← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 49

Sashe 36

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 27

Da hanzari Abdullah yashiga dakin "har kan gadon inda take zaune a takure ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsam a fadadan kirjinsa" ahankali ya kai bakinsa cikin kunneta am sorry.... am sorry.... my Aisha na barki ke kadai ko tun safe na shigo kina bacci naje naga su mami ne "ya matse a jikinshi sosai har suna jin numfashin juna sannan ya dago fuskarta yana kallon kwayar idanunta duk batayi kuka ba Amman da ganin idanunta ya gane bata samu ishashen barci ba. ya sake saita bakinshi daidai kunneta ya rada mata wani abu wanda har yasa ta janye fuskarta daga hannushi . yayi dariya sannan ya ziro kafafunsa daga kan gadon tare da fadin kin shirya ko? Sai muje muyi breakfast

Ahankali ya sake juyo wa yana mata kallon tsab idai har ba idonsa bane yake masa gizo sai yace tun kayan jiya datazo dasune ajikinta.

Ya sake kallonta tabbas su din ne Kuma ko fitar da yayi bai sa ta tashi tayi wanka ta gyara ba .ya dan zubawa jikinta Ido zuwa wani lokaci sannan yayi murmushi gefen baki.a hankali yace wayyo Allah ita da kanta ma bata yarda da kanta ba, Kuma tun a jiya ya lura da kayan sun da meta.
dalilin haka ma ya dada sawa ya bar mata dakin dan ta samu ta canza wasu yasa hannu ya kara jawota yana Yi mata dariya yasan lallai zai dan Sha wuya wannan yanayin Nata" yana matsa mata hannu ya kira sunanta bata amsa ba Amman ta dago da kanta yace idan munyi breakfast zanje gidan Dr sagir domin a yau din nan zamu wuce Abuja dan ta can zamu tashi idan na fita sai ki shirya duk da kaya biyu ya isa shima don zamu bi ta Abuja ne .

Ahankali ta zare hannuta daga gareshi tana narke fuska ta kallonsa yace mhm ko kina so in dawo in shirya ki da kaina ? Tayi saurin girgiza kai sannan ahankali cikin tsanyi murya tace tare zamu tafi ..

Yace yes mana wazan barwa ke hade dage mata girasa daya ...da sauri ta hau girgiza masa kai "tace Abdullah dan Allah kayi hakuri ka tafi kabarni anan ,ni zan zauna har ka dawo, bai tsammaci jin haka daga bakinta ba" ya dora hannunsa kan nata cikin sanyi murya yace me yasa bazaki bini ba Aisha kina ganin zai yiwu ina can wata kasa zuciyata na nan ,ban san halin datake ciki ba" please Aisha kada ki min haka ki tausayawa ZUCIYAR MASOYINKI yana sake matse hannayenta cikin nasa" ita kam zance tafiyar su tare ne ya tsorata ta . dama taji wai. Amman bata zaci da gaske bane" tace dan Allah kayi hakuri kome kake so zanyi Amman ni dai ka barni anan in yaso sai a samo wani mu zauna tare" tuni idanunta sun gama ciciko Jira kawai take taji me zaice .

Abdullah yayi shiru ya xuba mata Ido kawai yana kallon yadda take furta magana duk ta gama kashe masa sansar jiki ko kadan ita wannan yarinyar bata san wani abu rikici ba a rayuwata "Amman ita gashi gabadaya maganganunta na neman rikita masa lisafi. ya lumshe idanunshi da suka fara kadawa ya sake kallonta dasu ahankali cikin kalar tausayi yace Aisha saboda ba Kya sona shi yasa baza ki bini ba ko ? Ya nuna kansa da yatsansa daya

A frigice ta kalle shi a idanunta ya karanci ba haka take nufi bai sanda yasaki hannuta yayi rigingina akan gado tare da runtse idanunshi gam anan wancan ga wannan tun kafin ya aureta a duk sanda yake tare da ita yakan manta da duk wata damuwarsa" ya dinga jin wata ni'ima a tare dashi har sai sun rabu hakan yasa shima ko kadan baya son ya ganta cikin wani hali. yadda ta nuna a yanzu yasan tabbas bata son tafiyar su tare ya karanto haka sosai atare da ita. shirun daya yi mata yasake tsoratata" tana so tayi masa magana Amman gabadaya bata da kuzari .

