zarta sati 2 ita kanta muddin zata ci gaba da zama a gidan tana ganin Abdullah ta gwamace ta rasa karatunta da duk wani abu mai mahimmanci na rayuwar ta" Amman ta canza shawara dole ta tafi a Yan kwanankin nan ta koma tasawa mama hafsa kuka koma yaya zaayi ita dai tana son ta mallaki Abdullah dan tagane ita kadai ke haukarta .

Tun dare hadari ke daure a garin yayin da Werther garin gabadaya tacanza sakomakon iskar dake kadawa Amman ba'ayi ruwa ba sai wayewar garin lahadi aka sharara ruwa musamman dayake ranar hutu ce sai wajen 12 tukun ruwan ya dauke gari yayi tsanyi ni'ima yasauka a koina, mami tasanar wa Abdullah tafiyar faiza gobe Monday tana kuma da bukatar siyyayar wasu abubuwa dan haka da Abdullah take son suje tare ya tayata zabe abunda take so, bbu wani zance musu a maganar mami ,Amman ya gwamace ta rufe shi da duka ko ta hada shi da wani aikin wahalar akan wannan fitar . Sai dai yayi kokarin dane bacin ranshi ya amsa mata, karfe hudu daidai fitar ta kama yayiwa amina waya tashirya su fita tare ko kadan ba haka faiza taso ba taso abarta daga ita sai shi a mota, sai da suka shiga mota ita da amina sannan ya fito daga part dinsa da waya a kunne yana magana .faiza ta zuba masa Ido sosai ita dai kamar ita kadai take ganin kullun gari yawaye sai yakara kyau da kwarjini fiyye da ko yaushe Yar rashin kibar da bai daita, yasa kowace shiga yayi take masa kyau " sanye yake cikin kananan kaya masu colour ja da baki sai farin glass daya manna a idonsa yakaraso jikin motar tare cire wayar sannan ya kashe salis ne ya bude masa dayar mota yashiga ya rufe yashiga ya tuka yayinda musa ya tuka su faiza suka biyo bayan su gabadaya ranta ya gama baci ita da taso Abdullah din ne ya tuka su daga ita sai shi "sai gashi kusan mutun hudu akan uzirinta daman ita sam jininta bai hadu dana salis ba saboda yadda taga yana kaf-kaf da Abdullah din duk inda yasa kafa yana binsa "shima Abdullah yaso yadda ni'imar garin tayi masa dade yakasance cikin nishadi da tarin farinciki Amman duk ransa a bace yake tun fitowarsa daya lura da mayataccen kallon da faiza ke masa Abdullah daga cikin mota ya zubawa waje Ido ai ko idanunshi yayi arba da wasu dattijai guda biyu suka shige su yace salis stop the car .

Salis yayi gaba ya daidaita yayi parking ganin su tsaya ne yasa musa tsayawa Abdullah ya murda kofar ya fito ya karasa inda suke yana cewa musa suyi gaba kafin su karaso salis yakaraso da wata jaka ya mikawa faiza ya koma mota yayin da Abdullah ya dubi dattijain, har suka kure faiza na waigensa tana mamaki musamman da taga bai koma mota ba yacigaba da tafiya . Abdullah ya riske mlm abu da abokinsa bbu wani abu da ya Dame su ,suna tafe suna hira kamar daga sama mlm abu yaga Abdullah yakasa boye mamakinsa yana dariya Abdullah shima murmushin kawai yake ya rusuna ya gaishe su sunan tsaye har salis yakaraso da mota da hanzari shima ya fito har kasa ya gaishe su Abdullah ya karbi kayan hannun mlm abu ya bude musu mota yace Bismillah.mlm abu yace ai munzo gida ma Abdullah yayi murmushin yace kuyi hakuri baba ku shiga mukarasa daku .

A mota hira sosai tsakanin su har sanda aka sauke mlm dauda yayi godiya mlm abu yayi su sauke shi shima anan" suka ki har gida suka kai shi ,salis yayi parking a gefen titi sannan ya dauki ledar baban yayi gaba yayin da Abdullah da mlm abu suka Tako ahankali suna hira har zuwa kofar gida,mlm abu yace kadakata a kawo maka taka tsarabar nima ya'uri mukaje tun jiya . Abdullah yayi murmushin yana girgiza kai ni na gode baba.

Aisha kuwa tun azahar taje gidan aunty Maryam ta karbo sako saboda gobe zasu tafi ka'oje aunty Maryam tabata kayan su saifu tace abawa kannen hadiza makotansu dan haka tana isowa kawai tashiga tabawa babarsu hadiza bata wani bata lokacin ba ta fito har tazo soro hadiza tabiyo ta ahankali tace yaya Aisha da daddare idan mamana tayi baccin nan nata zan dibo kayana in kawo miki da safe sai in zo kawai mutafi ko bata sani ba.bata tsaya jiran amsa ba ta ruga da gudu ta koma kan aikin da akasa ta"Aisha na dariya ta fito kawai idannuta suka sauka akan Abdullah shima yana dariya mlm abu yadage sai ya tsaya an bashi tsarabar sa.
Chapter 15 · 0% Book details