Sashe 22
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na ga alama idan ina biya ki hawan ruwa sai ya kama ni, ai ni da wuya ta karni ai gwara daɗi ya karni, ai abin alfahri ne ma a ce miji ya nakastaka a kan kishin sa soyayya kenan, kuma ni ina nan ko sama da ƙasa za ta haɗe yau kwanane idan amarya ta isa ta yi kwanan turaka yau Allah tsine mini don wallahi ko a ni ko a ita domin sai ta jira na famshe gabaɗaya kwanankin da Malam ya haramta mini shiga turaka, sannan zan bata dama ta yi kwana ukun da kowacce bazawara take yi" Baki sake Haule take kallon Kuluwa tana mamakin ƙarfin hali irin nata, ta san yau ko gawa za ta yi Malam ba zai bari ta kwana a turaka ba!. In ban da ma rashin zuciya mutumin da ya haramta mata shiga turaka kusan kwana shida yau, shi ne zai bari ta shigar masa turaka a ranar da yake jin sa zai ɓarji amarci da amaryar da ya gama yi wa tanadi a cewarsa.
Fatan samun sa,a ta yi wa Kuluwar ta ja su Kabiru suka tafi. Suna fita Kuluwa ta rufe nata ɗakin ta tafi gidan mai maganin mata magunguna ta lodo ta biya kuɗin ta dawo gida. Tana zuwa ta kai ruwa banɗaki ta salsala wankanta, ɗaki ta dawo ta shafa wani turare mai suna MU JONE turare ne na jan hankalin mai gida da ta siyo an faɗa mata yana da kyau kuma matukar miji ya shaƙi ƙamshin shikenan sai yadda hali ya yi shiga motar mahaukaci!. Wando da riga ta saka domin mai maganin ta ce ta saka kaya na jan hankali, dan haka wani wandon Malam Nura da yake ajiye a ɗakin ta ta ɗauka ta saka sannan ta saka rigarta tshirt kasancewar bata da wanduna.Magani mai suna maƙale mata ta ɗauka ta zuba a nono ta dama ta shanye ta shafa humra.
Wani kwalli idonka idona shi ma duk yana cikin kayan da ta siyo ta É—auka ta rambaÉ—a a idanunta. Kanta da yake a tsefe ta shiga tajewa.
A can kuwa su Malam Nura masallacin magriba suka wuce, bayan an yi sallah ya musu sallama duk ransa babu daÉ—i domin har ya hango zai kwashi amarci amma gashi an samu akasin lissafi. Hudu cikinsa har ciwo ya yi wajen tsokanar Malam Nura yana faÉ—in
"Wai da gaske abokina duka ka shanye maganin nan kaɗan ka rage, gashi kuma mai maganin ya ce a ranar maganin yake barin amfani, to Allah ya sa ma kai ba gwauro ba ne, ga Haule nan ga kuma amarya Kuluwa sai wacce ka zaɓa" Ko amsa bai bashi ba saboda takaici.
Shago ya wuce yana zuwa ya ce mai shagon ya bashi sufagilu guda huÉ—u, haka aka É—akko masa ya bashi kuÉ—in ya saka a aljihu ya nufi gida.
Kuluwa da ta gama shiryawa tsaf sai kuma ta ce
"Ni da zan je turaka yau, gashi na gama haɗa bom wato na sha kayan gyara, gwara dai in shiga banɗaki in tsugunna don na ji taushen da ta sha ya saka mini ciki" Ta faɗa tana ɗaukan buta ta shige banɗaki ta rufo, a ranta tana ta saƙa yadda idonka idona kwallin da ta saka zai ruɗi Malam, da MU JONE da sauran abubuwan da ta yi amfani zai sanya idan har ta je turaka amarya za ta ƙufula ta ce an wulaƙantata a ranar amarci, in ya so da safe a yi badaƙala a sake ta shikenan ƙurunƙus.
Malam Nura a hanya suka haÉ—u da Haule da za ta je gidan nasu, take faÉ—a masa sai Kuluwa kaÉ—ai a gidan ita ma ba yanzu za ta dawo. Da sanÉ—a ya shigo zaure gidan, yana zuwa ya cire takalmansa ya shigo saÉ—af-saÉ—af motsin da ya ji a banÉ—aki ya tabbatar Kuluwa tana banÉ—aki bokiti ya É—auka ya koma zaure da sauri.
Yana zuwa zauren ya fito da gabaɗaya sufagilu yana buɗewa yna tatsewa a cikin bokitin wato can ƙasan bokitin amma daga cikin bokitin ba wai daga waje ba. Sai da ya gama tatsewa duka ya saka wani ƙaramin icce ya gyara shi ko ina.
Kuluwa wacce fitowarta kenan daga banɗaki ta cika ruwa a buta za ta yi alwala, tana ƴar waƙarta. Alwala ta zauna a kan ɗan dutsi tana yi amma ta ba ƙofar gida baya. Da ta zo shafar kai ta cire hularta ta ɗora a cinya daman kan a taje yake bata ɗaure ba. Malam Nura ya taso da sanɗa yana zuwa ya kifa mata bokitin nan a kanta, a take kan ya shige cikin bokitin, ya saka hannu biyu ya danna saman kan ta cikin bokitin a take sufagilu da bokiti suka ce sun ga wurin zama a kan Kuluwa, domin babu ɓata lokacin gashin nan ya yi nutso a sufagilu.
