← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 27

Sashe 18

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani haushin Kuluwa ne ya tokare masa maƙoshi, idan ya tuna cewar duk ita ce silar faruwar komai. Ta kalli Malam Nura ta taɓe baki ta cewa mai hoton ka wanke hotunan duka amma banda wanda ka mana ni da ango!" Tana faɗar hakan ta juya za ta shige cikin gidan, daman ƙawayen ta sun shige, suna son su ware kafin ta shiga gidan su yi gulmar kayan jikin mijin, tana dab da shigewa gidan ya ce

"Hadiza ki jira fitowata da yamma sai kin kasa gane ni, ya maganar jere na ga baku kai kayan ba kin san dai yau za ki tare ko?" Yana faɗar hakan ko amsa masa bata yi ba ta ja ƙaramin tsaki ta shige gida, Hudu da sauran abokan suka fara takawa ana ta hira, Zainaba wacce take laɓe a wani waje ta fito, lokacin Malam Nura yana ƙoƙarin barin wajen tana zuwa ta ce

"Ango bai sha ƙamshi ba, ango da kaya marar kyau, wallahi babana ya fika iya kwalliya gwara ma Innata ta koma gidansa" Tana faɗar hakan ta zuga da gudu cikin gidan, Malam Nura ya shaƙa, musamman da ya ga Zainaba sanye da shaddar da shi ya saya, amma shi ya ƙare a tsohon kaya.

Su Hudu da suke tafiya suna hira ana dariya, fuuuuu suka ga Malam Nura ya zo ya wuce su, suna masa magana bai amsa ba, sai sauri yake kamar ya ci ƙafar kare. Haka suke tafiya yana gabansu suna bin sa a baya amma da tazara a tsakaninsu. Ko sallama bai yi wa su Hudu ba ya shige cikin gidan, makaɗan da suke ta kiɗa a ƙofar gidan ma bai bi ta kansu ba, Hudu ne suna zuwa ya sallame su, suka tafi shi ma gidansa ya wuce don lokacin rana ta yi kuma ya san abokinsa da maƙo babu abin da aka girka na auren. Don su ma abokan tafiya suka yi.

Ko sallama bai yi ba ya shiga gidan kamar an koro shi, fuskarsa sam-sam babu fara,a, hayaniyar matan maƙota da suke ta magana ce ta masa dirar mikiya, yana shigowa gidan cike da mata suna cin tuwon masara da miyar ɗanyar kuɓewa sai hira ake yi, daman Haule ce ta yi don saboda da mutane masu shigowa.

Ana ta gaishe da shi babu wanda ya kula, domin su ne da suka zo suka dakatar da shi daga ɗaukan mummunan mataki a kan Kuluwa. Kuluwa ya gani zaune a ƙofar ɗaki ita da su Mariya sun saka tiren funkaso da taushen da suka kawo mata, sai ci suka suna hira, daman bayan fitar Malam ta yi wanka ta saka kaya ta cokara ɗaurin ture ka ga tsiya, don yanzu ransa ya mata ɗan sanyi saboda ta ƙona shaddar ɗaurin aure. Yana shigowa kallo ɗaya ta masa dariya ta taho mata, hannu ta sanya ta toshe bakinta da yake cike da funkason da ta saka, fuuuuu ya zo ya wuce hula a hannu, don har lokacin yana hango kallon tsanar da Hadiza take masa a matsayinsa na sabon mijinta angon ta.

Yana dab da shiga É—aki, Haule wacce ta fito daga É—akin ta ta hango shi ta kwashi guÉ—a, amma tsabar takaici ko waiwayowa bai yi ba, yana jin matan suna cewa ango ango amma babu wanda ya amsawa yanzu hankalinsa yana kan yadda zai birge Hadiza ya kankarowa kansa guntun mutunci a wajenta da kawayenta ma da ya ga suna masa kallon É—aya saura kwata.

Yana shiga ɗakinsa da wandon shaddar nan da Kuluwa ta ƙona ya yi tozali, ransa ya ƙara ɓaci yana tuno ranar da ya karɓo a wajan ɗinki amma yanzu ya zama gajere, gajeran ma iya cinya. Hular ya cillar a kan katifarsa. Yana rayawa a ransa cewar yau komin dare sai Kuluwa ta girbe shukar da ta yi domin ba za ta ci bulus ba. Rigar shaddar ya ɗauka, ya saka a leda, ya ɗauki gajeran wandon ya saka a ledar, wani tsohon wandonsa ya ɗauka na yadi ya saka a ciki, ya ɗakko kuɗi ya fito, fuuuuuuu yana tafiya kamar zai ci da ka, yana dab da shiga zauren Kuluwa da muryar dariya ta ce

"Ango ka sha ƙamshi" Ta faɗa cike da sheƙiyanci, domin a tunanin ta fasa auren ma aka yi tun da ta ga sai muzurai yake yi.

