← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 49

Sashe 19

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhj ishaq ya kalli dan nashi ya kira sunansa cikin sanyi yace Abdullah daman abinda ake so hali na gari ga kowane dan Adam to ALHAMDULILLAH anyi shedar yarinyar da iyayenta tun daga kan makwaftansu har zuwa can ka'oje inda aka haifin mahaifiyarta , mahaifiyarta itace kawai Diya sai dan uwanta wanda daba'asan inda yake ba wasu Fulani rigar dake can "sidi magaji )ne Amman duk da kakaninta na wajen uba ba'anan suke a ka'oje ba Killa ma da iyaye da kakanni suna nan raye da zasu San juna dan nima da kaganni asalin tushena kennan ka'oje cikin kauyen (sidi magaji) kmr dai yadda kasani sana'ace takawo mahaifinta nan mlm abu
Shedarsa itace talaka ne mai godiyar Allah suna zaune da matarsa uwar yayansa itama kuma Anyaba mata sai yarinyar data Kare karatu a makarantar yan'mata dake federal gwandu abin farinciki ,nagarta kamun kai da kokarin yarinyar yasa har tayi suna da aka santa a makarantar sosai ita ta rike shugaban dalibai dady ya dan tsagaita to daman wannan ake so a duk wani iri da'ake nema .

Dady ya janyo wasu hotuna guda biyu ya zuba masa a gabansa to Abdullah dai wani iri yake ji ajikinsa cikin sanyi jiki ya dauki hotunan yana dubawa hotunan Aisha ne sanye da uniform tare da yan'uwanta dalibai sai teacher dinsu sai Kuma dayan gurin wani daurin aure ne yagano mlm abu zaune a gefe shi da wani Abdullah dai yakasa magana dady yacigaba abinda na nunawa mamin ka kennan tun dazu ,nagarta yarinyar ta fito kuma shi zaisa a yada zuria ta gari dan haka tunda an samu wannan sai ature duk wani rashi tunda bashi ake bukata aure ba, ahankali yake kallon dady tamkar yasaka masa kuka farinciki haka yakeji ,dady na sonsa dan yadamu da damuwarsa alhaji ishaq yagama karanto hakan a fuskar Abdullah ya girgiza kai kasanar da iyayenta zanzo da kaina in ne ma maka aurenta murmushin Abdullah yayi dan tsabar farinciki, yana fadada murnarsa a fili yace thank you dady
Yace bbu komai tashi kaje ya fita yana rayawa aransa dadynsa ya dauki Aisha'rsa da mahimmanci da kansa zaije ya nema masa aureta sabanin yawancin abubuwa sai dai ya wakilta aje .

Tsantsar mamaki ne ya rufe mami to ita har yaushe Abdullah ya samu yarinyar dayake so batare da ita din tasani ba har zuwa yanzu dayake gabanta kallon mamaki take masa tace Abdullah tsawon wani lokacin kuke tare da yarinyar a garin nan batare da na sani ba Abdullah yayi shr ya fuskanci yadda mami ta dauki zafi akan maganar tace bazai yuwu ba dadynka yayi bincike akan yarinyar dole nima zanyi nawa bincike daban ,tashi kaje zan nemeka Abdullah yayi shiru kwance yake kan doguwar kujera a falonsa ya harde hannuwanshi a kirjinsa yana tuna maganganun mami ko me mami zatayi shi dai ta ceceshi ta amince ya auri Aisha shine kadai kwanciyar hankalinsa da samun lafiyar a rayuwar sa .to har yau dayadawo daga aiki yaje gurinta abubuwa biyu sun cushe masa farinciki da damuwa dady da mami ,yana matukar tsoron mami yadda tanuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna......

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 12

Yana matukar tsoron mami yadda ta nuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna kin mutun a fili bbu wanda ya isa yasata dole ,ya kalleta idanunshi suka Yi ja yace Aisha idan aka ce za'a daura mana auren cikin satin nan zaki amince ? A frigice take kallonsa tana girgiza kai gabadaya tagama rikecewa tace nidai kayi hakuri ba dai yanzu ba ,ta zuba masa idanunta shima ita yake kallo yace yes na matsu A ce kinzama matata " tace nidai kayi hakuri idan Kuma ka damu sai yanzu to kana iya samun wata ni sai zuwa wani lokacin "yaji haushi maganarta Amman yadda tayi maganar yagane yarinyarta ta a fili ya zabga mata harara yana mai jan tsaki yace ai ba sai kin gayamin ni kadai nike haukana akanki ba nasan bakya sona , takalleshi kamar zatayi kuka kayi hakuri dan Allah ba haka nike nufi ba" bai sake ce mata komai ba ya juya ya barta anan . Sai taji ba dadi aranta daman Kuma ta lura tun zuwansa ta fuskanci kmr yana tare da damuwa .

To har zuwa kwana biyu da maganar su da mami bata sake tada zance ba a iya nasa tunanin ko mami ta hakura ne" wani satin mami take sa ran tafiyar ta zuwa Egypt dubo mahaifinta dake kwance ba lafiya shine dalilin dayasa ta ajiye komai tabari sai ta dawo Amman a wayewar garin jumma'a labarin rasuwarsa ta same su dan haka cikin rashin shiri tayi tafiyar ita da su teema yayin da dady da Abdullah sai rana Saturday suka bi jirgin yamma suka isa, washegari uku dady yadawo Abdullah kuwa kwanansa goma suka juyo tare da su teema da minal saboda makaranta mami ta zauna saboda tafiyar bata kusa bace dole ta zauna har ayi arbain .

