← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 49

Sashe 12

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwance yake a falon mami kan kujera da yammacin ranar asabar kwanaki uku kennan da tafiyar Mama hafsa duk wani abu daya bukaci yana son ci an zube masa teema na hadawa tana mika masa yana ci yayin da mami ke kallon tashar larabawa sai da ta bari ya kammala komai sannan ta rage karar TV tare da Kiran sunanshi ,batare da ya amsa ba ya mayar da hankalinsa kacokan akan mami ,mami tacigaba ina ganin yadace ka ajiye maganar wasa kasan abunda zaka kama .
Abdullah ya zubawa mami ido yana son fahimtar abinda take nufi ,mami tace ina ganin next week zaka tafi sokoto gidan mamanka data wuce akwai diyart faiza daneke son kaje ku daidai daita domin yana da kyau ace ka rufa shekarar nan da naka iyalin.mami ta maida kallonta gareshi domin duk maganar datake idanunta na kan TV. Yacigaba da kallonta iya rayuwar sa ba zai tuna lokacin dayawa mami irin wannan kallon ba "kallonta yake sosai har yanajin wani abu na cracking brain dinsa cikin natsuwa ya sauke idanunshi batare da ya iya cewa mami komai ba" tayi tsai da ranta tana dubansa a wasu lokuta yakan bata mamaki a shekarunsa , ilminsa basirarsa kaifin hankalinsa yace ace zuwa yanzu shi da kansa ya bukaci yin aure batare da anfara yi masa maganar ba "haka nan rayuwarsa ita kadai tafi gane waye Abdullah sai dan cikin Yan kwanakinnan da suka wuce ta fahimci yanayin da Abdullah yake ciki haka kawai wani tunani ya darsar mata a zuciyarta ko dai dan nata bashi da lafiya ne da sauri ta kawar da wannan tunanin ,wanda a fili tace masa "banji kayi magana ba" ahankali ya dago da kansa tare da kakaro murmushin dole yace shi kennan mami Allah ya kaimu zanje .mami tayi murmushi ,duk da dai yadda ta fahimci sa maganar bata wani ratsashi ba tunda ya fito daga part din mami yake kwance akan gadonsa ,wanda tun safiyar yau yakeson yaje yasamu Dr sagir ,Amman maganar mami ta sanya shi yakasa kakkwaran motse gabadaya jikinsa rawa yake tamkar nazarin ya ja bargo ya lullube gangar jikinsa ya kamo lip's ya ciza da karfi ya zubawa ceiling dakinsa ido tamkar maganin damuwar sa na wajen ,babban matsala daya, kasancewa mami ce tafara yi masa zance wata ba tare da ya shigar da maganar Aisha ba,gashi shi kansa bai fahimci kansa da kansa ba sai da yahadu da Aisha ya rufe idanunshi da tafin hannunshi yana magana tamkar tana kusa dashi , Aisha duk ke kika bata mana lokacin inda kin fahimce ni tun farko da tuni mami tasan da zamanki ya bude idonsa a hankali yaga hoton zanenta wanda yayi shi da hannusa ya kafawa hoton ido shi kam kusan komai ya nema gurin Allah yana samu , Amman yarasa me zaiyi wa Aisha ta soshi ,duk wata dabararsa na neman karewa a wannan bangaren ,a fili yace mami nasan Idan kika ga Aisha zaki so ta sosai nasan duk abunda nike so kema zaki so shi .to cikin satin daya gabadaya wanda shine mami ke sa ran tafiyar Abdullah sokoto kamar yadda suka yi da mama hafsa sai gashi tafiyar tasamu Abdullah zuwa kasar Dubai domin nemo wasu sinadari da kamafaninsu ke bukata ,su biyu sukayi tafiyar shi da RK ,sai salis kwanansu hudu suka juyo tun ranar juma a ,sai talata don haka shima satin cikin aiki yake dole bbu maganar tafiya sokoto .duka karfe goma na safiyar juma'a cikin kamfanin nasu dike yake da maaikata kowa ya maida hankali akan aikinsa yayin da ba a fi mintina goma da shigowar MD Abdullah ba, yayin da Secretary dinshi yashigo ya gaisheshi sannan ajiye files akan makeken table din dake gaban Abdullah yadan rankwafa sannan ya juya ya fita ,salis yashigo da coffee cikin karamin cup ya ajiye a gabansa ya fita yadda yake neet haka komai na office din yake haka Kuma yake gudanar da aikin nasa ,bai fi mintina talatin da fara bincike files din dake kan table din wayar sa da ke ajiye agefe ta hau sauti mai ratsa jiki Abdullah ya dago ido yana duban system din wanda zanen hoton Aisha ne a bayyane ya furta ahankali Aisha kennan wasu na shekaru talatin da tara zuwa casain wasu sun gama shekarunsu sun tafi ke sai yau kikai 18 ya fada tare da kashe komai ahankali ya Mike zuwa kofar shigowa ,ta tsakanin glass din da ya ratsa kofa yake hange mutane dake bukatar ganinsa har sun Karu akan sanda ya iso hakan yasa yaji bai iya tsallalakewa yabarsu ya dubi agogon dake manne da hannushi goma da talatin da biyar uhummmmmm yaja numfashi Aisha wata abace mai mahimmanci a gareshi don haka akwai bukatar yaje yaganta koda na minti ashirin ne ya matsa intercom secretary yashigo , Abdullah yace zanyi off zuwa na da wani lokaci yana son komai yacigaba sannan adakatar da masu San ganinsa haka duk wanda yasake zuwa yayi hakuri sai zuwa Monday wanda suka riga suka zo sudan Jira shi,sannan yace yaturo masa salis , secretary yace Ok sir ,ya juya ya fita bai jima ba sai ga salis yashigo.
