← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 49

Sashe 35

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wanda a wannan zamanin ba wai wani abu bane agun namiji baligi musamman wanda yashiga matsalar aure irin haka ..
Jikin mami yayi sanyi.d dady ya numfasa tsoro bakya son aurensa da Aisha yasa shima yace ya hakura ya zabi farincikinki ,akan nasa kisani yadda muke da hakki akan sa shima haka yake da haki akanmu, haka ne ma yasa na tsaya tsayin daka naganin nabashi farinciki sa da lafiyarsa akan ko ma me zai faru ya faru" abin takaici da damuwa duk gur biyu ya kamata atoshe masa .ga dai Abdullah ya auri yarinyar da yake so . wanda burin rayuwar sa kennan sai gashi rashin hadin kanki yasa damuwar dai har yau bata barshi ba bbu koma bbu komai Allah yaraya min shi idan Kuma sanadiyyar hakan wani abu ya faru dashi har narasa shi , shikenan sai kiji dadi ki samu wanda zaki aurawa wacce kike so, ya fadi hakan yana girgiza kai ya sake cewa bbu komai kmr zaiyi kuka dattijon ya koma kalar tausayi .. mami tasan ya kai karshe kennan tunda ya nuna haka ,tasan sa tasan halinsa, tsawon sama da shekara talatin da suka fara rayuwa tare. zuciyarta fal tsoron yadda yayi mata magana. ta kalleshi bai sake cewa komai Ba kuma tasan a yadda suke ko zasu Kuma kwana a haka ba zai sake mata magana ba" a yadda taga yanayinsa ta jima anan zaune daga baya ahankali ta Mike jikinta yayi mugun tsanyi kafarta kmr bazata dauketa ba ..koda ta koma part dinta ma tunanin duk ya hanata sakat ko dazu daya shigo ta lura yanayin sa. ya kara ramewa akan sanda ya dawo daga jinya maganar dady akan hanya take "yadda Abdullah ke ratsawa kasashen duniya yana ganin yan'mata iri iri na turawa ai da tuni labarin yasha bam bam bama zai bukaci yin auren ba. ita daman ta dan soma sadudu biris din da tayi dai shine ya Dame yaron. Kuma gashi yawan damuwa ita zata haifar masa da ciwon zuciya amatsayinsa na wanda bai gama samun lafiya ba. ta furta kalma na shiga uku ,haka kawai ina neman kashe dana da kaina ...

Mu dai tafi hankali shin da gaske mami ta saduda kmr yadda tace ko kuwa dai tayi likimo ne "amsar ku naga Yar mutan bagudo ku dai biyoni a sannu ahankali dan kusha labari mai tsansar abin tausayi😭😭😭😭😭

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 28

Karfe daya da rabi daidai byn dady yayi sallah ana masallaci cikin gidan. biyu daidai kuwa a gidan Abdullah tayi masa Abdullah ya shigo dakin ita kadai yasamu domin aunty ta wuce tun dazun.

Tayi kyau tayi gayunta kmr yadda yadda ya Gani. ahankali ya matso kusa daita ,yana murmushin ya sanar daita zuwan dadynsa ,a frigice take binshi da wani kallo cikin marairaicewar fuska tace me nayi Kuma . har taso bashi dariya Amman ya dake baiyi dariyar ba" yace bawani abu bane ina ganin dai kan tafiyar ne, ba dai kince bazaki bini ba sai muje kusanar dashi da bakinki "dan kar ya dauka ko daga gareni ne yasake hade rai ,ta sauke ajiye zuciya ahankali yayin da tacigaba da kallon Abdullah, baya ya juya yasoma barin dakin yace yana falo .

Tabishi da Ido kawai ita dai da Abdullah ya tsaya sun sulhunta kansu zata bishi ba sai ya hada da dady ba" dan ita tsoro take ji ,batasan abune yafi karfin Abdullah din ba shi yasa ya sanar da dadynsa..

Tayi sallama ta isa falon ta nade jikinta da abayar har da dan kwali tamkar wata balarabiya cikin natsuwa ta nemi can gefe ahankali ta zauna ta takure jikinta waje daya .

Dady yana waya sanda tashigo sai da yagama ya ajiye wayar sannan ya kalleta ta sunkuyar da kanta, kwarjinin dady ya cika falon ahankali ta gaishe shi ya amsa yace Aisha kennan yasake maimaitawa ahankali yace taso zonan ki zauna yanuna mata kan carfet dake gefe kusa dashi" sai da ya Kuma maimaita hakan sannan ta taso a dan tsorace wanda har kallon da Abdullah ke binta dashi kasa kasa yasa ta kusan faduwa a diririce ta zauna .
Inda dady ya nuna mata. tare da sake sunkuyar da kanta sosai " poor Aisha dady ya fada akasan aran shi duk yadda ya dauketa ba haka ya ganta ba, dukkanta bata fi girman aminarsa ba ,ya kara jin tausayinta yashiga ransa matukar,a fili yace Aisha kun kwana lfy a gidan ko ?ta daga masa kai yayi murmushi madallah bayan dan shr yayi na wani lokaci sannan dady yace da gaske wai kince bazakibi mijinki ba "taji kmr kasa ta bude ta nutse ciki ta kara sunkuyar da kanta har ya gane tsananin nauyin data ji" yayi murmushi .

Yace Aisha dubi kigani ya nuna mata Inda Abdullah ke zaune" mijinki peticent ne daga gadon asibiti yazo daurin auren ku kinsa tun accident din da yayi kin sami labarin ko?

Ta daga kai yace to har yanzu bai gama warwarewa ba likita yace daurin auren "na daga ciki abinda zai taimaka gurin warwarewarsa .

