← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 49

Sashe 3

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da sauri abdulla ta Mike sorry dad garinan kan hanya wanka kawai ya fada ganin Tara ma ta wuce bai bata lokacin ba ya fito yashirya kansa cikin court ashi colour shoes dinsa sai kwalli suke suma machig colour da kayan jikinsa ga agogon diamond dake daure a tsintsiyar hannushi banda kamshi bubu abun ke tashi ajikinsa ya kwashi takardu , jakar system wayoyinsa ya fita gurin mami ,tana falo ita da sister s din shi teema ya gaishe ta ,mami tace ai tundazu salis ya iso baka tashi ba yace yanzu nan ma dady ya tashe ni ,ganin zai wuce mami tace to break fa tun eight yake table yace mami na makara yanzu fa goma fa tace Aa abdulla banason zamanka da yunwa in ka tafi office yanzu yaushe zata tsaya cin abinci shi yasa ulcer keson kama ka kai tsaye zama yayi akan table teema tayi serving din sa bai fi minti goma ba ya Mike yayiwa mami sallama ya fita da sauri salis ya taso byn ya gaisheshi ya karfi jakarta hannushi sannan ya bude masa mota yashiga ya mayar ya rufe musa direver ya tuka yayin da salis ya biyo su a baya cikin wata motar dai dai traffic da ta tsadasu ya sake amsa Kiran dady ke cewa yana gida ne har yanzu , abdulla yace A'a ai mun fito mun dan samu traffic ne a hanya .
Bai karasa maganar ba kit wayar takatse ya cire wayar daga kunne yana kokarin gano abinda ya haddasa katsewar wayar ba yayi tsaki tare da daga kai a sannan ne ya hango ta can dayan side wani Abu ji yana mishi yawo ajiki ga zuciyarsa dake wani irin beating dum dum dum tana tsaye gefen titi wannan caran abayar dake jikinta ya koma kmr karamin hijab tayi kyau matuka haka Kuma akame take da alamun natsuwa atare da ita farin takalmi flant ne a kafarta sai farar jaka a matse a hannunta ya salam kawai ya iya furtawa akasan ransa yana mai runtse idanunshi sannan ya bude su ahankali yasauke su akanta ita kadai ce a bakin titi da alamar tana jiran wani Abu ne wannan karan bbu glass a idanunta Amman duk da haka ya gane ta ya kura mata idanunshi sosai lokacin daya ya fahimci dai mota take Jira dan haka bai batawa kansa lokaci ba ya sanya hannu ya bude murfin mota ya fito ya rufe ya dan risina yace kuzagayo ku same ni wancan side din ahankali yake takunsa cikin natsuwa kallo daya zai masa gane dan wani kusa ne ko dan wani "yayi gaba nesa kadan daga inda take ya tsaya yadda ya mai da hankalinsa kacokan akan titi baza ka taba zaton don ita yaje gun ba ,cikin sa'a har su musa suka sami juyowa bata samu taxi ba sai daidai lokacin da suka karaso gurin sannan mai taxi ya ja ya tsaya gabanta yashigo hjy tashiga tare da sanar dashi inda zataje jiyayi kmr anwatsa tafashashen ruwan zafi yashiga motarsa da Kyar ya iya bude baki musa wancan taxi din zakabi "to yallabai tunda ya zauna yarasa me damun rayuwarsa tabbas wani abu da sani ba na shirin faruwa dashi lip's dinshi yakamo yana cizawa kadan kadan ...........