Tun da ya fito yake sauri, burinsa É—aya ya ganshi a shagon É—inki, yana zuwa ya samu mai É—inki ya ce

"Ibra wajenka na zo"

Ibra da yake saka maɓalli a wata riga ya ce

"Ango ango, ango ka sha ƙamshi, a mini afuwa ban samu zuwa ɗaurin aure ba, ina ta ɗinkin muta... Malam Nura ne ya katse shi da faɗin

"Aure dai an É—aura!" Sai ka bari ma haÉ—u a wani É—aurin auren" Dariya sosai Ibra ya saki ya ce

"Haka ne fa mutumina, kai ai baka wata uku cikakke ba ka yi sabon aure ba!" Malam Nura bai bashi amsa ba, domin yanzu hankalinsa ya karkata ga yadda za a yi masa wandon nan ya saka kayan da yamma ya je wajen Hadiza ko ta huce ya lura in bai yi kyan nan da take naci ba, wataƙila a samu matsala, shi ya ga ko tsinke ba a kawo gidan ba, kuma ya gama sakawa a ransa yau amarya za ta tare amma kuma ya ga babu niyya wai ango ya kwana da wando.

Cike da jimantawa ya fito da kayan daga leda yana faÉ—in

"Ka ga dai ɗinkin da ka mini, duba ka ga yadda Kuluwa ta mayar da wandon nan, don abin kunya da mazaunai suka mutu suka bar zani wai da wannan yadin na je ɗaurin aure!" Salati Ibra ya ɗauka yana riƙe da haɓa cike da zuga ya ce

"Wannan shaddar mai tsada da kyau, shaddar da shugaban ƙasa yake saka irin ta, amma saboda kishin banza ta ƙona, amma dai ka hukunta ta ko?" Baki Malam ya dantse yana cewa

"Barni da ita, wallahi ƙafafu na so datse mata kawai dai lokacin cirewar ƙafafun ne bai yi ba amma dai na san zan cire mata ƙafafu ta koma tuƙa keken guragu" Ya faɗa yana cika yana batsewa.

Ibra ya ce

"Yanzu ya za a yi da wannan?" Malam Nura ya ce

"Faci za ka yi"

Da mamaki yake kallonsa ya ce

"Haba Malam Nura wane irin faci kuma, ai wannan ka haƙura da shi kawai, amma faci sai ka ce wata tayar keke"

Malam Nura kamar zai kai masa duka ya ce

"Ibra idan ba za ka yi ba ka faÉ—a mini na kai wani shagon, an ce maka sai keke ake yi wa faci"

Ibra ya ce
.

"Ina jinka yi min bayani"
,

Malam Nura ya ce

"Wannan wandon yadin nawa za ka datse shi daga gwiwa zuwa ƙasa, sai ka yanke ƙasan rigar shaddar ka haɗa ƙyallan da ka ciro a jikin riga, da wandon nan ƙonanne da wannan guntun ƙonannan wandon ka yanka mini ƙafar wandon zuwa gwiwa, idan ka yanka sai ka ɗora a kan wannan wandon yadin da ka yanke, sai ka ɗinka mini, ka ga idan na saka babu wanda zai ga saman tun da rigar ta rufe, iya ƙafafun ne za a hango, so nake in yi wankan kece raini na fita kunya da yamma, yadda zan gigitawa Hadiza tunani, don na ji hatta ƴarta Zainabar wannan da ba sona take ba tana cewa wai babanta ya fini iya wanka da gayu, gwara na nuna musu nima Kuluwa ce ta mini tsiya shi ya sa suka ganni da tsohon kaya!"

MAMAN AFRAH
09025576222
[4/15, 3:33 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA*

NA

MAMAN AFRAH

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222

🅿️9️⃣

Tun da Malam Nura ya fara bayanin facin wando Ibra yake ta dariya, har ya gama faÉ—a masa amma bai tsagaita dariyar ba sai da abin ya ishi Malam Nura ya kalli Ibra cike da takaici ya ce

"Dalla Malam ba kyauta za ka yi ba kuÉ—inka zan cake na baka" Dariyar ta tsagaita ya ce

"Zan yi maka mana ai ka san ni da kai bata ɓaci, kawai dai lamarin ne ya bani dariya, yanzu duk kuɗinka abin ka sake ɗinka sabuwa ka zauna kana ta wannan lissafin, ka yarda mace ta maka aika-aika har burinta yake neman cika" Malam ya ce

"Burin Kuluwa in tozarta ni kuma ba zan tozarta ba kuma sai na yi bikin nan yadda ba ta so, kai dai ka yi ƙoƙarin fito mini da shaddar nan kawai" Amsa masa ya yi ya ajiye aikin da yake ya shiga yi masa nasan kamar yadda ya buƙata. Malam yana zaune a gefe aka yanki ƙasan rigarsa aka yi ƙasan wandon aka yanke ƙasan wandon yadin aka jona na shaddar. Bakin Malam Nura har kunne ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu yana kallon Ibra cike da girmamawa ya ce

"Ba gashi ba, ai wallahi da na san za a iya yin wannan dabarar da ko wajen ɗaurin auren ba zan je a haka ba" Ya faɗa yana karɓar wandon ya kara a jikinsa ganin ya masa yadda yake so ya biya Ibra kuɗin gyara har da ƙari. Ibra yana ta tsokanarsa ya ɗauki ledarsa ya nufi gida, lokacin gar an fara kiran sallar la,asar, Hadiza kuwa ya kira ta ya fi sau goma amma bata ɗauka ba, da ya gaji sai ya ƙyale ta. Babu abin da ya saka a cikinsa wuni guda, haka ya wuni a shagon ana masa gyaran sai da ya ga ya kammala sallah ce kawai take fito da shi daga shagon, ko da suka haɗu da Hudu a masallaci ma ya sanar da shi cewa yana can ana masa ƴan dabaru dariya ya masa saboda ya san kawai wandon nan ba zai saku ba.
Chapter 18 · 0% Book details