Sashe 10
Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yakira sunanta cikin tsanyi murya Aisha are you ok ? ahankali ta daga masa kai ya zuba mata manyan idanunshi hade da kamo lip's dinshi na kasa yana cizawa ahankali "let me allowed you to rest "tayi shr still har yanzu taki tace komai ,ita kadai tasan abinda take sakawa a ranta " ko kadan hausar bakinsa bata fita da kyau hakan yasanya gara yayi da turanci zai fi masa sauki yakan dage yayi hausar a gurin dake da mahimmanci a wajen sa ,ya furta zai tafi yafi akirga Amman still yakasa barinta tashiga gida ya xura hannushi duka cikin aljihun wando sa yakara step biyu zuwa gabanta yana sake hango tsoronta a Fili yana kallon yadda ta gigice take fidda numfashi da sauri da sauri "ya runtse idanunshi tare da jin haushin kansa sai yabude baki da niyar sanar mata da sakon zuciyarsa Amman sai dai yaji hakorin sa sun datse harshen A'a bazan iya ba Aisha tayi kankata dayawa "Brain dinta bazai iya daukar wannan Kalmar ba yafi bukatar ya nuna mata A aikace duk a zuciyarsa yake wannan furucin yayinda idanunshi kai kanta ko kifta su yakasa ya salam ya furta akasan ransa jin hucin numfashinsa a fuskarta yasa tadan ja baya kadan ,gabadaya tarasa natsuwa zuciyarta ke beating sosai" sai kusan karfe goma na dare ya barta ya wuce badan yagaji ba sai dan yabarta ta huta.
Cikin sati nan biyu ya zamewa Abdullah jiki dole ne kullum sai yaje yaga Aisha sannan yake samun bacci da kwanciyar hankali musamman da yake mami na da bakuwa bata wani bincike kan yawan fitarsa da dawowarsa haka nan a bangaren Aisha iya kuluwa tayi da Abdullah domin duk yadda taso ta raba kanta dashi yadaina zuwa abun ya gagara ,da alama yasamu karbuwa a gidan ,ta fahimci Abdullah yagama gane aladar babanta ne zama a kofar gida duk dare ,dan haka yana zuwa kai tsaye mlm abu ke turawa tazo haka nan halayyar Abdullah ce yawan kyauta kullun ne idan ba'a aiko salis da abu ba to zai turo musa ,ba Aisha kadai ba hatta su salis suna yabawa da Abdulla da irin wannan halaiyyar tasa" hakan yasa ko zance Abdullah aka tayar wani lokacin a gidan sai ta shigewarta daki ta banko kofa sai ma ta wuni bata ci abinci ba saboda an yi zancensa dan ita bata ga abun birgewa a wajen sa.
A bangaren Abdullah kuwa yagama fahimtar inda Aisha ta dosa duk da bai sanar da ita abunda ke cin zuciyarsa ba Amman shi ya danganta rashin sakewarta har da karancin shekaru a ganinsa kurciya ce tasa takasa fahimtar sa Amman akwai lokacin da zata fahimce sa awajensa duk abunda zatayi sake birgesa takeyi .
Idan yazo yakan sake sosai da mlm abu suyi hira kafin A kira Aisha"Kuma yana karuwa da hirar mlm abu domin akwai ma'ana a duk maganar da zai fada ,a wajen mlm abu ma har cikin ransa yakejin Abdullah ya kwanta masa duk da yake da ganin Abdullah din zaka San daga gidan manya ya fito , Amman hakan bai hana shi shiga cikinsu ba sau Tari duk dare idan usman ya siyowa mlm abu goro shike karfa da akwai buta nan kusa ya wanke wa mlm abu ya bare sannan ya Mika masa, har ya zamanto shi din ma idan ba mantawa yayi ba duk zuwa sai ya kawo wa mlm abu goro.
Da yammacin ranar lahadi Aisha na sharar tsakar gida sai ga sakina ta shigo da sauri Aisha ta Yar da tsinsiya hannunta, suka rungume juna suna dariya ,rabon da su ga juna ko wani labarin tsakaninsu kusan sati hudu kennan tun kafin tafiyar sakina mina, byn ta gaishe da inna suka shige daki suka fara bawa juna labari sakina ta fito da tsarabar mina ta bata sannan cikin tsanyi jiki tace sister tare muke da bakonki fa yana waje .
Cikin mamaki Aisha ke kallonta bakona Kuma ?
Sakina tace wallahi Ahmed ne dan gidan mama hauwa tun randa mukaje dubota asibiti ya ganki shine yayi ta damuna Kar ki ga irin kakkauce masa da na dinga yi saboda sanin halinki Amman ya nace shi kawai in kawoshi sai in barshi dake ,dan Allah sister ki taimake ni ki leka wallahi tun kusan 12 yau yake zaune agidamu ya tasani gaba wai sai munzo .
Wani irin kallo Aisha kebin sakina dashi abu daya take jin rashin zuwanta wajen bakon zai sanya sakina taji ba dadi gashi tanason suyi hirar yaushe gamo ,baki ta dan tabe gami da gyada kafadarta any way ki sanar da inna tukun .
Cikin murna sakina ta rike hannunta tace am so happy thank you sister sannan tafita gurin Inna .
