← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka rabu da su kowacce ka san daidai da zamanin ta nake ita ma Hadiza dama ce na ara mata, sai ta shiga gidan zan nuna mata asalin waye malam waye Malam Nura don duk wannan iyayi da juyannin da take kamar waina a tanda ba É—orewa zai yi ba, idan har na wawuri abin da zan wawura na daga dukiyarta to da wasu daga cikin kuÉ—in zan yi amfani in gallo wani sabon auren!" Hudu yana kallonsa yana jijjiga kai ya ce

"Ka ƙaddara gidanka ya kama da wuta kenan, don ni yanzu haka ina hararo irin zaman da za a yi tsakanin Hadixa da Kuluwa" Tsaki ya ja ya ce

"Rabu da su daidai da su nake, kowacce ta yi tsarara kamar shayi!"

Ayarin jama,a suka biyo makaɗa suna aikin su na kaɗe kaɗe, ango sai wani jin kansa yake, yana tunano irin garar da zai kwasa idan an kai amarya ta tare, don yanzu yana tunano cewar la,asar sakaliya tana yi zai aarasa haɗe sauran magungunan da Hudu ya siyo masa a Kano ya shanye don ba zai tsaya kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa ba!. Dole ya sha amarci don yana rayawa a ransa cewar Hadiza sai ta yi wata guda currr tana amarci kuma ita kaɗai ce za take zuwa turaka amma su Kuluwa sai dai suke tuƙa tuwo babu mai zuwa ɗakin miji, ya saka hakan a ransa sai dai a yi wacce za a yi duk nacin Kuluwa kuwa dole ta haƙura su barwa amarya Hadiza turaka daman ya san ita Haule baiwar Allah ba za ta ƙi amincewa ba, Kuluwa ce uwar ƴan taurin kai.

Ana tafiya Hudu yana danne dariyarsa idan ya kalli Malam Nura ya san ƙarfin hali ne domin duk da yana cika baki amma ya lura yana tsoron Hadiza ta ce ba za ta yi hoto da shi ba. Gabaɗaya mutane kowa ya kama gabansa, daga Hudu da Malam Nura sai wasu abokansu guda huɗu ne suka nufi gidan su Hadiza, don masu kiɗan ma Hudu ya ce su je can gidan Malam Nura su jira su.

Suna tsaye a ƙofar gidan abokansu suna ta zolayarsa, sai yaƙe yake musu don hankalinsa ba a kan su yake ba, yana fatan ya tsallake rijiya da baya. Wayar Hadiza ya shiga kira, Hadiza kuma ganin kiransa da sauri ta tashi daga cikin mutane don daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, damab kar jira take saboda ta yi ta kira bai ɗaga ba, yanzu kuma faɗuwa ta yj daidai da zama tun da gashi ya kira da kansa, har sauri take don ta shiga ɗaki ta kora masa kashedin kar ma ya dosk gidansu idan aka ɗaura auren nan, domin ta fasa hoton sannan ta ƙara faɗa masa cewar ya aiko da takardar saki ta fasa auren. Tana dab da shiga ɗakin Babanta wanda shigowarsa kenan sun dawo daga wajen ɗaurin auren ya hango ta ya ce

"Ke Hadiza!" Da sauri ta juyo ta ce

"Na,am Baba"

Yana kallon ta ya ce

"Malam Nura ba ke suke tsaye a waje suna jira ba, shi ne kika bar su a tsaye"

Ranta ba don ya so ba ta ce

"Yanzu zan fita daman" Ɗakin ta fasa shiga ta juyo ganin Baban ya ja ya tsaya, Bintu ma ta tashi, sauran ƙawayen ma duk suka fara miƙewa suna faɗin

"Ah lallai ashe ango ya samu ƙarasowa bari mu je" Hadiza kamar ta yi inu haka ta ji, amma babu yadda za ta yi, haka ta biyo bayansu suka fito. Baban ma juyowa ya yi yana faɗin

"Zainaba É—akko mun kujera zan fita waje saboda masu zuwa, wanda suka rasa É—aurin aure" Zainaba wacce take sanye da shaddar ta ta taso ta É—akko kujerar ta biyo bayansa.

A can ƙofar gida kuwa Malam Nura ya fara zargin ko dai wani ya ƙyanƙyasawa Hadiza cewar bai saka kaya ba, gani yana kiranta bata ɗauka va, wata zuciyar kuma tana faɗa masa ko dai kiran da ta yi ta masa ne bai ɗauka ba ya sa ta ƙi ɗauka.

Kamar daga sama ya hango ta sun fito ita da ƙawayen ta, gabaɗaya tsabar kyan da ta yi ya sa kwata -kwata ya sha,afa da kayan jikinsa, kwalliya da ɗaurin ɗankwalin Hadiza sun tafi da hankali da tunaninsa, bai ma lura da yadda ƙawayenta suke rarraba idanun neman ango mai sanye da shadda kalar ta ƙawarsu amarya ba.

Hadiza kuka ne kawai bata saki ba, gashi babu halin ta masa wani rashin mutunci tun da ga Baban ta can a waje a wajen inuwa shi da mutane, bata ma san haka yadin jikin nasa yake ba sai da ta gani ido da ido ta gane cewar ashe dai wayar da ta ganshi a hoto a wayar Salmanu hoto ya gyara yadin. Hudu kuma Malam Nura kawai yake bi da kallo ganin gabaÉ—aya ya raja,a da kallon amarya ya manta da laifin da ya mata.

