← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga ɗakin ta fara tunanin makomar ta a gidan Malam Nura, domin sai yanzu ne zuciyarta ta shiga zulumi da abin da ta aikata na ƙona masa wandon amarci!. Duk da ta san shigowarta ɗakin ba mafita ba ce amma dai ya zama wajibi ta tanadi wani abu da za ta tsira, tun kafin ya fito ya mata tijara.

A can cikin banɗaki kuwa Malam Nura sai da ya saɓa jikinsa sau takwas, yana wankan yana ta ƙiyasta irin kyan da zai yi yau, ya san lallai zai tashi kan mutanen ƙauyen Shabaru, duk da ya gama tsara nawa zai siyar da shaddar idan an kammala biji, don hatta kuɗin ɗinki sai ya fitar har da riba zai ɗora!.

Yana gama wanka ya mayar da riga ya fara shirin buɗe ƙofar banɗakin. Kuluwa tana ta tunanin abin da za ta aikata, wata dabara ce ta faɗo mata a rai, da sauri ta leƙo tsakar gidan daga jikin wata ƴar tula da take jikin ƙofar ɗakin, Haule ta hango tana duba ƙaramin mudubi a hannunta ta nufi ɗaki.

Da sauri ta zare sakatar ɗakin ta da ta saka, ta ɗan buɗe ƙofae kaɗan yadda ba za a ce rufewa ta yi ba, baki Kuluwa ta buɗe da ƙarfi ta shiga yin jiniya irin wacce ake yi wa sarki ko gwamna da sauransu. Malam Nura yana shirin fitowa sautin jiniya ya sauka a kunnuwansa, ɗif ya yi ya saurara don gabaɗaya ya rasa ta ce a zuciyarsa ya ce

'Ikon Allah, lallai wannan ɗaurin auren nawa zai tara mutane, to ko dai a dangin su Hadiza suna da alaƙa da sarauta ne, Allah ya taimakeni da na cire son kuɗi na yi ɗinkin na kirki, da kunyata zan yi, lallai yau akwai shagali' Ya faɗa baki washe yana buɗe ƙofar ya fito. Sai da ya fito tsakar gidan ya ji sautin jiniyar kamar ma ya ƙaru tamkar a cikin gidan ake yi.

Haule da ta shiga É—aki ta jiyo ana

"Wooooo,waw,waw,waw,waw, waw" Dakatawa ta yi daba ajiye madubin ta saurara, amma sai ta ji ƙaran kamar daj da baki ake yi hakan ya sa ta ɗaura yara ne suke wasa.

Fitowarta ya sa ta ji ƙaran a ɗakin Kuluwa yake fitowa, mamaki al,ajabi ne suka mata dirar mikiya, hakan ya sa ta nufi ɗakin da ɗan sauri, domin sautin ya banbanta da muryar yara, tana leƙawa ta hangi Kuluwa tana ɗan zagaya ɗaki tana jiniya idanunta a rufe, gaban Haule ne ya faɗi domin tana ganin hakan ta san ba lafiya ba, salati ta kwasa lokacin Malam ya ƙaraso yana sauri domin lokaci ya ƙure.

Saurarawa ya yi ya ji ƙaran jiniyar daga ɗakin Kuluwar sannan ya tabbatar da baki ake yi. Haule cike da tashin hankali ta ce

"Innalillahi Malam akwai matsala zo ka ga abin da Kuluwa take yi" ,Wani kallo ya mata cikin halin ko in kula ya ce

"To daɗi ne ya mata yawa shi ya sa take jiniya wataƙila ta tuno da lokacin yarinta ne"

Cike da damuwa ta ce

"Ba lafiya ba fa, leƙa ka ga abin da take yi" Tsaki ya doka ya ce

"Kina jin dai yadda dandazon mutane suke jirana a waje da makaÉ—a, yau fa za a É—aura aurena da Hadiza kuma a yanzu, ni har ina da wani lokaci ne bayan na É—aurin aurena"

Yana faɗar hakan ya nufi ɗaki da sauri har yana neman faɗuwa, a kiɗime ta tura ƙofar ta shiga a take Kuluwa ta ƙara ƙaimi wajen jiniyar tun da duk tana jin abin da ake yi ta san yanzu zai je ya ga wandonsa amma tun da dai ita ta nuna babu lafiya a tare da ita babu mai tuhumar ta.