Kasancewa yammace bbu mutane sosai a cikin layin haka nan kofar gidan nasu ba kowa shi yasa suka tsaya a waje ita da Ahmed batare da sun shiga ciki soron gidan ba" ita dashi ne kawai tsaye dan sakina taki rakota hakan yasanya Aisha yi kicin kicin da fuska har ta sanya Ahmed din ya dinga inda inda yakasa yi mata magana .
Kanta a sunkuye taji yana kokarin son fahimtar da ita Kalmar so nan da nan tadago kai da nufin dakatar dashi Amman me sai cin karo tayi da idanuwan Abdullah cikin nata suna nufowa inda suke shi da wani da bata San kowaye ba ,ta dake taci gaba da tsayuwar karfin hali Amman haka nan taji zuciyarta na harbawa ,cikin kamewa da tafiyar mutunta kai ,su Abdullah suka karaso har suka shige su ,ganin sun shige inda suke yasanya Aisha sauke numfashi ta tsiri murmushin dole har Ahmed ya tambaye ta tace ba komai .
Shi kuwa Abdullah duk wata wuta dake jikinsa sai da ta dauke bai taba jin wani irin mugun kishi daya ji yau yana jin tamkar zuciyarsa take barazanar tarwatse gawani dake tsatsafowa masa ya cire hanky daga bayan aljihun wando sa a tsanake ya gogewa Amman kallon daya zaka masa kasan baya cikin natsuwarsa " komai ya tsaya masa cak tsammaninsa rashin fitar da Aisha take Yi yasanya Maza basu farga da ita ba ashe abun ba haka bane ,kinyiwa Dr sagir magana yayi sai da suka kai karshen layin suka sake juyowa suka zo suka shige su Aisha suka tafi batare da ya sake kallon inda suke ba ,barin su gun ya sanya itama taji gara ta tafi ,ta masa sallama ta shige gida abunta tana shiga ta tarar da usman da sakina ne a tsakar gida suna hira tana yiwa inna gyara kayan Miya sakina tace kai sister ashe anyi wani sabon handsome Abdullah shi ne bamu sani ba .
Aisha ta harari usman don tasan shi ya fesa mata tace dan sa ido banza kawai har suka shiga dakinta sakina nacewa A'a sister ni gara ki sanar mana kada Ahmed ya kwallafa rai . Aisha dai bata kulata ba har suka zauna tasake cewa kisanarmin da gaske ne maganar da usman yagayamin ,waye Abdullah ?
AISHA ta kalleta tace dan Allah sister ki manta da wannan zance muyi hirar mu yaya mina ?
Tun magarubar farko Abdullah ya sallame salis haka nan yace musa ma ya tafi sai zuwa gobe , sallah ishai a kofar gidan mlm abu tayi masa dan tare suka yi jam'i sallah da mlm abu byn an idar ne Abdullah yasami mlm abu yace shi dai yazo ne yana nema a gurin mlm abu daya bashi auren Aisha ,mlm abu ya zubawa Abdullah ido kana kallon Abdullah zaka gane irin mutane nan ne da ilimin boko ya yaratsa su tare da wayewa da natsuwa , uwa uba gata da jin dadi dake jikinsa ya nuna karara "sannan kamannin Abdullah din da yanayin sa ya nuna wata kabila ce da ta bambamta da hausa , hakan ma zai iya kawo wata matsalar wajen yuwar abun akwai baiwa da da natsuwa dake tattare da yaron hakan yasanya mlm abu ya dade yana tunani yuwar abunda yaron yake so"domin dai su din ba wasu bane Amman sai gashi Abdullah din da kansa ya durkusa gaban shi yana nema daya bashi auren diyar sa Aisha mlm abu yayi murmushin game da gyara murya sannan yace Abdullah ni kam dai ta bangarena dama mahaifiyarta haka muka fi so ace Aisha tayi aure yanzu domin shekarunta sunja a yanzu Aisha kadan yarage tacika sha takwas inda watan 12 ya tsaya da kwana 14 in banda karatun da ta tsaya yi da tuni ta dade a dakinta hakan nan Kuma nine mutun na farko da zai Yi farinciki da kasancewarta matarka.
Mlm abu ya numfasa sannan yacigaba Amman duk da hakan Abdullah bazan iya aura Maka Aisha ba tare da hadin kanku ba ma'ana bazan iya aura Maka Aisha ba sai ta amince da tana sonka domin shi aure ana yinsa ne dan mutun biyu matukar bbu jituwa tsakanin maaurata bbu abunda zai je yadawo illa rashin kwanciyar hankali. haka nan kaga Aisha ita kadai gareni Diya mace duka yayana Maza ne shine naci alwashin duk namijin da ta zaba matukar na duba naga yadace zan bata shi ", banason na mata dole dan haka Abdullah abinda nike so gareka kaje ka nemo so gurinta matukar kun hada kanku ,ni ne mutun na farko da zan soma murna km da yarda Allah nabaka Aisha .
Wanna shine KAKA KARA KAKA Amman duk da haka ya fahimci abinda mlm abu yake nufi shi kansa ya Karu Kuma hakan ya karawa Aisha kima a gurinsa domin yanzu dai yasan ko bbu komai yasan mlm abu ba zai taba mata auren cin fuska ko na kudi ba wannan ya nuna ita din mai daraja ce a gurin iyayenta Kuma ko da Allah yayi shi din ne zai aure ta yasan badan kudinsa suka bashi ba , kodan wani abu nasa ba .