Ko kadan ita batasan da wannan ba dan haka a yanzu ma dagowa tayi takalli inda yake 'dady yacigaba to kinga zai yiwu adaura auren Kuma yabarki anan ya koma shi kadai "kiyi hakuri kibi mijinki da taimakon Allah da taimakon ki zai karasa samun sauki hakan yasa gabadaya jikinta ya mutu ita duk batasan da haka ba..

Shi kuwa Dady kallonta yake sak maimunarsa tana karama Amman ita Aisha kusan har tafi ta komai ,yana jinjinawa al'amarin Allah , a ganinsa kmr tayi karama da tabi Abdullah din. bugu da Kari yana ganin kmr ta yiwa Abdullah yarinta ,sai dai ba,a nan take ba tunda daga kallonta zatayi hankali ,a fili ya sake cewa kiyi hakuri kibi mijinki ki duba shi kinji ..

Ta daga masa kai yace yauwa Allah yayi miki albarka Allah yabaku zuria ta gari ya dade yana Yi musu addu'a sannan ya tambaye ta ko akwai wata matsala tace bbu yace taje ta huta ..
Karfe hudu zuwa biyar zasu wuce ta amsa ahankali ta Mike ta shige ciki dady yabita da kallo yana girgiza kai ya koma ya jingina bayansa da kujera "ya Kuma jin tausayinsu na ratsa shi ,yace aransa duka abinda mami kewa rikici kennan "dan shi dady bai taba ganin Aisha ba sai yau haka ma mami "ya waiwayo ya kalli Abdullah ya kira sunnansa yace Abdullah Aisha ba suruka ta bace diyata ce ko bbu aure tsakaninku ni mai iya rike ta ne "tare da duk kan dawainiyar komai nata dan haka kai ma dan Allah ka rike amanarta..

To abangaren dady ya wanke ZUCIYAR Abdullah din tas domin ya yaba da Aisharsa ciki da waje. "byn tafiyar dady ya shiga dakinta ya sameta ta daga Ido tamkar wanda tayi kuka ganin da yayi zata yi magana yasa ya matso da saurinsa ahankali tace su innarmu basu san yau zamu tafi ba yadda tayi maganar ne tayi matukar bashi tausayi" ta sake cewa ga sister tun jiya bata zo ba. Ya kamo hannuta cike da kulawa yace bari yanzu naje gidan, me yiwuwa baba yabiyoni sai kuyi sallama Inna ce dai nasan da kyar ne" shi Kuma salis sai yaje ya dauko miki sakina

To shima mlm abu addu'a yayi musu sosai sai dai su yaya yusif da umar da Ali ne suka biyo Abdullah dan dama ita aunty tabiya ta fadowa su Inna koda ma Abdullah baije ba daman za'a tura wani ,sai ga salis shima ya dawo wai sakina ta wuce zuru tun safe ..
A falo Abdullah yabar ta da yanuwanta yaya yusif ya Mika mata sakon su inna ta duba taga har da dan karamin alqurani me kyau wanda aka taba bawa baba abu tsarabar saudiya ,suke ta rige rigen ita da usman ya basu kowa yana so baba yace abar masa abin sa shima yanaso, tayi murmushi ta rungume shi a kirjinta tace ina usman .umar yace ai tun jiya da aka tawo dake yayi kuka har zazzabi ya rufe shi har yanzu yana gida bai fita ba "idanunta suka ciciko da hawaye tayi murmushi tace aranta bazai san yayi tarashina ba sai nabar garin gabadaya.basu fi mintina talatin ba duk suka Mike .

Abdullah da ya amsa wayar teema ,daga cikin wayar take sanar dashi mami ke nemansa nan da nan yadan Sha jinin jikinsa ko wani abun ne kuma ya faru tare suka fito da su Ali .

A part din mami zaune yake kusa da ita kanansa duk suna zagaye dashi . ya dan sake musamman tunda su faiza sunbar gidan tun ranar daurin auren tun kafin adawo faiza ta hau iskar karya tana fizge fizge tana surutai tana hadawa da sunan Abdullah, Amman duk haukan nata bata tona irin abinda tayi ba. Da bai samu Abdullah ba". nan kallo ya dawo kanta mama hafsa naganin haka ta tattara ta suka bar gidan ko cikakkiyar sallama basuyi da mami ba" dama haka abin Allah yake idan Allah yariga ya tseratar da kai ka tsira.

Mami tarinka kallonsa wata rayuwa ta daban dan nata zai shiga wacce acikinta girma yake shigar mutun" koda mutun bai shirya hakan ba .duk yadda taso da kasancewa auren nasa ba haka yazo mata ba. "ga Abdullah din zaune a gabanta matarsa a can wani waje daban wadda bata ma san ko wace kala bace "daman Kuma dady ne ya hana akawo Aisha gidan yace kai tsaye a wuce da ita gidanta ,mami ta jinjina kai Amman ita yanzu rayuwar dan nata ita tafi damunta, ta numfasa tace yanzu yau din kennan zaku tafi yadda yaga tayi maganar cike da kulawa ba kmr a yan kwanakin nan ba ,yasa ya ji ko mamin tasa ta fara saukowa ne .
Ahankali ya dan kara matsowa kusa da ita yace dady yace yau yake so mutafi ta sake numfasawa tace tunda yace yau din ne nasan bbu fashi ta girgiza kai sannan ta Kuma cewa shikenan sai kun dawo Allah yabada zaman lfy ..

kukaramin hakuri sakamakon rashin yimuku typing da yawa zuwa wani lokaci komai zai tafi yadda ya kamata
Chapter 35 · 0% Book details