Sashe 8
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nura saboda wulaƙanci ka sako min ƴar shi ne ba za ka barta ta taho ita kaɗai ba sai ka kawo min ita saboda rashin ta ido" Kuluwa har hawayen baƙincikin kishi ya silalo mata domin ta fara tunanin saboda amaryarsa ya dawo da ita gida, ba komai ne ya sanya ta zubar da ƙwallar ba sai tunowa da ta yi da irin barikin da Malam ya nuna mata ta yadda ya yudare ta ya kawo ta gida. Cikin muryar kuka ta.ce
"Wallahi baka isa ba" Mahaifin ta ne ya tsawatar mata, ta ja bakinta ta yi shiru ba tare da son ranta ba, Malam ya ce
"Ya kamata a barni in mutu kafin a binne ni, ni dai babu wanda ya ji na ambaci kalmar saki don haka bam saki Kuluwa ba" Wata nannuyae ajiyar zuciya Kuluwa ta sauke, saboda kalmar nan ta mata mugun daÉ—i, don ta fahimci cewar har yanzu tana da sauran damar da za ta hana shi rawar gaban hantsi dangane da wannan la,anannan auren da ta tsana, saboda ta san tun da har ya kawo ta gida a kan maganar auren ne.
Mahaifiyarta cike sa takaicin cin fuskar da aka yi wa Æ´arta ta ce
"To a kan me za ka kwaso kaya ka kawo ta gida?" Kafin ya furta wata kalma ta juya wata tambayar ga Kuluwa tana faÉ—in
"Ke Kuluwa ba cewa kika yi gaishemu kuka zo ba? Har kina faÉ—in yana wajen zai taho da sabulai, amma yanzu muke jin wani sabon al,amari?" Kuluwa ta ce
"Wallahi ba ƙarya na yi ba haka ya faɗa ... Babanta ne ya ɗaga mata hannu ta yi shiru tana goge guntun hawayen da ya zubo ya mayar da kallonsa ga Malam Nura cikin kakkausar murya ya ce
"Nura wane dalili ne ya sa ka dawo da ita gida tun da babu saki tsakaninku?"
Gyaran murya ya yi tamkar wanda zai yi kiran sallah, har sake nannagawa yake sannan ya ce
"Na dawo da ita gida ne ta zauna tsawon watanni uku ko huÉ—u" GabaÉ—aya kowa idanu ya zuba masa, mahaifinta ya ce
"To ina ga ko sakin ta ka yi idan ta yi wata uku ai ta yi idda, wane dalili ne zai sa ka kawo ta gida ta zauna har tsawon wata uku ko huÉ—u?"
Kuluwa ta yi karaf ta ce
"Wallahi ba zan zauna ba ƙafata ƙafarka" Babanta ne ya nuna ta da yatsa ta koma ta zauna tana jin kamar ta shaƙo Malam ta masa shegen dukan da ko cewa aka yi ga mace ba zai yi sha,awar kallon ta ba ma bare har ya ce zai aure ta.
Mahaifiyarta ta ce
"Banda sakarci namiji yana yakice ki, ke kina manne masa, shi kaÉ—ai ne autan maza? Wallahi albasa dai bata yi halin ruwa ba, ni namiji yana cewa kama gabanki nale nufae gidan iyayena don gidansa bai fi na iyayena ba... Babansu Kuluwar ne ya dakatar da ita.
Malam Nura ya ce
"Daman rawar kanta ne ya yi yawa, tana ƙetara maganata a cikim gidan, kuma ita Haule ba haka take yi ba, na basu kuɗin faɗar kishiya ɗari biyar biyar amma Kuluwa tana karɓar kuɗin nan yadda ka san ta samu tsohon tsumma haka ta yayyaga ɗari biyar ɗin wai ta raina"Babanta ya ɗauki salati sai da ya salance kowa yana jiran dalilin salatin nasa ya ce
"Amma Kuluwa an yi ƴar banza, yanzu kuɗin kika yaga naira ɗaiɗai har ɗari biyar?" Ran mahaifiyarta ne ya ɓaci ta ce
"Haba mai gida ina tsiya ina wata É—ari biyar a faÉ—ar kishiya, maganar kishiya ake yi fa wallahi ta min daidai ai ko dubu biyar ce gwara ta yaga" Baban Kuluwa ya ce
"Ai ka ji ku mata daman ku kuke ɗaurewa ƴaƴanku tsantsa, ina laifin ɗari biyar gado ba na uwarka ba aka baka ƙyallan zani ai an mutuntaka, idan bai bata ɗari biyar ɗin ba ma ba wai ƙwata za ta yi ba" Malam Nura ya murmusa alamar jin daɗi ya ce
"Wallahi tana neman takura min ne, kishin ta ya yi yawa, to babban dalilin da ya sa na kawo ta ma, na basu hutun zuwa turaka, ka san abu in ya shafi gidan aure to babu waji ɓoye-ɓoye ko jin kunya, to na ce su haƙura da zuwa taraka har sai amarya ta tare ita ma, to Haule ta yarda don wallahi har naira ɗari na ƙara mata... Baban Kuluwa ya katse shi da faɗin
"Allahu akbar ka ga mai rabo, wata bayan ɗari biyar ɗin ka ga ai ta tashi da ɗari shida" Ran Kuluwa ya kai ƙololuwa wajen tashi, daman ta san babanta yana ja mata raini.
