← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dady ya numfasa ya riko hannunshi cikin nasa yace Ab..dul..lah..maminka zata so duk abinda kake so ni nasani ko ba dade balle ita wannan yarinyar dabance acikin zuciyar Abdullah dinta ,kuma gashi yar'uwa Mafi kusanci agareka Abdullah ya zubawa dady Ido dan bai fahimci komai dady yake nufi ba in baka manta ba na taba sanar da kai ina da kanwa maimuna Kuma ta taba zuwa lokacin kana oxford to itace mahaifiyar. Aisharka ...jikin Abdullah yayi sanyi sosai saboda tuna yadda matsayin dady yake Amman yabar su cikin halin rashi Amman me shi duk yadda takasance daidai ne awajenshi dady yace babu abunda zance maka Abdullah saboda kai ne tsanin sake hadani da yaruwata har yanzu Abdullah dady yake kallo. dady ya numfasa sannan yace ni dai burina ka kwantar min da hankalinka maganar mami kaajiye a gefe bbu abunda zai faru kacigaba da farincikinka kaji .. Abdullah ya daga kai dady yace yauwa ya dubi agogon dake manne a bango yace kaje ka kwanta goma tayi idan bbu wani dalili bana son ka dinga wuce goma baka kwanta ba Abdullah ya amsa ya Mike yashige ciki dady yabishi da kallo har ya bacewa ganinsa sannan ya sauke ajiyer zuciya hadisin ne guda na annabi (saw) JUBULATILKULUBI ALA MAN AHSANA ILAH cewa zuciya an Gina tane akan son me kyautata mata , Abdullah bai san musu ko wani gajiyawa akan iyayensa hakan yasa zuciyarsu takafu akan soyayyar shi" dady ya lumshe idanunshi yana tuna can wani zamani daya shude baya da abinda mahaifinsa ke yawan gaya masa yace ishaq Allah ya albarkace ka kai ma Allah yabaka me Yi maka yadda kayimin dady ya bude Ido yayi murmushin ya shiga yiwa iyayensa addu'a ..

Idan badan dady da kansa ya sanar masa aurensa da Aisha ba da bazaiyarda ba wai da gaske shi din ne zai auri Aisha kuma ita din wata shashi ce gareshi" shi ko wani irin aikin alkhari ya taba yi arayuwarsa . Amman da ya tuna rahmar Allah tana dayawa ,ya fiso ya farka daga dogon tunanin daya tafi yagansa a gadon asibiti Amman ina komai a zahiri yake ganinsa ..
Yarinka kallon AV daurin auresa yana karantawa har yazo kan sunanta Aisha abubakar bahindi full name dinta kennan ya fada hakan a ransa yayinda ya hangota ta cikin katin tana masa dariya shima ya dinga mata daga can ya sauke katin ya dinga wa kansa murmushi wautarsa a fili ya tabbarwa ransa yana matukar sonta dayawa har bai san yadda zai yi ba shida kansa yasan rasata daidai yake da tarwatsewa zuciyarsa ,Kuma yasan tabbas in bai mutu ba to zai shiga mummuna rayuwa ,, ya sake gyara kwanciyar sa yana kallon celling dakin, tsawon lokacin rabon daya ganta har zaman sa asibiti bbu wani abu da yake gani wanda yake da alaka da ita ko ya danganceta Amman kullun ya tashi sai yaji soyayyarta taninku a zuciyarsa "yau ta zo masa da abubuwan dayawa na farinciki a hankali ya furta da wa zan raba wannan tarin farincikin nawa ? ya runtse idanunshi ya sake bude su har yanzu ita yake gani tanayi masa gizo a dakin a hankali ya furta sunanta Ai....sha.. kina son kina neman zarar da Abdullah, gabadaya giyar soyayyar ki tayi sikater din brain dina yasa hannu ya dafe saitin ZUCIYAR sa dake dokawa da sauri da sauri yana Jin kmr zata basa masa kirji ...

Washegarin da karfin sa sukeyi komai tare da dady wanda har ya dinga bawa dady din mamaki..barin dady yayi agida byn yashirya ya fita yiwa Aisharsa siyayya duk wata sutura da kayan kwalliya an hada ,fanin Kannan kaya kuwa ba'a maganar su dan zagewa Abdullah yayi yarinka zabawa Aisharsa da kansa saboda rayuwar can ta zame masa jiki yawancin duk kayan da yan matan can ke rayuwa dasu ya rinka kwasar mata wanda anan Germany zai barsu, kayan bacci kuwa ba kunya yarinka daukan masu shara shara da bayyanar da duk wata surar ta dan Adam kusan wunin ranar a shopping yayi spend din shi ..

Da safiyar talata jirginsu ya sauka a Nigeria gabadaya I .m sidi magaji industry ranar hutu ake a dalilin saukar managing director Abdullah ishaq Muhammad ...

Idan ka dauke ramar Abdullah yayi zaka masa kallon Germany din tasa ce, ya kara kyau fiyye da wanda yake dashi, fatar nan tasa ta sake gogewa ya kara kyau me yiwa ko Werther garin ce ta karfeshi baza kace ruwa biyu bane shi Amman fa fuskar nan tasa tamke take kmr koda yaushe Kuma daman can kullun kaganshi a haka take sai aikin cizan lip's" har kana hango lobowar dimple dinsa a duk sanda ya ciza lip's dinshi" haka nan yawanci ma'aikatan company dinsu tare da su aka taryo shi ..