Yasanar dashi bukatarsa nason fita Amman dole sai ta kofar baya domin masu jiransa bazasuji dadi ba idan suka ga fitarsa, kofar baya salis ya bude suka fita salis ya kwaso wasu ledoji guda biyu yabiyo dashi yana mai jinjinawa Abdullah da irin wannan halin nasa nason kyautatawa mutane da sauri musa yataso yayi da Abdullah ya daga masa hannu yace ya zauna zasu je da salis yanzu zasu dawo musa ya girgiza kai hade da hanzarin bude musu murfin mota suka shiga sai suka biya yakara mata siyyaya har dasu greeting cards "kai tsaye gidan su Aisha suka wuce basufi minti uku da tsayawa a kofar gidan mlm abu ba wata yarinya da bata fi shekaru bakwai ba zuwa takwas ta fito daga gidan cikin sauri abdulla ya kirawo ya tambaye sunanta tace hadiza yace yauwa hadiza Maza jeki ki gayawa inna Abdullah ne yazo yana son ganin Aisha yarinya tace ai inna bata nan tun jiya Abdullah yadan ciza leban sa , sannan yace usman fa.
Hadiza tace duka suma basa nan usman yaje makaranta ba kowa agidan sai yaya Aisha Abdullah yadanyi shiru sannan yace salis ajiye kayan yaje mota ya jirashi , salis yayi yadda yace tun bai wuce ba yaji yana cewa yarinya ta dinga daukar kayan da daya da daya tana shiga da su , sannan idan tashiga ta turo Aisha yarinya ta kwashi Leda biyu da karfinta tashiga dasu ta ajiye cikin zumudi ko Aisha batayiwa magana ba tadawo ta kwashi ragowar ta shige ,sai byn ta tara kayan guri guda take gayawa Aisha taje inji Abdullah .
AISHA dake kusa da famfo tana wanke wanke ta dalla mata harara tace shine ya hanaki kisiyomin Omo dana aikeki . hadiza tace A'a sannan cikin sanyi jiki ta Kuma fita ,aiko sai gashi tasake dawowa wai yace dan Allah kije yanzu zaki dawo Aisha ta kalleta tace kice masa aiki nake Kuma ke nake jira da omon fa . hadiza ta fice haka ta gayawa Abdullah sannan ita Kuma tashige dan gaba da su ta siyo Omo tana yi tana waigensa Abdullah ya dafe kai game da duba agogonsa yana mai sauke hadiyar zuciya ,kai tsaye zuciyarsa ta raya masa ya shiga da kansa dan haka ya shige soron farko yashiga na biyu shima a gyare yake kmr na farko yana karasawa tsakar gidan zai shiga dan haka yadan tsaya daf da ciki ya leka Aisha ce zaune abunta hankalinta kwance akan kujera tana wanke kwanuka a gaban famfo ta gama sauran tukane har yashigo bata sani ba Kuma bata ji motsen komai ba shi Kuma bbu akan abunda idanunshi ya sauka a cikin gidan sai kan damuwarsa bbu ruwansa da wani yanayin na cikin gidan shi sam bai lura da komai ba sai Aisharsa ,tayi masa kyau sosai bai taba ganinta a daidai irin wannan lokacin ba, dan hasken ranar da ya haskata yasake fito mata da sirrin kyan da take da shi. kananan kayan dake jikinta ya dada taimakawa wajen fito masa da kyawunta da bai tabaSani tana dashi ba , hakan yasa tasake daukar hankali matuka, bai taba tsammani ta iya dressing irin haka ba" ya zuba mata idanunshi da sukarigada suka gama rikecewa ko kiftasu bayason Yi, yakarasa sannu ahankali yadan tsugunna daidai inda take zaune motsen tsugunawarsa ne yasanya ta dago a tsorace sukayi 4 eyes dashi ido cikin ido suke kallon juna sai ayau ya kara tantance sexy eyes dinta kullun idanunta a lumshe kmr maijin bacci. yayin da Aisha numfashi ya tsaya cak na wani lokaci kafin daga baya yasoma circulating zuciyarta ke dokawa da sauri da sauri sai da ta saita kanta da kyau sannan ta iya bude baki tayi magana tace manene haka abun naka yawuce waje har cikin gidan iyayena.
Chapter 12 · 0% Book details