Sashe 9
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ta je gidan ta shige abin ta ko sallama bata yi ba ta ajiye ƙullin kayana tana mamakin kayan da suke ciki domin ta ji da ɗan nauyi, tana cikin buɗe ƙofa Malam Nura da ya dawo daga majalisa ya shigo ya rufe ƙofar gidan, baki ya buɗe zai kwaɗa sallama, domin ransa fari ƙal Kuluwa tana gida, duk da ransa da sauran ɓurɓushin ɓacin ran kayan da Hadiza ta ambata zai yi mata. Sallamar ce ta maƙale, baki sake yake kallon ta ita da ƙullin kayan ta, Kuluwa kuwa ko kallo bai ishe ta ba ta buɗe ɗakinta ta kinkimi kayanta ta shige. Har ya ƙaraso ɗakin ƙofar ɗakin bakinsa a buɗe shi ya rasa tsakanin Hadiza da Kuluwa waye yake addabar rayuwarsa. Labulen ya bankaɗa lokacin ta kunna fitila tana since ƙullin za ta mayar da kayan mazauninsu.
Yana bin ta da kallo ya ce
"Waye ya je bikon ki?" Ƙugu ta riƙe da hannu biyu ta ce
"Ni ce nan na bikato kaina, kuma wallahi idan ka ce kule casss zan ce, in banda ma maza baku da kunya kai kana da idon da za ka kalleni, ka zauna ka sharara mini ƙarya da daɗin baki ashe dai duk bula ce" Da yatsa ya nuna ta ya ce
"Wallahi kika ƙara ambata cewar ina ƙarya sai ranki ya ɓaci" Ƙaramin tsaki ta je ta ce
"Ya daɗe bai ɓaci ba" Fuuu ya fice daga ɗakin, sai kuma ya dawo ya ce
"Ki shirya ƙunsar takaici idan amaryata ta tare domin da ƙafafun ki za ki fice ki yi yaji"
Baki ta taɓe ta ce
"ÆŠan halak ka fasa!.
Yana saka ƙafarsa a ɗakin tamkar da kiran Hadiza ya shiga, sai dai filashin ne ta masa, hakan ya sanya ya doka tsaki yana faɗin
"Uwar son kuÉ—i ai wallahi kin gamu da gamon ki domin zani ce ta tarar da mu je mu" Ya faÉ—a yana doka mata kira ya zauna a bakin katifarsa, tana É—auka ta ce
"Nura wai mai ya sa kake so ka nuna gazawarka ne?" Harara ya galla mata ta wayar ya ce
"Shigowa ta gidan kenan, ina jinki gimbiyar mata, autar mata" Bata tanka masa ba ta ce
"Maganar kayan da na maka, nawa da na Æ´aÆ´anka" Gabansa ne ya faÉ—i ya fara tunanin ita kuwa mai haÉ—a ta da sabgar cikin gidansa da har za ta ce ya yi wa yaransa wani kayan fitar bikin ta.
Yana É—an gyara murya ya ce
"Haba Hadiza su Kabiru duk suna da kaya fa, wallahi ba za su rasa yadin da za a saka musu ba kin ga ba auren fari ba ne bare na ce zan yi ta wadaƙa da kuɗi, wannan aurena na ashirin ne, kin ga Haule ce matata ta farko, kuma na mata kishiyoyi goma sha takwas kin ga idan aka haɗa da ita goma sha tara ke ce ta ashiri... Bai ƙarasa ba ta ce
"Malam Nura ban tambaye ka wannn dogon bayanin ba, ni kaina na sani wannan ne karon farko da zan aure ka, sannan da kake maganar su Kabiru ni ina ruwana da wasu su Kabiru? Ni fa ban san ma Æ´aÆ´anka mata ne ko maza ne ko kuwa maza da mata ba ne, da har zan ce ka musu É—inki"
Yana sauke ajiyar zuciyar jin daÉ—in ashe shi ne bai fahimta ba ya ce
"Allahu akbar wallahi zatona su Kabirun kike nufi da kika ce Æ´aÆ´ana" Tsaki ta doka ta ce
"Ni da su Zainaba nake ita da Shafi,i" Dakyar ya samu zarafin amsa mata ya ce
"Mai za a musu Hadiza???" Jin tambayar tashi kamar da gayya ta ce
"Bari na maka gwari gwari, kayan fitar biki nawa da nasu za ka mana, ai su ma ƴaƴanka ne ko kuwa ƴaƴana ne ni kaɗai?" Wani ƙululun baƙinciki ya haɗiye ya ce
"Wane mutum in ji mutuwa, ya za a yi in ce ba Æ´aÆ´ana ba ne, ai da an mutu har liman, ai Æ´aÆ´anki Æ´aÆ´ana ne"
Ta ce
So nake ka mana É—inki iri É—aya mu saka ranar É—aurin aure har kai da kuma su" Karaf ya yi ya ce
"Ki muku a wanann kuɗin dana baki, ni daman na ba Hudu saƙon shadda kano zan ɗinka" Ta ce
"Wato ma ka bashi to wallahi ka bashi namu ya siyo iri ɗaya idan ba haka ba ka zo ka karɓi kuɗinka na fasa auren" Tana kaiwa nan ta kashe wayar.