Ganin halin da take ciki Kuluwa ta fito da sauri tana faÉ—in

"Malam jikin na nata fa kamar tsamari yake, wallahi kamar fa aljannu ne... Yana dab da shiga É—akin ya juyo tun kan ta dire maganar ta ya ce

"Haule ya kamata ki san wanda ya yi nisa ba ya jin kira, yanzu duk abin da za a faÉ—a ba ganewa zan yi ba wallahi, gabaÉ—aya hankalina ya karkata ga É—aurin zuren nan, kuma ba kallon aljannu ba ko kukar bulukiya ce ta bayyana a jikin Kuluwa ba zan fasa tafiya ba" Yana kaiwa nan ya bankaÉ—a labulen É—akinsa ya shige ya barta a tsaye da sauri ta juya zuwa É—akin Kuluwar.

Yana shiga ya samu wayarsa tana ƙara alamar ana kiransa, kafin ya ɗauka ta katse nan ya hangi miss call rututu yana dubawa ya ga sunan Hudu da Hadiza su biyu da ransu suka tara masa wannan uban kiran. Yana shirin kiran ɗaya daga cikinsu kiran Hudu ya shigo ya ɗauka Hudu ya ce

"Haba Nura ya za a yi ka bar mutane tsaye ana jiranka, ka san kowa kai yake jira a tafi wajen É—aurin auren nan, ga makaÉ—a ka bari suna ta faman kiÉ—a kuma ka san dai duk kiÉ—an nan da suke a kuÉ—i yake, daga wanka kamar wanda kake canja fata" Ya faÉ—a a faÉ—a ce.

Malam Nura ya sheƙe da dariya ya ce

"Wallahi ina can ina ta sheƙe wanka, gani nan fitowa" Maimakon ya bashi amsa ya ce

"Wai ihun jiniyar me nake jiyowa ne?" Hudub ya tambaya, Malam Nura ya doka tsaki ya ce..

"Kuluwa ce da neman jafa,i ta tada aljannu bata san ba ni ko bataliyar aljannun ne za su sauka a gidan nan sai na tafi ɗaurin auren nan" Shiru ya yi kafin ya ce wani abu Malam Nura ya kashe wayar domin ya ga ana ɓata masa lokaci, yana shirin ɗora wayar a kan katifar kiran Hadiza ya shigo,.ɗauka ya yi cike da rawar jiki ya ce

"Amarya bakya laifi, amarya mai magana suga... Kafin ya ƙarasa a gadarance ta ce

"Wai ina kuka tsaya ne gabaÉ—aya dangin amarya sun hallara babu dangin ango, ana jiranku, kamar za ku zo daga waji gari?"

Cike da farincikin jin muryarta ya ce

"Allah ja zamaninki ranki shi daÉ—e, gamu nan zuwa"

Shiru ta É—an yj ta ce

"Gani nan na sha kwalliya da shaddata, ana gama É—aurin aure nan za ka zo a mana hoto, ina son ganinmu da shadda iri É—aya" Ya washe baki kamar ta masa busharar da kujerar makka ya ce

"Ai ina nan ki jirayi fitowata nima, dan ba bari zan yi ki fini kyau ba atoh" Ya faÉ—a cike da wasa, dariya sosai ta yi ta ce

"To sai kun ƙaraso" Ya amsa mata. Har zai kashe ta ce

"Ai na bango za a mana hoton na rataye a É—akina" Ya yi karaf ya ce

"Ni guda huÉ—u xa a mini naki ke kaÉ—ai guda uku na jera su, sai namu wanda za a mana tare in kafe a bango" Tana Æ´ar dariya ta ce

