← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 49

Sashe 25

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bbu yadda mama hafsa batayi na san ganinsa Amman fur aka hanata ance yana bukatar hutu ta ciza yatsa na ba adadi. daganin wautarta tun farkon xuwanta saboda a yadda taga Abdullah laga laga a kwance shi yasa take son ta fara aiwatar da shirinsu , kmr yadda sukayi da faiza , Amman sai gashi daga gani daya tun bata fara aiwatar da komai ba ,an datse sake ganin Abdullah din ta buga ta buga Amman sam aka hanata ganin Abdullah" haka ta hakura domin visa dinta ya cika na dawowa dole ta taho batare da tayi komai ba daga cikin abunda taje da niyyar Yi.....

Watan Abdullah biyu da kwanaki dady yasake biyo jirgi ya ganshi yadda yaga Abdullah yayi matukar razanashi ya tsorata tamkar ba'a asibiti yake ba , Abdullah ya rame sosai ta yadda har kwayar Idanunshi sun nuna haka , sannan ga wata muguwar kasunba daya tara ,dan ya hana a gyara masa tamkar ba Abdullah din dayasani ba mai matukar son tsafta da kyamkyami...

Aranar dady ya gana da babban likitan dake kula da lafiyar Abdullah a office din doctor jack suke a zaune dady ke tambayar yadda yaga jikin Abdullah yakasance doctor jack kwararen likita ne da ya nakalci cututtuka da dama ,yayi gyaran murya yace shi duk wata cuta da Abdullah yazo da ita iya bincikensu ya samu saukinta koma ya warke musamman daakayi saa Abdullah din bai da kyan jiki to abinda yake damunsa a yanxun kirjinsa Amman akwai magunguna a yanxun daake son Yi masa amfani da su.

Sai dai Abdullah ya hana zuciyarsa sakat da yawan tunane tunane,wanda iya bincikenmu Abdullah yana tattare da damuwa aransa wanda sakamakon yawan damuwar da zuciyarsa take har yasa ZUCIYAR ke barazanar kamuwa da wani ciwon na daban .,kirjin dady ya buga da karfi doctor jack yacigaba munyi kokarin ganin ya'ajiye duk wani damuwa saboda ganin yadda lafiyar sa take yin kasa ni kaina na zauna dashi ya kai sai hudu Amman har yanzu bbu wani canji ,shi yasa muka dakatar da shan maganinsa mai karfi dan gudun faruwar wani abu. doctor ya numfasa yace Amman yanzu abinda naga za'afarayi wanda zai ceto shi daga hakan a binciki abunda ke damunsa a kawar masa da damuwarsa dake damun zuciyarsa , Allah sarki dady kasa ko motse kasayi yayi akan kujera yace to doctor kmr yaya kake ganin za',ayi ciki harshe turancin duka suke magana doctor yace abunda yafi a bincika idan wani abu yake bukata ayi masa idan Kuma damuwa ce yake tare da ita a kawar masa da ita yin haka kadai zaisa yacigaba da karfan magani na karasa samun lafiyar sa ,domin duk kan masu yi masa hidima na bincike su bayani guda daya ne , kawai yake cewa abinda ya dame shi, ko yake bukata wanda Kuma bbu naganin sa asibiti ..

Hankali dady a tashe yabaro office din doctor Abdullah ciwon zuciya INA..... yana ta nanata hakan a ransa to a dare sai da Abdullah yadawo tsaf da shi komai yayi neet a jikinsa , dady yana kallonsa yana cin abinci yana sake nazari akansa yana Jin tautsayi dansa har washegari suna manne tare duk wani zirga zirga ta sha'anini aiki bai kai mahimmanci zama da Abdullah ba a wajen dady ,Abdullah yasamu natsuwa kadan yaji dadin zuwan dady ,wanda har da kansa dady ya fahimci hakan ba kamar farkon da yasame shi ba ahankali dady ke bincikawa me ya sawa ransa har da yake son jefa shi cikin wani hali,ka tausayawa dadynka kasanar dani damuwarka bakada sama dani duk duniyar nan nima haka na jure abubuwan da dayawa game da rayuwa Amman bazan iya jurar rashinka atare dani ba ya kamo hannushi cikin nasa yana masa duban ina sauraronka Abdullah dai yasan dady yana da fahimta abu yana da Kuma saurin ganewa dan haka baiyi shakkan komai ba yadda yagayawa maminsa haka ya gayawa dady har zuwa jenyewar da yayi na auren Aisha dan ba yadda ya iya ....da kuma fushin da mami tayi dashi ... Dady ya zubawa dan nasa Ido sosai yake kallonsa ya damu da fushin da mahaifiyarsa tayi dashi , Amman bai sani ba itama mami tana can hankalinta da ranta suna kan Abdullah kullun cikin maganarsa take.. matsalar dai can gurin yarinyar da iyayenta da akaje aka ciwa mutunci ....

