← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 49

Sashe 28

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dare byn sallar ishai kafin mlm abu ya fita waje, inda yake zama domin shan iska suna tare da inna a daki duk dai inna mlm abu take sauraro danji wani abu daga gareshi dangane da zuwan yayanta Amman yamata gum da baki har sai da taga yana niyyar sake fita sannan tace mlm kamin shiru Kuma kasan kai nike Jira ya juyo yana fuskantata sannan yayi murmushin yace yakira sunanta " munah" kennan ta dago kai ta dube shi dan bakasafai yake kiranta da sunan ba" kin damu da dan uwanna nan naki dayawa gashi shi bai damu dake ba ,bai ma san inda kike ba balle yasan da zamanki....tagane mlm kmr yana jin haushin yayanta ne Amman duk da hakan kin damu kanki akansa da dansa, ta mai kallon second daya sannan ta dauke idonta daga kansa tace to yazanyi ni dai ina son danuwana a haka shima nasan har da makircin mace acikin lamarinsa mlm abu ya karkace kai yana kallon inna yace to Allah shi kyauta tace ameen nan dai yamata bayanin duk yadda sukayi inna tayi shiru ta sunkuyar da kanta kasa sai kuma ta tsinci kanta da rashin Jin dadin abunda mlm yayi wa yayanta yace naji kinyi shiru ta sauke naunauyen hadiyar zuciya tace mlm ina ganin tunda yazo da kansa me zai hana ka amince masa da bukatar shi ,ni fa nasha mafarkin kusancina da danuwana Amman bansan ta sanadin auren nan bane..
daga lokacin da mahaifiyar Abdullah taxo gidan na gasganta wannan shi mafarkin dana dade nakeyi akan sa ,dan Allah mlm kada kabari damar nan ta subuce min wlh ina matukar son kusan cina da danuwana mlm abu yayi sukutun yana sauraronta kafin daga baya yace to shikenan zan duba abun sannan zan tambayi ita yarinyar ko tana son Abdullah din. dan dai kinsa bazan bin son ran wasu na wa diyata auren dole ba ko ya kafe inna da Ido itama innar shi take kallo uhmm tace abunda yakamata shine yazamo farko shine sai yanzu zakayi yace uhm ,mlm abu dai ya fahimci inna sarai ta shaki maganar sa ne , Amman me sai canza wata maganar zuwa mikomin radio ta ta Mika masa yabar dakin shiru tayi sannan yayi wani tunani sai ta Mike tashiga dakin Aisha kwance tasame akan katifa tana ganin shigowar inna ta Mike ta zauna tunda taga Inna tashigo batare ta kirata dakinta ba tasan koma meye abu ne mai mahimmanci zama inna tayi kusa da ita tana mai Kiran sunanta Aisha....ta amsawa inna cikin sanyi jiki "inna ta tsaya tana duban diyarta duk Aisha ta kagu taji mai ke tafe da inna " inna numfasa tasake kiranta ina bukatar wani abu daga gareki da sauri ta dago tana duban inna alamun tana jinta, ina son kimin wata alfarma kifadi komaye shi inna ashirye nike dana miki bukata kawai kisanar dani kinji innata ,inna tayi murmushi tace so nike ko mlm ya tambaye game Abdullah kice kin amince zaki aure shi wani abu taji yana mata yawo a ilahirin jikinta takasa amincewa aduniya take ko a lahira inna tace kinyi shiru bazaki iya ba ta girgiza kai sannan cikin tsanyin nan nata tace zan iya inna indai hakan zai saki cikin farinciki kin sa matsayin Abdullah aguna Aisha cikin sauri ta girgiza kai inna ta sauke hadiyar zuciya to "dan , dan' uwa na ne uwa daya uba daya kinga kennan Abdullah dana ne halak malak Aisha daskare zaune tamkar an dasa ta tarinka bin inna da shanyayun idanunta inna tace nasan zakimin fiyye da haka domin ke Yar albarka ce Allah kuma yayi miki albarka na go....ai tun kafin takasa Aisha tasa hannuta ta rufewa inna baki tana girgiza mata kai haba inna ai abar ikonce umarnin kawai zaki bani nabi kuma ni karkimin wata godiya a duk lokacin da kike da bukatar abu ashirye nike dana miki shi tsabar dadi inna bata San sanda rungume ta ....

To washegari da safe byn mlm abu ya gama shirinsa na fita, yasa inna takira masa Aisha" zaune take a gaban mahaifinta ta sunkuyar da kai kasa ta zubawa yatsun hannunta Ido tasan koma meye yasa baba yayi kiranta tasan yaba da nasaba da maganar inna ta jiya duk dai bai wuce kan Abdullah ba mlm abu ya kalli diyarsa zai dai tambaye ta ne kawai kar inna ta dauka bai son hada iri da alhj ishaq ne yakira sunanta Aisha kina don auren Abdullah .....tayi shr har sai da ya sake maimaita wa sannan ta daga kai mlm abu yayi shiru yana nazarinta da kyau sai yake ganin kmr ba raayinta ta fada ba ya sake cewa kin amince kennan ta dago cikin dakiyar zuciya tace Eh baba na amince to shikenan kina iya tafiya ta Mike kmr wacce kwai ya fashewa aciki tabar dakin zaune yake har yanzu tabbas yayan zamanin nan ba'a shedarsu .....

