← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna aji biyar mmansu sakina taje akin haji dan haka har suka dawo hutu suka koma basu hadu ba, sai byn da suka dawo hutun daga shi sai aji shida suka risketa dayake tunda suka fara makarantar idan sun dawo sai anfara sauke Aisha daga bisani a wuce da sakina gida" ya sanya sai byn kwana biyu da dawowarsu Aisha ta shirya taje yiwa mama sannu da zuwa,sakina ta taro ta da murna kmr ba a satin suka rabu ba ,suka isa falon mama suka tadda ta, ganin Aisha sai da ya tsorata mama , yarinyar ta koma sai kace wata aljanna don tsabar kyau duk yadda tayi zaton Aisha ta wuce hakan ga wani shegen less a ajikinta ya dace da ita sosai km ya zauna ajikinta tamkar dan ita akayi shi,tabbas shine less din da sakina ta nuna mata A aminu yayi musu da sallah babba lokacin da batanan mama takasa cinye fushinta da kishinta har ya fito Fili ,wanda tunda ta amsa gaisuwar farko ta hade girar sama da ta kasa tayi murtuk ganin haka ya sanya Aisha fita ta koma dakin Aunty amarya aiko mama kmr an zugata Aisha na daga falon aunty amarya Amman tana jiyo balbalin fadan mama ,kin bari wacan kinibibiyar yarinyar tagama kanannade miki kurwa jikinki har bari yake idan tazo ni bansan yadda kukeyi a makarantar ba duk da alhj aminu ne ya cuceni da ya hadomin ke da ita, na rasa yadda zanyi dan wannan idan kika samu saurayi tsab zata kwace shi,ko aure kikayi taje inda kike sai ta kwace miki miji da wannan idon nata irin na Mashya .

Sakina ko sai juya hannu take tana rokon ta dan Allah tayi hakuri tayi shiru kada Aisha taji karshe mama korota tayi daga falon ita tashi tayi tashige dakin, tabarta nan idan kan yarinyar nan ce gayar kauye masu gadon tsiya to tabbas zanci ci mutunciki ,. Ta dafe kai hawaye na zubo mata taji antabata daga baya tana juyowa taga Aisha ga mamakinta murmushin Aisha take tare da girgizamata kai tasa hannu tana share mata hawayen tare da fadin ni zan wuce .

Cikin sauri sakina tace to ai....
To kibari a kaiki .
Tace Aa barshi da kai nazo ai sakina tace bari nazo narakaki ta dafa kafadarta na gode sister ki zauna ki huta ta fice da sauri ba yadda bata yi ba dan gano bacin ranta Amman takasa gano komai dan Aisha bata nuna bacin ranta har Suka koma makaranta duk yadda sakina tayi kokari tausasa mata akan abunda ya faru sam Aisha ta nuna mata batason maganar Amman agun Aisha bata taba haduwa da abunda yamata ciwo irin kalaman maman sakina gareta ba ,ta dai bar abun a ranta domin abin yafi karfinta bata da yadda zatayi .

Sunshiga shekarar karshe a makaranta Aisha ta kwatarmusu school dinsu a wani debit daakayi na English sosai ta kware da amfani da manya kalmomin turanci kmr ma baa school din tafara gogewa dashi ba,haka nan sun buga quez akan scientific abinda bata zataba sai gashi ita tasake karbar school dinsu .

Sakina ce tazo ta sami A bahindi a wani dare tace sister zoki ga wata drama taja ta har wani hostel abinda ke faruwa wasu yaran GSS 3 zuwa ss1sukayi group a yadda suka samu cikinsu suka zauna mutun biyu daga cikinsu suka tashi kowace tana gwada tafiyar A bahindi ana ihu daga can Kuma wata Yar aji hudu da duk tafi su zakewa ta Mike ita har da dressing din A bahindi na riga da siket sune ajikinta hakanan Kuma colour da A bahindi tafi so ta fito tana gwada tafiyar A bahindi har da maganar ta idan takeyi kmr zatayi kuka duk sai da yarinyar nan tayi duka gurin akasa ihu ana kidi da botikan robo , Aisha ko ta zubawa sarautar Allah ido can yarinyar ta buga kafa tace da kawayenta nice da komai irin na A bahindi kusan daman ni ina maseefar sonta momy .

Ragowar suka ihu sakina ce tasa tafi tare da cire hijab din da tasa very good ta taso ta nufi inda suke kafin ta karasa kuwa sai fliin gurin tuni suka tarwatse domin basusan shuka sukayi akan idon makwafta ba.

Malamin physic dinsu yanuna yana matukar son Aisha Amman tunda ta fuskance sa ta dauke masa wuta haka malamai da dama suna nuna suna son ta Amman ita sam basa gabanta .

Sun gama karatun su cikin sa'a, da yawa kawayensu an Sha kuka domin wadansu shikenan , ranar da suka gama last paper ko hostel basu koma ba akazo aka dauke su suka tafi.

Watanni kennan dagama school din Aisha yayin da kaninta usman ke aji biyar a secondary ,su yaya yusif na da shekara ta hudu ajamia sabida matsala kudi yasa karatunsa yabata lokacin , ,yayin da ya'ya Umar keda shekara 2 da shiga ita dai aunty Maryam tun bayan gama secondary tayi aure tacigaba da karatu a school of nursing yanzu haka aiki takeyi shi Kuma Ali army school yake son zuwa .

