← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 49

Sashe 5

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin inna ya tsufa da Kyar take iya komai ga wani sabon tashi hankali daya samesu ,mai gidan ta basu notice nan da wata 3 zata gyara gidan danta zaiyi aure Kar kaso kaga yadda hankali mlm abu ya tashi a kullun da zance yake kwana yake tashi har rama yayi a wannan lokacin a safiyar laraba har ya fita can bakin titi inda yake zube takalma sai wajajen Tara sai ga yusif da gudu yaje yakirasawoshi yazo inna bbu lfy a gigice ya taho byn bar kayansa gun makocinsa daman tun jiya bata jin dadi ganin abun ya gagara ne yasa tani makwaciyarsu tace akirasa su wuce asibiti yana zuwa ko yace su tafi saboda yadda yaganta ita kuwa inna da taki kasancewa ita bata taba haihuwar asibiti ba sai a gida tani tarike zuwa titi a sami mota tare da mlm abu basufi mintina da tsayuwa moto ci nata wucewa Amman bbu ta haya wata mota kirar passant mai dauke da lambar sokoto har ta gota su sai km ta dawo ahankali ,ta sauke gilashin motar wani mutun mai fuskar fara'a ya tambayi su mlm abu yayi masa bayanin mutumin yace bbu laifi su shigo ya taimakesu su duka duka shiga domin a wannan lokacin bbu rashin gaskiya sosai a duniya a motar yake sanar dasu shima asibiti zai je dauko matarsa ta haihu tun jiya da daddare yau za a sallemesu .

Asibiti ya zarce da dasu ya tabbatar an gama musu komai an tura ta dakin haihuwa saannan ya karasa gurin iyalinsa mlm abu kuwa bai iya tsayawa ba shima ya bishi suka shiga tare suka tarar har an basu sallama ,suna hada kayansu ita da wacce suke tare alhj yakarasa ya dauki bby yana kara mata addu'a sannan ya mikawa mlm abu ya juya yana ma matar sa bayanin sa ya karbi yarinya yayi mata addu'a sannan suka sake gaisa da matar mutumin yana kara Yi musu Godiya sosai da sosai alhj yace bbu komai nima nan jiya bananan makocina ne ya kawo su dama ai haka rayuwa take a haka suka fito yana so yaga likita domin jin dai dai da sallamar tasu, tani ce ta tare su da murna ai har ta sauka yanzu da sauri suka sake karasawa ciki lafiya ta haifi diyart mace har an fito da ita an gyara yarinya ita ma inna ana gyarata,duka basu fi minti ashirin ba da zuwa ta haihu , nurse din tace dama da an dau wani lokacin mai tsawo sai dai ta haihu a mota aka gyaro yarinya tasa siyo mata kayan bby aka turasu inda zasu huta sannan su mlm abu suka karasa ya dauki bby baki yaki rufuwa yana Yi mata addu'a ya mikawa alhj yana karbarta yana murmushin shima yamata addu'a ya yaba kyaun da Allah yayi mata ya mikawa tani yarinya sannan suka fita a haka sukayi sallama da mlm abu yana kara jaddada godiyarsa ga alhj da bai San sunnansa ba, da zasu rabu har kudi ya bawa mlm abu akan su nemi mota idan zasu koma mlm abu har yarasa bakin magana illa iyaka ya nemi yasan inda alhj yake zaune don idan komai ya natsa yaje yasake masa godiya ,alhj yace bbu komai Amman yana iya zuwa a gaisa yayi masa kwatance unguwar da gidansa a haka sukayi sallama .

Wanna karan cikin kebbi akayi suna inda yarinya taci Aisha iyaka dangi da suka samu zuwa suna har da kanwarsa Laure tun ana sauran kwana biyu suna ta iso.

kwana uku da suna mlm abu yabi kwatance da alhj yayi masa har unguwar aka nuna masa gidan alhj aminu yakara yayi sa'ar samunsa a gida sun gaisa sai gashi mlm abu ya fito da goro da alawa har da Naman sunan Aisha yabawa alhj aminu ya karba yana godiya mlm abu ya tambaye sa iyali da Sunna jaririya , alhj aminu yayi dariya kawar Aisha kennan tana ciki ta karbi sunanta sakinatu sun dan taba hira sukayi sallama ,alhj aminu mutune mai son Hulda da jama'a gashi wayayye yana da rufin asiri dan boko ne sannan yana taba kasuwanci duk abunda yasan zai samu halak dinsa akai ,yana da mata biyu yayansa hudu yasir musba ummulkursum sai sakina yayin da amarya dukka watanta bakwai kennan hakanan alhj aminu yana da raayin kansa idan yace ga abunda zaiyi bbu mai iya canza masa ra'ayin ba iyalinsa ba ko wansa a yanzu da suke ciki daya idan ya tsaya kan abu.........

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 3

Ko wansa da suke ciki daya idan ya tsaya akan abu sai dai ya kyale shi, ma'ana kaifi daya ne idan zaiyi zaiyi ,idan ba zaiyi ba ba zaiyi ba ,Kuma ko kadan baya yarda hakan yasashi shiga hakin wani wannan kennan.