Dady da kansa ya taka kafarsa har zariyar Kala kala yaje inda iya haka yanzu ma anan duk wata kalma ta bada hakuri yayi amfanin da ita a wannan lokacin mlm dahiru ne yayi magana to dama shi sha'anini rayuwa haka yake ko atare ake wata rana za'a saba ballanantana dady yace abin dubawa kennan kuma ko wacce halinta akwai inda Allah ya rageta idan kana da wannan to kana bukatar wancan .
Alhj aminu yace haka ne yake kuma ita dole ita rayuwa sai ana hakure mata mlm abu kam kasa magana yayi jin halin da akace yaron yana ciki a yanzu ya tuna karshen zuwansa wanda shine yayi hatsari jikinsa yayi sanyi wanda kowa sai da ya fahimci haka a gurin ..

Mlm dahiru be yakatse shiru da akayi da cewa to yaya zaayi Allah yaringada ya hada yara ba mai iya tabawa kuwa sai dai ikonsa nan fa jikin mlm abu yasake sanyi alhj aminu yace maganar tsakanin su aure abar ta kamar yadda take a da can mlm dahiru ya amsa haka ne kawai zai fi dady yashiga murmushi ya fara godiya tamkar wanda aka cewa Abdullah dinsa ya tashi ya warke sarai ..

Mlm abu yace alhaji ishaq kana da wata kima ta daban a idona hakan ne yasa duk nike neman afuwar ku yaro kuma Allah yabashi lafiya duk aka ce Ameen ... sannan

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 21

Cikin gidan kaf bbu wanda yasan da zance yuwuwar auren Abdullah ,hatta mami da kanta illa iyaka taga ana ta gyare gyare ta koina part din Abdullah kuwa gabadaya sai da aka canza masa tsari ,to mami dai tasan ana yawan yimusu gyara kusan duk karshen shekara Amman ba kamar wannan ba domin yadda ta ga dady ke rawar jikin bari da kudi a cikin gidan tasan wannan ya zarce gyaran kowace shekara ,zuciyarta tarinka mata zargi iri iri koda ta tambaye sa game da gyaran sai ya sanar da ita kawai saboda Abdullah ne zai dawo wani sati ..
Mami tariga tasan yadda Abdullah din yake da matsayi a gurin dady shi yasa bata bawa ranta komai ba Amman duk da haka tasake fahimtar Abdullah ya kara karfi a zuciyar ubansa...

Faiza kuwa kmr tayi karamin hauka dan dadi tawa mama hafsa waya tasanar da ita dawowar Abdullah har gidan gyaran jiki faiza taje aka mata duk dai akan dawowar Abdullah Mama hafsa daman tayi kwana biyu da tafiya dan haka tana jin wayar faiza tayo shirin tahowa...

Duk wani tsari da shiri sai da dady yakusan kammalawa da shi dan hatta AV na daurin aure ya fito duk inda zaije tsakanin danginsa dana mami yan'uwa da abokan arziki kusan kowa ya isa gareshi hatta sokoto ya aika sabanin da aka samu ranar da mm hafsa ta taho a ranar katin ya isa dan haka itama batasan da zance daurin auren ba har ta iso ...

Dady yatafi Germany ana sauran kwana shida daurin aure aranar da ya sauka Abdullah yabar hospital da yake zuwa wani shiryayen plat house wanda Dady ya siya da sunan Abdullah tun ba yau ba" bawani babba bane Amman tsarinsa yayi matukar birge Abdullah a daren dady ya zubewa Abdullah AV din daurin aure cikin sanyi jiki Abdullah ya janyo ya fara dubawa dady yacigaba zamu koma zuwa jibi da yamma domin ranar jumma'a yakama daurin aure mun gama magana da doctor jack idan an daura auren upper week zaka dawo tare da yarinyar nan acigaba da duba lafiyar ka "dan haka wannan gidan na siya da sunnanka ko byn Raina cikinsa ne zaka zauna idan ka dawo ba'a asibiti ba doctor zai dinga zuwa nan yana duba lafiyar ka ... Dady yadan tsagaita sannan yacigaba akwai bukatar a siyawa yarinyar nan kayan sawa wanda zatayi amfani da su anan domin can mahaifinta ya hana ayi mata ko dai dai da zani daya ...

Abdullah bai gane a yanayin da yake ciki ba dan haka hawaye kawai yaji na farinciki yana zubo masa wanda rabon hawaye a fuskarsa ya jima kai bama zai iya tunawa ba "ya kwanta nan gaban dady yana Yi masa godiya dady ya dafa kansa yace A'a Abdullah ba komai kai ma Allah yayi maka albarka sanadin ka na samu cigaba a rayuwa wanda bazasu lisafu ba.. farinciki Abdullah yaki boyuwa bai san yadda zai misalta wannan ranar ba ,daga can kuma ya dan natsu har da dan tsoro a fuskarsa ,dady ya fahimci sauyawarsa ya tambaye shi cikin sanyi jiki yace dady mami fa?..
Chapter 28 · 0% Book details