Malam Nura wani ɗan ƙaramin tari ne ya suɓuce masa, a take ya yi gyaran murya ya ce

"Amarsu ta ango, aure ya ɗauru, mun zama tsintsiya maɗauri ɗaya, na zama naki kin zama tawa buri ya cika" Wannan kalaman da ya yi su ne suka ankarar da ƙawayen nata cewar angon nata ne wannan!.

Hadiza rasa ma bakin magana ta yi ta ce

"Uhm an É—aura" Ya washe baki tamkar mai tallar makilin ya ce

"Yau sai kwanan gidan Malam Nura" Kafin ta bashi amsa mai hoton da ta tsayar ya ƙaraso wajen domin daman yana cin abinci ne, kuma da ya ji Babanta ya ce ango da abokansa sun zo shi ne ya ƙarasa ci ya taso. Yana fitowa daga gidan camerarsa a hannunsa, Malam gani mai hoto ya ce

"To ai sai mu fara abin da ya kawo mu" Ya faɗa yana jin wani daɗi, haɗe da saka hannunsa ya gyara zaman hularsa da ta ƙara kifuwa a kan tamkar ya saka hula dara. Irin hular nan da ba a mata kari.

Abokai haka suka shiga yi wa Hadiza Allah sanya alkairi, tana amsawa kamar an mata dole!.Ƙawayen ta kuwa kowacce ta shiga danne dariyarta ganin abin da yake faruwa, sai dai ta yi alƙawarin abin da ango ya mata ba zai tashi a banza ba sai ta rama. Umarnin mai hoto suka bi wajen layuwa aka shiga yin hotuna, sai dai tun da aka yi na jam,i sai mai hoto ya ce saura amarya da ango. Amarya daman bata tsaya a kusa da ango ba da aka yi wancan hotunan, kusa da Hudu ta tsaya, duk abin da take ango yana lura da ita kuma hakan ya ɓata masa rai, da Hudu ya ga amarya ta ƙi tsayawa a kusa da ango sai ya fita daga hoto ya koma gefe .

Hadiza ta kalli inda su Baba suke ta ga hankakinsa ba ya wajen, ta É—agawa mai hoto da yake kai camera idanunsa zai walla musu hoton ta É—aga masa hannu ta ce

"Dakata!" Daga mai hoto har malam da idanu suka bi ta, ta mayar da kallon ta kan Malam ta ce

"Nura! Gaban Malam Nura ne ya faɗi amma ya yi kokarin dakewa ya zuba mata idanu ba tare da ya amsa ba, tana zaro idanu tare da kama ƙugu da hannu ɗaya tana wani karkaɗa jiki na rashin arziƙi ta ce

"Nura ni ka sincewa zani a kasuwa ko? Ni ka sakawa wannan yadi ka je wajen ɗaurin aurena! Bayan ka ɗinka shadda saboda ban isa ba, kuma matsayina bai kai a saka babbar shadda a je ɗaurin aurena ba shi ne ka saka wannan yadin mai kama da likkafani don ka zubar mini da mutunci, ka sa na yi wa ƙawayena ƙarya, ashe wannan dalilin ne ya sa kake ta ɗago hannu kamar katako a wajen kafinta, to ina so ka sani darajar babana ka ci na fito don haka yanzu ba sai an jima ba ka bani takardata" Kamar mai raɗa haka take faɗar maganar, abokai da kawaye basu san mai take faɗa ba kuma ta yi hakan ne don kar hankalin su Babanta ya dawo kansu, amma da sai kowa ya ji abin da za ta masa.

Yana kallon ta ya ce

"Hadiza aure ya É—auro, kuma ki sani tamkar auren zobe ne babu saki!." Kafin ta furta wani abu Babanta ya juyo inda yana magana da wasu mutane hakan ya sa ta kama bakinta duk da zugin da zuciyarta take mata.

Malam Nura ya sake gyara zaman hularsa ya matsa kusa da ita ya ce mai hoto ya ɗauke su, ai kuwa da sauri ta matsa ta ce sai dai a masa shi kaɗai, mai hoto ya masa, Malam Nura ya waiwaya wajen Baba ya ga hankalinsu ba ya waje yanzu, da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta tana fisgewa amma a haka aka ɗauke su tare, ƙawayenta da abokansa ganin ya kama hannunta suka shiga musu tsiya yana ɗauka ta fisge da ƙarfi ta kalli mai hoto ta ce

."Idan ka sake ka wanke wannan hoton sai ranka ya ɓaci" Malam Nura ya kalle shi ya ce

"Idan ka wanke ka kawo zan biya ka da kuɗi mai tsoka" Hadiza rai ɓace ta matsa kusa da Hudu da bai ma san ta tsaya kusa da shi ba ta ce

"Ɗaukemu da abokin ango" Kafin Malam ya juyo sai ganin hasken camera ya yi wal an ɗauki hoton, Hudu ma bai san da shi za a ɗauka ba sai bayan an ɗauka, ta yi haka ne domin ta turawa malam Nura haushi, ai kuwa ya shaƙa domin kawai ransa ne ya ɓaci, ƙololuwar ɓaci daman ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, wato dai saboda bashi da kaya mai kyau shi ya sa ta yi hoto da Hudu saboda kayansa masu kyau ne.
Chapter 17 · 0% Book details