Kuluwa da bata ankara ba ta ji wani abu kamar roba a kanta, kafin ta ankara ta ga ya rufe mata har fuskarta, tana shirin yin magana ta ji an buga abun, abu na farko da ya fara zuwa ranta shi ne aljannu, don ta san dai gidan babu kowa, kuma daman wataran Haule tana cewa idan ta fito fitsari cikin dare tana ganin kamar gilmawar mutum, amma saboda ƙi faɗi irin na Kuluwa da ƙaryata mutum sai tw ce ita bata taɓa gani ba don haka ba za ta yar da ba. Baki yana rawa ta ce
"Subhanallahi waye, mene ne haka, mai na yi muku? Ni ce fa Hauwa Kulu, da aka fi sani da Kuluwa don girman Allah ku yi haƙuri" Ta faɗa jikin ta yana karkarwa idan akwai abin da take tsoro shi ne aljannu. Shiru ta ji hakan ya sa ta saka hannu biyu domin ta cire abun ta cece ranta tun da bata gani bokitin ya rufe mata ido, am a tana ja ta ji gabaɗaya a manne yake da gashin ta, gabanta ne ya faɗi ta tabbatar da wannan aikin aljani ne. A take ta shiga lalume kwaraf ta buge butar alwalar ta, butar ta tuntsura ruwan ya zube, kasancewar wajen alwala ne duk a jiƙe yake kuma har ya yi laka a wajen irin tsantsin nan da ƙasa take idan ruwa yana jiƙa wuri. Da hannu biyu ta dafa ƙasa ta miƙe tana ta salatin da bata iya ƙarasawa take dawowa farko, a zuciyarta tana jin daman ta raka Haule dubiyar babanta. Malam Nura ransa fari rass cike da mugunta yana tuno irin ɗiban albarka da ta yi wa wandon sa ya kai wani ɗan icce ya ɗan soka mata a jikin hannunta, a take Kuluwa ta tabbatar da cewa ta faɗa hannun aljannu domin zaton ta farcen aljani ne aka caka mata a hannun.
Salati take yi kafin ta ƙarasa sai ta kamo hailala, bata gama hailalar take kamo a,uziyya, a haka ta samu nasarar miƙewa tsaye tana baza hannu kamar makauniya ƙafafun ta ta yi wa masauki a wajen santsin lakar nan, a take santsin ya kwashe ta suuuuuu ƙafarta da babu takalmi ta tafi, domin gabaɗaya ta sille takalman wani ya yo kudancin Nigeri,a wani arewacin Nigeri,a ya nufa. Ji ta yi kamar an yi sama da ita sai gata ta faɗi jirif, duk da ta ji faɗuwar amma yanzu ba wai ta faɗuwar take yi ba batun ceton rai ake daga hannun mutanen da su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba. Da sauri ta tashi ta muskuta ta shiga rarrafe domin ta san matuƙar ta sake tashi to faɗuwa za ta yi tun da ba gani take yi ba bare ta taka inda babu laka.
Wata zuciyar tana bata shawarar ta kama hanyar waje a nan ne za ta samu a rabata da abin da aljannu suka kifa mata ya manne mata a gashi, wata kuma tana faɗa mata ta koma ta shige ɗaki ta kulle duk da ta san aljannu har bango suna shiga. A zaton ta ko Haule ko ƴan kawo amarya sa kawo mata ɗauki. Tana sunkuye tana rarrafawa Malam Nura ya lallaɓa ya naɗe hannun rigarsa ya jimƙe ya sakar mata ƙulli a baya saboda bokitin iyakarsa wuya da kafaɗarta. Jin saukar ƙulli rididif har sau biyu ta ji dukan da bambanci da na mutane a take faɗuwar gabanta ta yawaita Malam kuma a zuciyarsa ya ce
',Yadda kika salwantar mini da daren amarcina da Hadiza, da yadda na yi asarar maganin da na ɗaɗɗaka yau, wallahi sai na baki wuju-wuju sai kin gwammace kiɗa da karatu, har da wani saka wandona ke kika san jarabar da kika taka, amma yau yadda zan tsurar da ke sai kin ji daman ƙafafun na guntule miki don har suma sai kin yi Kuluwa, za ki san ni kika yi wa rashin mutunci, kika barni ina yawo da wando kwambileshin (Combination)"
Muryarsa ya shaƙe ta zama kamar ta yara kamar ta tsoho ya ce
"Kuluwaaaaaa" Kuluwa da daman a tsorace take ga kuma bokitin da ya rufe mata kunne wani irin sauti ta ji da wata murya a take a tsure gudawar da take matsewa ta fara ƙoƙarin fitowa!!!.
*Saura page 1 mu gama free pages daman na ce muku a 10 za mu gama masu son karantawa har ƙarshe za su biya 700 domin shiga group ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222, *mutanena na Niger ga*
*naku acc É—in da za ku saka 88630104 nita ko* *amana*
*Issaka issoufou.*
MAMAN AFRAH
09025576222
[4/17, 12:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿ï¸1ï¸âƒ£0ï¸âƒ£