A bahindi babba barinta bai wuce tacigaba karatu a jami'a kmr yadda sakina ma ta kwallafa rai akan karatu mlm abu yacewa Aisha sai abunda A aminu ya yanke akai inzaiyuwo suci gaba to idan Kuma bai amince ba shi kennan .

Wannan shine cikakken tarihin mlm abu .

Yau kmr jiya tun shabiyu yashiga meeting da sauran maaikata sai karfe biyu ya fito duk da sanyi AC dake dakin meeting din hakan bai hanashi jin zafi ba ya fito zuwa nashi office din yayin da salis ke biye da shi da Yar saman court dinsa byn ya shiga ne ya kunna wayoyinsa wayar mami ce ta fara shigowa ya amsa da sauri a dayan bangaren mami tace kun fito meeting din ne? Abdullah yace yanzu muka fito tace zaka karaso da wuri ne domin ina da baki agida .
Abdullah yayi kasa da murya cike da shagwaba yace zan taho da wuri zan tsaya na dan tura sako ta email ne Amman zuwa 5 ina gida yakatse wayar yana mai lumshe idanunshi yana matukar son maminsa ........

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 4

Yayi sallama ya shiga falo mami wanka kawai yayi ya canza kaya yafito , a nutse ya zauna yana fuskantar maminsa sannan yayi fuska yaki gaida bakin da yagani duk yasanta , mami cike da kulawa tace baka gane mamanka hafsa ta sokoto bane .

Abdullah ya waske sannan gaida ita mama hafsa tace ai ni tun yashigowarsa nake kallonsa gabadaya Abdullah ya canza min ,ya koma bature .

Abdullah ya gyara zama hade da lallasa wayar dake hannushi yayin mami ke dariya gashi baije yagaida ke ba har kinzo .

Mama hafsa tacigaba da nuna mamakin yadda Abdullah din yazama tace tsawon shekaru goma zuwa Sha daya fa dole ya sauya kana cikin turawa sun maida kai irinsu da wuya karinga gane yan,uwa mami tadan gunri kafarshi ta yadda mama hafsa bazata gani ba saboda bataji dadin yadda yayiwa mama hafsa ba dagowa yayi suka hada ido ta haaresa ,shi dariya ma tabashi, yayi murmushin gefen baki sannan yace kuyi hakuri mama wlh ba haka bane tun dawowata mukai maganar da mami ina son kwarai in zo aiki ne yarike min wuya Amman ina nan zuwa mami kam abun nasa mamaki yabata dan haka da ido take bin Abdullah da kallo ganin irin karyar dayake shararawa daga tace yayi magana Kuma sai ya bige da karya suna hada ido ya marairaice mata fuska .mama hafsa tace a to dan wannan wata rana sai ka hadu da yan'wanka baka San su ba.

Mami ce ta kwallawa ramatu kira sannan tace wannan yar'uwarkace nasa baka santa ba Abdullah yamata kallon kasan ido tabbas itama Yar mama hafsa ce don ga kamannin nan rahma ta gaishe shi ya ams a ciki sannan ta tashi ta koma gurin su teema dan dukkan su saannin juna ne ,mikewa Abdullah yayi dan zaije ya duba wasu sakonnin a system din shi ,bayan ya fita mama hafsa ke sake yabawa da abdullah km yayi mata kyau matuka .

Har kusan magariba yana gaban system sakonnin dai akan tafiyar da sukayi da dady ta south korea akan neman hadin gwiwa da suke so domin bude reshen company acan reshensu na Denmark shine tun safe yaga sakon ya shigo. sallah magariba da ishai ne yatashe shi a gurin , hakan kuwa yasa mu dady da batun nasarar da suka samu na yarda da kungiyar tayi da km interview din da zasu nemesu .

Duk a wannan dare suka tautauna da dady kan batun don haka bai shiga part dinsa ba sai wajen goma saura na dare ,wanka yayi yasha tea ya kwanta yayi rigingine yana kallon sama , tabbas a dare yau yaso kwarai yaga Aisha Amman hakan bai zai yuwu ba ya rufe Ido tare da fadin Aisha.....ahankali , bai San sanda murmushin ya kufce masa ba sunan yadace da ita komai nata simple ,haka da ganin family dinsu baza suyi tashin hankali ba ,ya jawo filonsa ya rungume shi a kirjinsa yana tuna kallon tsoron da ta dinga yi masa a Daren jiya .

A wannan lokacin kuwa mami da mama hafsa sun kulle a daki suna shawarar hada Abdullah da diyar mama hafsa faiza auren zumunci dake karatu a sokoto to a ganin mami ya dace kwarai Abdullah yayi aure yanzu musamman yadda harkokin ke yin gaba , komai Kuma Abdullah ne inyayi aure hakan zai kara masa kima sosai a idon mutane ,mami ta dada amincewa da shawarar mama hafsa don ko ba komai dai gara ita faiza ta gida ce ,don bata San wacce Abdullah zai kwaso ba Kuma yawan fitar da yake shima tana gudun kada yaje ya auro wata baturiya da ba kabilarsu ba don haka suka daidaita a atsakaninsu sosai , sannan a dan zuwan da mami take sokoto tana ganin faiza bazata bawa dan ta matsala ba ,duk ma wani abu da takeji zata dau nauyin nunawa yarinyar yadda zata kular mata da abdullah .
Chapter 7 · 0% Book details