Malam Nura ya É—ora da faÉ—in
",To ita tana da taurin kai jiya ma a ƙofar ɗakina ta kwana wai sai na buɗe" Mariya da Hinde jin maganar ta fi ƙarfin su cike da kunya suka tashi suka shige ɗakinsu. Mahaifiyarta kuwa sai saƙon harara take aika mata jin zubar da ajin da take yi a kan mijin da ko damuwa da ita bai yi ba
Mahaifinta ya ce
"Wannan kam bai kyauta ba, ke da kika je zaman aure ina ruwanki da aurensa, kuma duk dokar da ya shimfiÉ—a ai sai ki ce to" Ya juya ya kalli Malam Nura ya ce
"Amma sai ka ce a mata faÉ—a ba wai zaman gida har watanni ba"
Malam Nura ya ce
"To a mata faÉ—an don aurena da Hadiza babu fashi" Baki sake take kallonsa tana tuna magangnun da ya faÉ—a a hanya amma yanzu har ya sauya ashe rami ya mata ta faÉ—a ba wai fasa auren ya yi ba, ita har da cewa daga gidansu su je gidan su Hadizar a zuciyarta ta ce
'Lallai namiji munafuki ne'
Mahaifiyarta takaici ne ya hana ta sake furta komai Babanta ne ya ringa faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake shiga ba, sai da aka kammala amma Malam Nura da ƙarfin hali sai ya ce
"To amma ta zauna ko sati ɗaya ne ta yi ta koma daga baya" Babanta ganin abun ba na ƙare ba ne sai ya amince Kuluwa tana ji tana gani Malam Nura ya musu sallama ya fita ranta in ya yi dubu ya ɓaci don ta lura kawai so yake sai ya gama ɓarzar amarci sannan ta koma amma duk da haka ya yi gudun gara ne ya tare a gidan zago don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, don ko a su ko a ita wanna amarci babu wanda zai ci shi ta daɗi!.
Malam Nuwa kuwa yana fitowa waje ya yi wata miƙa haɗe da yin hamdala a fili ya furta
",Na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda, ina dalili mace kamar cingam, ai wallahi ba don kar na sake ta na yi asarar dubu goma ta ba da sakin ta zan yi, ko kuma in sake ta idan na gama amarcin na dawo da ita?" Ya sake jefawa kansa tambayar, sai kuma ya kaɗa kansa ya kama hanyar zuwa gida.
Yana dab da zuwa gidan kiran Hadiza ya shigo, ya ɗaga ta balbale shi da masifa a kan cewar idan har basu yi maganar kayan da za ta saka a fitar biki ba to wallahi tana iya fasa aurensa, babu yadda ya iya ya shiga bata haƙuri yana faɗin yanzu zai je gidan ya fita wani abu ne.
Ta saki gajeran tsaki irin na kai ya dama É—in nan ta ce
"Ka turo min kuɗin katin wayar da na kira ka, don ni ba a yi kuɗin katin wayata don kiran namiji ba, shi namiji shi ya dace ya bautawa mace" Shiru ya yi yana nazarin maganar ta, wato shi namiji shi ne wahalalle, bayan ya san kuɗin da take saka katin daga jikinsa take ɓanɓara.
A zuciyarsa ya ce
"Anya wannan za a yi abin arziƙi da ita kuwa in ta shigo gidana, tana titi ma katin waya ma ba za a mora ba to ina ga in ta shigo gidan za take siyan kayan miya idan na bada hatsin tuwo kuwa?' Kansa ya tamabaya yana ta wasi-wasi duk da bai gama yanke hukunci ba amma dai ya san cewar dole a more ta saboda yana ganin duk burga ce ganin tana gidansu amma in ra shiga gidansa sai yadda ya yi da ita.
Haƙuri ya bata ya fasa shiga gidan ya nufi wajen mai siyar da kati ya saya ya tura mata, maimakon ya dawo gidan sai ya nemi waje ya zauna a majalissa ake ta hira.
Kuluwa kuwa haka ta kinkimi ƙullin kayan nata ta nufi ɗakin su Mariya, ranta duk a ɓace sai dai ta yi alƙawarin ko ana mutuwa ana falkowa yau a gidan mijinta za ta kwana!.
Babansu yana jin rediyo yana hamma, can da ya gaji ya kwashi rediyon ya shige ɗakinsa, haka ma mahaifiyarta tun da ta ce ta zubo mata tuwo ta ƙi sai ta watsa yinta, don ta lura Kuluwa ta yi nisa a rakiyar ɗa namiji ba za ta ji kira ba, hakan ya sa ta shiga ɗaki ta hau gadonta ta miƙe ta shiga sakin munshari.
Baba ya taso ya saka sakata a gidan ya koma ɗakinsa, su Mariya ma tun suna hira suna zagin Malam Nura Kuluwa tana kare shi, har kowacce bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Kiran sunansu ta shiga yi amma ɗif, tasowa ta yi ta fito ta nufi ɗakin Baba tun kafin ta ƙarasa take jiyo tashin munsharinsa, ta leƙe ɗakin mahaifiyarta nan ma baccin take, saɗaf-saɗaf ta koma ɗakin su Mariya ta sungumo ƙullin kayanta ta ɗauki takalmi a hannu ta nufi hanyar ficewa, a hankali ta zare sakatar ta ja musu ƙofar ta saka takalmin ta yi fiyarta.