A falon mami ya fara sauka kasancewa dady bai fadi dawowar tasu a ranar ba shi yasa duk wani girke girke duk a lokacin su minal da wata kawarta ikram suka tashi sukayi domin teema da faiza sun fita mama hafsa na gidan suna tare da mami duk ta rude domin dai ga Abdullah ya diro kuma shirin da aka basu ana son daya diro kasar amai amfani da abubuwan ya fara aiki a ranar da ya dawo gashi faiza bata nan ..
Mama hafsa kuwa kmr tayi hauka tai ta zagin faiza hade da tsine mata a zuciyata ,daman wannan sirrin da za'a yi yanzu shine wanda zai karkato musu da hankalinsa domin duk wadancan da suka zo da su na da ,sun tashi daga aiki wa'adin su yakare tunda ba su aiwatar da su ba a lokacin da ake so sai gashi yau din ma abun yana neman fin karfin su domin dai bbu yadda mama hafsa zatayi hatta abinci ma a gaban mami yaci ai kuwa faiza ta sha zagi iri iri gurin mama hafsa sai dare suka dawo dan daga inda suka je ma wani gurin nufa.....

Abdullah yayi matukar mamakin yadda ya tarar da mami ba tare da wata damuwa ba har ishai suna tare da dady sannan ya umarce shi da yaje ya huta shikam ba haba ya so ba ...

Sai a wannan daren ne dady ya zubewa mami katunan daurin auren a gabanta kuma yake sanar da ita yace kada ma tasamu damuwa duk inda take tunanin zata aika shi tunin ya riga ya aika yana tunanin ma wajen gobe wasu zasu fara wuntsulowa gidan ..
Da farko dai mami bata fahimcesa Sosai ba sai daga baya ta kalli dady tamkar zatayi kuka tace daman abinda kuka shirya min kennan kai da danka dady yace bbu ruwan Abdullah ciki shima yadda kika tsinci maganar haka yaji ta.. mami tayi shr tasan wata fuskar tafi gaban mari".banda haka wlh da baza ta yarda da wannan auren ba komai zai faru , dan yanzu ta soma tunanin da wuya in dady yasan ko wacce yarinyar "da Abdullah zai aura" ta sauke naunauyen hadiyar zuciya sannan tace yanzu ko Abdullah ba jinina bane ya dace ace sai yau za'a sanar da ni yinin gobe da jibi ,gata kuma daurin aurensa maganar taso hassala dady dan duk abunda ta shuka agidan yaruwarsa yasane yashare bashi da niyyar tunkararta da maganar Amman tana neman harzuka shi dan haka shima cikin zafi da kausasa harshensa yace bayan kin dauki zafi da yarona in ma ansanar miki me zakiyi? baya ki damawa mutane lissafi sannan yadan sausauta murya ya shiga gaya mata yadda sukayi da doctor jack mami ta numfasa dan jin bai sako wani zance can ba, tace yanzu idan Abdullah yaro ne bai hango ma kansa abinda aka hango masa ba kai ba zaka hango masa ba irin gidan da Abdullah yadace ya nemi aure kennan tana kallon cikin idon dady, duk da a tsorace take . maganar sakamakon kallon dataga yana jifan dashi ... Dady yace uhmm anzo gurin ....da hanshi ya dakarta daita...... daka malama banason shirme da shashanci "kar fa kidauka bansa komai ba , alhalin ina sa ne da abunda nike kawai dai ina raga miki sanadin abubuwa dayawa Amman na lura baki san da hakan ba ,ok diyar yaruwarta wa ce bata dace da dana ba, sai ta hafsa yarwarki ko? jikin mami ya dauki rawa taso ma inda inda aa..Aa..ni fa ba haka nake nufi ba ok ya kike nufi" fahimtar dani ina son sani hankali yayi matuka tashi". shikenan abunda take gudu ya afku ya zuba mata Ido alamun ita yake Jira .. ...

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 22

Dady Ya sausauta murya yace haba mamin Abdullah wai me wayan nan bayin Allah suka Yi miki kodan sun kasance su bawasu bane ? Hanjin cikin su ne kawai ba a caje ba "Amman komai nasu sai da aka bincika Amman ajiye yan'uwantaka kina tsammanin kai tsaye zan bar Abdullah ya nemi aure ai ance sai kayi kuskure a filin yaki ka tsira Amman idan kayi kuskure gurin neman aure ka fadi mami ta numfasa to me yasa sanda na kawo maka zance faiza baka Kuma bi takai ba me yasa ita ma ba'a bincika an ga nagarta ta ba" saboda ita ba family dinka bace ..Dady yayi murmushin a zuciyarsa su fa mata duka sunansu daya ,a fili yace Abdullah fa ba yaro bane yasan ciwon kansa. experience dinsa ya wuce ace za ai masa wani zabi sabanin son zuciyarsa yana da kyau kiyi masa uziri a matsayinsa na da namiji.ita fa wannan yarinyar na bincike ta tun bansa wacce ba dan ki ajiye duk wata dangantaka abinda Abdullah ya nuna yanaso shine farincikina "har karfe daya na dare dady da mami ba su runtsa ba duk akan maganar Abdullah ,domin taji zafi abinda akamata sosai ganinta ammata fin karfi ne kawai shi da kan sa dady yasan ammata laifin rashin sanar daita zance auren tun farko shiyasa ya dinga lallashinta saboda Abdullah din dai daga jikinta ya fito dan haka akwai ciwon sa a tare da ita, Amman in bayan haka me yuwa sai daita hangi Abdullah da ya'yansa suna shigowa gidan.....
Chapter 29 · 0% Book details