"Ai ina so in ganmu da kaya iri É—aya"

Ya ce

"Yau kwa za ki gani" Har za su yi sallama ta ce

Wai ƙaran mene ne nake ji?" Da kamar ba zai faɗa mata ba don ya ga tana cinye mishi lokacin gashi ana jiransa, amma da yake so ya rufe masa ido ya ce

"Kuluwa ce zazzaɓin kishi ya kama ta, take jiniya kamar wata motar ƴan sanda" Baki ta taɓe ta ce

"Ta jirayi zuwana" Dariya ya yi suka yi sallama yana ta mamakin ta domin ya san ta da zafin kai bai sani ba ko don ranar ɗaurin auren ne shi ya sa take lallaɓa shi ko kuwa wani abu ne ita dai ta sani domin shi dai ya san ruwa ba ya tsami banza.

Turare ya ɗauka ya shafa a jikinsa, ya ɗakko mai zai shafa ya lakuto kenan wayarsa ta sake ƙara, ganin sunan Hadiza ya ɗauka cike da masifa ta ce

"Wallahi idan ka ƙara wasu daƙiƙai baka zo ba da wani za a ɗaura mini aure, ka san zan aikata ko?" Tana faɗa ƙit ta kashe wayar har lokacin yana iya jiyo jiniyar Kuluwa.

Wannan man na hannunsa da ya lakuto ko murzawa bai yi ba tsabar kiɗimewa, bai san ya lakuta man a tsakiyar hancinsa ba. Da sauri ya ɗaga rigar ya ɓalle maɓallin ya saka da sauri, don gabaɗaya Hadiza ta faɗar masa da gaba, domin a maganar ta babu wasa kuma ya san matuƙar aka ɗaura auren ba za ta biya shi kaf kuɗaɗensa ba.

Yana saka rigar ya ɗauki wandon amma saboda hankalinsa ba a jikinsa yake ba haka ya zura ƙafafunsa ya ji kowacce ta wuce ya ja mazugin ya ƙulle ba tare da ya lura da abin da yake faruwa da wandon nasa ba. Maɓallin rigar ya ɓalle ya ɗauki hula ya saka, turaren ma bai fesa a kayan ba ya ɗakko wayarsa ya fito a sukwane.

Kusan karo suka yi da Haule da ta taho sanar da shi cewa ko malami za a nemo ya yi wa Kuluwa ruƙiyya. Ganinsa yana sauri ta ce

"Malam na faÉ—a maka halin da Kuluwa take ciki" Malam Nura yana zare ido cike da masifa ya ce

"Haule ki ƙyaleni, don a halin da ake ciki yanzu ko gawa ce a ajiye sai dai a jira idan na dawo daga ɗaurin aure a yi jana,izar" Baki sake take kallonsa don ya bata mamaki ta rasa wane irin so yake yi wa wannan auren, ita dai duk aure-aurensa bai taɓa ɗora rai a kan aure kamar wannan ba.

Sai lokacin ma ta lura da wani lafcecen mai a saman hancinsa ta ce

"Malam ka ga fuskar ka kuwa mai ne lafke a wuri guda ko shafawa baka yi ba, kuma fuskar gata nan firi-firi babu mai" Bai jira cewarta ba ya saka hannu ɗaya ya murje fuskar, kasancewar man da ɗan dama sai ya yi wani uban maiƙo yana sheƙi kamar ya shafa man ƙuli.

Takalminsa ya saka ya fara tafiya, gaban Haule ne ya faɗi ganin ƙafafun Malam Nura a waje, duk da halin damuwar da take ciki na jinyar Kuluwa don gabaɗaya ma muryar Kuluwa ta shaƙe saboda jiniyar da take yi amma hakan bai hana dariya ƙwacewa Haule ba, don a tunaninta tsabar sauri ne ya sa Malam ya manta bai saka wandon shaddar ba.
Chapter 10 · 0% Book details