Ko sanda ya dawo da washegari sai da yaje yaga Aisha ya rinka nuna mata yadda yayi missing dinta na kwana biyu da bai banga ta ba Aisha taringa kallonsa yanabata mamaki ko kadan baya da riko iya tunanin ta fushi da yayi ranar da yayi zuwan sa na karshe shi ya hanashi dawowa ,sai da yasanar mata da rasuwar da akayi musu. Tayi masa gaisuwa yace idan mami tadawo zaizo ya dauketa ya kaita tayi mata gaisuwa ta amsa da to "Amman ita kam sai ta tsinci kanta tana mai tsoron shiga cikin family dinsu,

Sun sake zama na musamman da dady akan maganar sa da Aisha ya shidawa dady ya sanar da iyayenta cikin satin nan zaizo bai dai samu mlm abu a gida ba Amman yagaya mata ta sanar da inna, ko gwaggo Laure da tazo haka tasa Aisha gaba da zance Abdullah shiyasa har daren ranar da dady zaizo din da Abdullah yazo sai da yasake tuna mata akan tasanar saboda yasan halin kayansa, sai a wayewar garin ranar lahadi mlm abu yafito zai fita suna sallama da gwaggo laure domin itama a ranar zata wuce sannan tashiga rumfar inna da Kyar take gaya mata inna ta hau salati ta fito tana sanar da mlm abu yakira Aisha yana Kuma tambayarta ta amsa da yau da yamma karfe hudu .
Gwaggo laure tace ma'aiki anmabi Muhammad ke yanzu dan iskanci gidan sirikan naki zasu zo shine kika kiyin magana ?
Inna zata kuma yin magana usman dakatar da inna yace ai mun godewa Allah ma da aka samu Allah ya matsi bakinta ta fada ,ai da sai dai anjima kawai Kuga baki, inna tace zata aika ai wannan yarinyar bansa halinwa ta dauko ba gwaggo laure ta rike baki tace miskili kafi mahaukaci ban haushi yarinyar kin zama sai kace harsashi acikin gida Aisha ta hade rai hade shigewa daki mlm abu yace aiko bai ga tafi ba nan da nan akashiga gyara gida ,dakinsu yaya yusif dake soro aka bude aka gyara da yake daya kofar ta fita waje gwaggo laure ma fasa tafiyar tayi yayin da inna tabawa usman kudin machine yaje yagayowa aunty Maryam ,tayi musu dan abun da zata tare su dashi mlm abu da kansa yabar komai ya tafi yagayawa alhj aminu domin a ranar zai Yi tafiya to haka nan alhj aminu yaji maganar daga sama dole dashi za'a karbi baki to shima din sai barin tafiyar yayi yana jinjina al'amarin Allah yadda ya kwallafa ransa akan yahada jininsa da yarinyar Allah bai nufa ba har sapani sukai ta samu da maidakinsa .

Karfe uku aunty Maryam ta iso da kulolin snacks iri iri da juice dakinsu yaya yusif yasha gyara aka shimfida katuwar dadduma Aisha kuwa barin gidan ma tayi gabadaya .

Dady yacika alkawari ya dangana ga iyayen Aisha anyi barkwanci musamman ga alhj aminu to duk yadda dady yayi tunaninsu sai yatarar basu kai haka ba ,sai dai karfin hali da rufin asirin ubangiji Amman ta ko ina bbu, sai dai yaji dadin ganin mahaifin Aisha dagani zai Yi datako shidai mlm abu zaune yake yana bin alhaji ishaq da kallo tsabar kamamani dayake hangowa a fuskarsa tayi masa kama da wata fuskar a haka akayi abunda za'a Yi dady ya tambayar ma dansa kuma Mafi soyuwa acikin yayansa auren Aisha alhj
Aminu ne yaba da Aishar ga Abdullah cikin murna da farin ciki suka rabu .

Bayan dady yadawo Abdullah zaune agaban mahaifinsa yayi shiru yana jiran daga dadynsa yaji mai zaice dangane da zuwansa dan gabadaya baya cikin natsuwarsa burinsa Bai wuce yaji mai dady zai ce ba .
Dady ya yadan Nisa sannan yadago Ido yana kallon Abdullah sosai yaron nasa ke bashi tausayi ganin yadda soyayya tamai dashi cikin kankanin lokacin, wajen yadauki shiru zuwa na wani lokaci sannan dady ya iya Kiran sunanshi Abdullah ya dago yana duban dady ,dady yace Abdullah Aisha dai tayi Maka ko ? ya sunkuyar da kansa kasa yanajin yadda gumi ke bin jikinsa dady yasake numfasawa ya girgiza kai yace shikenan yanzu a yadda nike ganin a aika musu da dukiyar aure da duk wani abinda ya kamata Amman abari sai zuwa hutun karshen shekara sai ayi bikin ta yadda zaka samu hutun ka gabadaya .
Abdullah yajin jina kai dady yacigaba sannan yace akwai bukatar a sai musu gida babba mai wadatar guri musamman saboda taron daurin auri sai mota Hawa ina ganin biyu ko uku zata musu sai maaikatan da zasu taimaka musu da gyara koina ,Abdullah ya dago idanunshi yana wa dady kallon murna yana sakewa dady godiya. dady ya girgiza kai yana lumshe idanunshi shi awajen sa Abdullah ya cancanci fiyye da komai agunsa domin Samar masa farinciki.
Chapter 19 · 0% Book details