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 2

Sun rufawa dan taxi baya har da salis dake cikin dayar mota gasunan sune har badariya ,har sanda aka sauketa da inda tashiga duk akan idon abdulla har kofar gidan suka isa sukayi parking layin shr bbu wata hayaniyya haka gidan data shiga ba wani babba bane sosai , sun sami kusan mintina goma kafin suga wurgawar wani. daga can km sai ga wani yaro dan kimanin shekaru goma , zai shiga gidan salis ya kirawo shi ,byn yaron yazo yake tambayar sa yarinyar data Shiga gidan ko yayarsa ce.yace A'a ai shi almajiri gidan ne , salis yasake ce masa ,to ko yasan yarinyar gidan yaya sunanta , ya Kuma cewa ai matar gidan batada babbar ya duka yaranta kananane Kuma Maza guda biyu an Kuma tafi dasu makaranta tun dazu , atare suka gane itama bakuwace kennan, salis yace to idan kashiga kace ana sallama da bakuwar datashigo yanzu yaron ya shiga bai jima ba ya fito kai tsaye yace wai bakuwar tace dan Allah kuyi hakuri ku tafi ,dama tun da yaron yafito abdulla ke kallonsa yana jiran yaji mai zata ce har ya juya zai sake shiga gidan salis yace kace mata wai mai taxi din dayakawotane yace tayi mantuwa .yaro ya amsa yashiga musa yayi dariya aciki ,ya juya musu kan motocinsu yana daidaita su,ai ko bai wani jiba sai gata ta fito sanye cikin riga da siket na less marun colour mayafin abayar tayafa akanta da alamun kayan ne acikin abayar dazu "sai yaga tasake masa kyau fiyye da dazu suna yin ido hudu da abdulla da ya zuba mata idanunshi duka sai tabi ta diririce tana kokari fito sosai don ta hango mai taxi dake kiranta , tsammaninta ko zai ce bata bashi kudinsa bane ita dai tasan tabashi Kuma bata manta komai ba,kwata kwata bata ga alamunsa ba sai kawai tajiyo gyaran murya daga bayanta abdulla ne yayi nan da nan salis yace bakiji ba gashi nan fa , ahankali ta sake juyowa duk tsammaninta mai taxi ne ,tana juyowa abdulla dake jingine da jikin mota ya harde hannuwanshi a kirji ya zubamata manyan idanunshi yanabinta da kallo ganin duk ta daburce yasa yadan saki murmushin har gefen kumatunsa ya lotsa , salis yace madam ba gaisawa sai ki leko Kuma zaki koma . kallonsa kawai tayi mai hade da harara ,ta sake juyawa ta shige abunta salis yadafe kai yayin da abdullah ya cije lebansa yana mai runtse idanunshi,salis yace ta leko ta hararemu ta wuce abunta . Hade da cewa kai dagani madam fa za'a dama daita . abdullah ya dubi agogonsa muje kawai salis ai munga inda tazo yashiga suka wuce .

Tana shiga aunty Maryam tace me kika manta tace bakomai wlh aunty, irin banzayen kwarorin nan kawai" sukayi me kwarorin?inji aunty su dai nagani awaje aunty Maryam tadanyi dariya hum kedai baki da kara akan Maza .

Yana idar da sallah yashiga part din maminsa yasame ta itama ta idar da sallah duk da agajiye yake yadan zauna kusa da maminsa ,sister dinshi amina ta Miko masa fresh milk a Kofi ya karba ya Sha ,ya bata cup ta wuce kicin yace mami zandan fita bazan dade ba dan ita mami irin mutane nan ne dabasason arabeta ko ita tarabi mutun haka ko mijin bata barinsa ya sakewa da kowa inba ita da yayanta ba,mami takarasa jan carbi ta shafa ta kallesa tace Amman kasan salis yatashi daga aiki ko,ko a haka zaka fita daga kai sai musa yace ni kadai nike son fita ba direba mami tace no abdullah banason fitarka kai daya ga dare gashi kai bawani sanin gari kayi ba sosai" kayiwa salis waya kawai yazo ku je tare abdullah yadan langwabar da kai yace mami banason takurasa cikin iyalinsa ,tunda yarigada ya tafi a kyaleshi nima ba dadewa zanyi ba ta kada kai ,shi kennan Amman banso ka dade a waje" yayi murmushin ya Mike bazan dade ba har zai fita tasake cewa yanzu kai kadai zaka fita kennan ahankali yace don't worry mamina I can drive my self tace agaida sagir zatonta can zashi taci gaba da abunda takeyi yayi murmushin ya fita ,.

Cikin natsuwa yake tuki cikin dark green din benz har ya iso badariya dai dai kofar gidan dazu yayi parking cikin sa'a mai gidan ya tarar tare da wani bako ya isa yayi musu sallama tare da gaishe su , sannan yadan koma gefe basu jima ba sukai sallama bakon yashiga motarsa ya wuce .
Chapter 3 · 0% Book details