Zamewa ya yi daga kan katifar ya yi zaman ƴan bori yana jin ɓacin rai, ba komai ne damuwarsa ba yadda ya bada kuɗin shaddar dubu ashirin amma yanzu ana cewa ya ƙara, duk wayar da yake Kuluwa tana laɓe, sai da ya gama ta juya ta koma ɗakinta tana jijjiga kai tana mamakin wannan wace irin amarya ce tana saƙawa a ranta dole ta yi fito na fito da wannan amarya domin ta lura za ta sha gabanta a wajen miji.
Katifarsa ya janye bayan ya rufe ƙofar, ya tashi ya leƙo window ganin babu kowa ya koma ya shiga tona tsakiyar inda ya ajiye katifar, yayi tono sosai sannan kuɗi suka bayyana yan fito da su yana kuka mai cin rai, a fili ya ce
"Ni dai wannan so ya zame mini jaraba ma ba jarabawa ba, ta yaya a ce Æ´aÆ´an bazawara ma sai ka musu É—inkin fitar biki" Dubu talatin ya lissafo ya ce ita dubu sha biyar yadi uku su ma Æ´aÆ´an yadi uku, ya mayar da ramin ya rufe ya mayar da katifar yana kallon kuÉ—in gabansa yana faÉ—uwa yana tunanin da wannan kuÉ—in sai ya auri kusan mata uku amma wai iya hidimar amarya da Æ´aÆ´anta ne.
Haka ya kwanta da kuɗin a aljihu yana saƙa da warwara. Ko da ya fita da safe zai kai wa Hudu har ya tafi Kanon sai wurin mai pos ya kai aka tura masa ya masa bayanin cewar iri ɗaya zai siyo shaddar, sannan ya kira Hadizar ya ce ya bayar sai dai abin mamaki ko godiya bata masa ba lamarin da ya sanya cikinsa kaɗawa.
Da dare Hudu ya dawo sai dai basu haɗu ba sai da safe, ya basho shaddar blue ta yi kyau sai ƙamshi take, haka ya ɗauki tashi ya kai ɗinki ya kai mata tasu, a haka ma sai da ta karɓa musu kuɗin ɗinki a wajensa, shi ya rasa wane dalili ne ya sa ya zama kamar wani sauna a wajen Hadiza.
Kwana biyu aka ɗinka masa shaddar ta sha aiki ya kai aka goge, sai dai ya saka a ransa idan ya saka ranar ɗaurin aure cirewa zai yi ya samu ya fansar ya karɓi kuɗinsa domin ba zai saka shadda mai tsada haka ba.
Tun daga zauren gidan yake karaÉ—i yana faÉ—in
"Ga angon Hadiza nan, lallai Hadiza ta ciri tuta, wannan shaddar ko a aurena na farko nan saka ba, amma sai gashi a aurena na ashirin zan saka, Allahu akbar kabiran" Ya faɗa yana kara shaddar a jikinsa, Kuluwa tana kallonsa ta windown ɗakin ta amma bata fito ba, baƙinciki kamar ya kashe ta tana cin alwashin da ita kaɗai ta sani.
Haule ce ta fito tana ta zuga shi tana wasa shi, haka ya ringa mata ruwan sanya albarka.
Tun da ya faÉ—i cewa ba za su sake shiga turaka ba, babu wacce ya bari ta shiga, magungunan da aka haÉ—o masa ne yake ta narkawa cikinsa shi ala dole mai amarya.
Ranar asabar, wacce ta kasance ranar ɗaurin aure, ango kansa ba rawa yake ba gilgilwa yake domin a yau ne sabuwar amarya za ta tare da daddare. Ana shirin tafiya ɗaurin ya baro su Hudu da sauran abokansa, sai wasu makaɗa da duk suka karaɗe layin da kaɗe-kaɗe suna ta waƙe ango suna ambaton sunansa da sunan amarya!.
Baki a washe ya cika roba fal da ruwa ya kai banÉ—aki, ya dawo ya cika bokiti ya nufi bayin Haule wacce take gyara É—aurin É—ankwali ta ce
"Ango yau ruwan wankan har makayi biyu" Bokitin ya ajiye ya washe baki ya ce
"Allah ne kaɗai ya san daɗin da nake ji yau Haule, ji nake kamar na ɗaga ruwan gidan nan na sheƙe a jikina" Da dariya ta tuntsure tana faɗin
"Idan ka sheƙe duka ruwan ina muka kama muka riƙe, da wanne za mu yi aikin gidan, gwara dai ka je da guda biyun" Shi ma dariyar ya yi yana ɗauka ya shige banɗaki ita kuma ta shige ɗakinta.
Kuluwa da take leƙosu daga ɗaki tana banka musu harara ganin babu kowa a tsakar gidan ta fito riƙe da ashana a hannunta, da sauri ta nufi ɗakin Malam ta ga shadda a kan katifa tana ta sheƙi ga wayarsa da kwalbar turare a gefe da kuma hula, baki ta taɓe ta ɗaga rigar ta ɗauke wandon ta fito, bayan ɗakinsa ta nufa ta ƙyasta ashanar ta saka a jikin ƙafar wandon, saj da wutar ta cinye gabaɗaya ƙafafun wandon ya koma gajeran wando mai iya cinye sannan ta saka ƙafa ta take, wutar ta mutu ta ɗakko wandon ta linke ta je ta mayar mazauninaa ta fito daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta garƙama sakata!.
MAMAN AFRAH
09025576222
[4/9, 6:17 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
🅿ï¸5ï¸âƒ£
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*
*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿5⃣
*KULUWA*