a fili dady ya kira sunnansa yace Abdullahi...
kana son yarinyar nan Aisha har yanzu?
"A firgice Abdullah ya dago da sauri yana kallon dady hade da mummunar faduwar gaba, ZUCIYAR sa ce tashiga dokawa da sauri da sauri yadan jigina da gadon da yake zaune akai yayin da har yanzu hannushi na cikin na mahaifinsa ,yasake kallon dady da kyau yana son karanto wani abu yadda yaga idonsa bbu wata zolaya ko wasa a cikinsu kuma kusan koda yaushe a hakan yake ,ya kau da kai gefe ya fara inda indar magana yace da..dy mami bata son.....that is not the answer to my question I said do you still love her ....cikin tsanyin jiki Abdullah yace ina...ina sonta sai dai ma...hannu dady ya daga masa ya isa shikenan abinda nike son ji daga gareka yacigaba da yi masa wata maganar a hankali yake sake nazarinsa..
Tun yinin biyu nan da sukayi da dady sai ya kasance kullun cikin zirga zirga dady yake a nan cikin Germany sai dare zai kasance tare Abdullah wanda har Abdullah din yadinga mamaki ,kwanan Dady takwas tare dashi a daren da zai baro shi ya kara nuna masa barcin ransa Sosai akan wayan tunanin dayake yawanyi ,da bakinsa Abdullah yayi wa dady alkwarin ba zai sake ba domin yasan barcin ran dadyn nasa ,a hakan ya baro shi da cewar next week zai dawo...

Ta zubawa takardunta na makaranta da aka karbo mata idanu tana Jin daya daga cikin abunda ke sanyata farinciki kennan a Yan kwanakin nan, Amman kuma tun a jiya da safe da yaya umar ya shigo yana yiwa inna bayanin zuwan mahaifin Abdullah abin ya tsaya mata a rai dan tasan dai koma meye magana ce a kanta ..inna kasa zaune tayi kmr tayi tsuntsuwa taganta alhj ishaq taji tana son taga danuwanta har gashi bakin basu tadda mlm abu a gida ba kasancewar da wuri suka zo gashi duk an tura koina bayanan dan haka dady yabar sakon a yau zasu dawo shi yasa ta natsu a daki haka nan Kuma shima mlm abu yau tun safe yana gida sannan Kuma tun safen ya tura yusif yaje ka'oje yazo da mlm dahiru to har yanzu sai dai bbu yusif din bbu baki daga bangaren Abdullah duk inna tabi tadamu dan tana son sake ganin danuwanta ita dai banda mlm da kuma tana da cikakken karfin iko akan Aisha zata so ayi .....

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 20

Sannan kuma naji kace kana bukatar auren cikin sauri nan kusa nidai ina ganin idan har ba wata matsalar a dan dagamin kafa zuwa nan da sati hudu nan gaba.
Dady ya sake Yi musu bayani dalla dalla akan yadda likitan Abdullah yace alhaji aminu ya numfasa yace a satin nan kennan a yadda kuke so dady ya girgiza kai Amman yake dan nakalci wani abu kadan game dasu "wanda da kamar ya manta Amman nan da nan yayi saurin cewa basa bukatar komai game da kayan daki yarinyar kawai suke bukata" mlm abu yace matsalar dai kennan tun farko ta hargitsa abu idan har ya kasance kowa yayi hakuri abin yawuce to a gaskiya ni dai sadaki kadai da yazama dole shi kadai nike bukata daga yaro ya fada yana duban mlm dahiru.... sannan batun daurin aure abarshi nan da sati biyu alhaji Mansur abokin dady kusan duk wata dawainiyar nan da shi akayi ,wanda tun zuwansa sau biyu kawai yayi magana sai yanzu ya shiga juya kai yace yaya za'ace za'ayi haka mu da aka taimakawa aka bawa yaron mu ai mu yakamata muyu komai .

Mlm abu yace sadaki ma dan shine aure in ba haka bbu abunda zan amsa a auren AISHA dady kuwa shiru yayi mutane nan sukara cika masa Ido irin mutane da suka zabi su tsira da mutuncinsu ne ba su tsira da dukiya ba ,a fili yace to haka ma mun gode kwarai Amman maganar gurin da za"ayi taron daurin auren fa?
Chapter 25 · 0% Book details