Sallama suka jiyo wanda Abdullah a hankali cikin sanyi jiki ya tashi ya fita. aunty Maryam ce da yara tare da kulolin abinci ya gaishe da aunty batare da ya wani tsaya ba saboda yanayin daya tsinci kansa ya wuce dakinsa .

Zuwan aunty Maryam yasa ta dan sake "taji tamkar ta sami wani security ne "nan da nan tafada wanka yayin da aunty ke ta fada da tunhuma yaya ta ganta a haka .

Sha biyu ta gota Abdullah ya sake fita" Aisha kara sake jiki tayi sosai abunta, har take sanarwa aunty zance tafiyar da yayi mata .

Maganar dai tafiya dady yarigada yayita, dan ma kusan angama komai na tafiyar tasu Abdullah zaune agaban dady . Inda yake sanar da dady da batun Aisha ta zabi zama anan akanta bishi .
Sai Dady ya gama ji komai sannan ya kalle shi "da kyau duk sai yaga hankalin Abdullah din ya rabu kashi kashi. yayi murmushi karfin hali sannan yace to me akayi kennan ,idan har baku tafi tare ba , yasake yin murmushi zanzo gidan naku da kaina .

Abdullah ya amsa sannan acikin zuciyarsa yana mamaki dadynsa. dady yace shabiyu ga wannan watan hutun ka zai fara dan haka idan doctor ya sallameka, kana iya wucewa duk kasar da kuke bukata ..
Ya amsa da to daga nan gurin Dr sagir ya wuce da salis ya bar RK a can gidan .

Manage please.....

kumin uziri rasuwa akamin , .dan haka zan rinka kokarin ko read more daya ne kunasa mu🙏🏻🙏🏻🙏🏻

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 29

Da sauri Abdullah ya dago idanunshi yana kallon mami ,ta daga masa kai alamun haka take nufi "tuni hawaye ya fara zubo masa a karo na biyun daya zubo masa a jin abinda ya danganci farincikinsa" na game da auren sa da Aisha ahankali yace thank you mami thank you mamina ..... tacigaba da murmushi ,su teema ma gabadaya suka hau murna ita kanta mami taso su bar tafiyar sai zuwa gobe domin su dan kara sakewa, minal tace bros idan kuntafi Kuma sai yaushe zaka dawo mana da aunty mu. yace ba dadewa zamuyi ba zamu dawo, mami ta karfa Allah ya dawo da ku lafiya ya tsareku...

Teema ta zagayo daga bayan mami tana dariya tace Ameen maminmu..
Mun gode ,Nan Abdullah ya kwanta a gabanta ji yake tamkar ya dauko Aisha itama ta zauna a cikinsu ,anan yayi sallar la'asar har kusan biyar suna tare" duk da rabin zuciyarsa na gurin Aisha bai san a halin da take ciki ba itama, sai da dady ya yo masa waya sannan ya fito ya iske dady a bakin get ya shiga part dinsa agurguuje sannan ya fito ya samu dady tare da direver da zai kai su airport har bakin get su minal suka biyoshi yayin da mami ke makale can jikin Window dakin ta tana hangensa ..

Sai karfe shida suka bar kebbi shi da Aisha da RK .

Kwanan su biyu a tsohon gidan su, na Abuja inda anan ne taga ainihin hotunansu na family shi. dady da mami sai kannensa tun ma yana teenage dinsa kafin Tafiyarsa oxford anan taga inda Abdullah ya samo kyau har gidan wani friend dinsa ya nema suka je wanda sukayi secondary school tare alokaci suna matasa shima ya dade da yin aure har da ya'yansa biyu .
Ranar laraba suka bar Abuja da daddare suka isa Germany karfe shadaya agogon can gabadaya su a gajiye suke duk da sun dan sami bacci ,a abuja har kusan shabiyu basu yi bacci ba har Abdullah ya fito daga wanka da rigar wanka ajikinsa tana zaune har yanzu a gefen gado "ya dubeta yayi murmushi ya dauki fam dinsa yace idan kinshirya ina falo kisame ni sannan ya fita ya barta .
Chapter 36 · 0% Book details