Duk da wannan lokacin mlm abu yayi girbin amfani Gona dan haka ya raba har gidan alhj aminu Yan magana dai sunce naji dadi shine gari, a bangaren alhj aminu shima yaji dadin abinda yayi masa ,a lokacin har ya nema sanin inda Mlm abu yake da zama , Mlm abu yayi masa bayanin sai dai ya nuna masa a halin da suke ciki yanzu na shirin tashi suke alhj aminu yace muddin ya samu daki a garin nan zaizo yasanar dashi in km bai samu ba zaso koma garinsu ne ,alhj aminu ya tambaye shi tsawon shekarunsa a garin da km lokacin da aka basu notice duka mlm abu yayi masa bayani komai alhj aminu ya Nisa yace yanzu dai zaiyi tafiya gobe ,km in Allah yaso nest week zai dawo dan haka yazo nan da kwana takwas ko Tara yazo yasamesa yace yadan jinkirta tashi har ya dawo, haka suka rabu ,A aminu yace a gaida masa da Aisha.

Ranar alhamis ta kama kwanansu Tara da yin magana ,jiya laraba kennan A.aminu ya dawo daga tafiya da yayi zaune a sitting room din A aminu tare da mlm abu byn gaishe gaishe A aminu ke tambayar sa dama can shi baya wata Sana'a ne mlm abu ya sanar da shi irin sana'ar daya tabayi da wacce yakeyi yanzu ,alhj aminu yace ai yanzu ina gani komawa gida ba naka bane hakan yawon biye biye gidan haya ba mai yuwa bane ,ina ganin abinda yafi ka tsaya ka nemi naka na kanka ka siya ka zauna da iyalinka .

Mlm abu ya zaro idanu zaiyi magana A Aminu ya katse shi ,ta hanyar daga masa hannu ,yace akwai wani dillali dake kawo min filaye ina siya byn Yan watanni kadan sai na siyar ,haka nan ya kawomin gidaje kanana har sau biyu na siya daga baya siyar dasu ,to nayi magana dashi tun a Daren da zanyi tafiya nasa ayi cigiyar gida karami a wancan zuwa da kayi kasanar dani kana da Gona a garin ku , dan haka zaka koma ka tsaida wancan Gona.

Mlm abu yasake zuba masa ido , A aminu ya cigaba "haka nan a labarin daka bani yanzu ba aikin da baza ka iya ba,.

ka iya tuki da sauri mlm abu yakada kai to ALHAMDULILLAH dan haka zanyi kokari naga nasamarmaka tuki a wani kamfani ka fara ,ba zasu biya ka ba har sai kayi wata biyu su hada su gabadaya ,to da wannan albashin naka da kudin wancan Gona ina ganin zasu isa ka nemi gida karami naka na kanka .

Mlm abu ya hadaye yawu da Kyar ga bikin zuwa .... A aminu yace kafin wannan yana da kyau kafarayin shawara tare da tunani akan hakan mlm abu yadan sake gyara zama sosai yace alhj ni banida kowa a garin nan sai matata da ya'yana sai kum abokin arziki irin ku ,don haka wannan shawara daka kawomin ma tayi min sosai na km gode kwarai da gaske ,sai dai km ita wannan Gona bani kadai ke da ita ba gadarta mukayi nida kanwata , haka nan a jikinta muke dan samun abinci na wani lokacin , wannan shine matsala , maganar komawa gida dama nidin ma sai takama dole don banason komawa alhj aminu yace wannan gaskiya ne sannan yace abunda zaayi mlm abu ....yasakeyin shiru can ya Nisa yace abunda zaayi kasake bani kwana biyu zuwa uku zan sake ganinka.

Mlm abu yayi godiya tare dayin musabaha alhj aminu yace muje na sauke ka a gidan.a hanya suna ta hira yanayin rayuwa ta titi da su mlm abu ke kafa tebur suka wuce har ya nuna masa inda yake zama alhj aminu ya sauke shi kofar gida da yake yammace ,a dai dai lokacin sai ga yusif da Umar Maryam na rike da hannun Ali antaso daga makaranta Allo dukkan su da allunansu a hannu da gudu sukayo wanjen mlm abu, yayin da Ali ya tsaya baya yaki tawowa wai don sun rigashi zuwa mlm abu yana dariya ya karasa ya dauko shi ya cika ZUCIYA ,alhj aminu ya rike hannu yusif da Umar yana tambayar su sunansu mlm abu ya karaso ya ajiye Ali yana lallabashi alhj aminu ya kama hannusa yace taho nan abokina ka rabu da su anan yake tambayar yaran ajinsu nawa a makarantar boko yusif yayi caraf yace ai bama zuwa alhj aminu yace subuhanallahi ya akai kuna cikin birni ba kwa karatu boko ,ya dubi mlm abu.

Yace wannan km laifin ka ne mlm ya'ya irin wadannan basa karatun boko mlm abu yayi murmushin saannan yace dasu yusif suje gida dazasu wuce A aminu ya fiddo kudi cikin aljihun babbar rigarsa ya basu , saboda sabon da innarsu tamusu suka ki amsa sai da mlm abu ya sanya baki sannan suka karba sukayi godiya suka wuce gida , A aminu ya bisu da kallo yana yabawa da yaran Masha Allah.

Sun Tautauna akan wannan matsala ta rashin karatun yara kafin surabu inda A aminu ya Dora laifin kan mlm abu shi km har a lokacin mlm abu yanaganin akwai saura lokacin da Allah zai kawo yaran suyi karatu tunda shima daman akwai soyayyar karatun aransa Allah ne baiyi ba,a haka suka rabu A aminu yace zai nemeshi acikin kwana kin nan.
Chapter 5 · 0% Book details