← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta É—an dakatar da dariyarta marar sauti lokacin har ya kusa da zaure ta É—aga murya ta ce

"Malam...Tun kan ta kai aya ya É—ago mata hannu ko juyowa bai yi ba, alamar ba zai samu damar tsayawa ba, cike da É—aga murya ta ce

"Duk saurin ne ya sa ka manta baka saka wandon shaddar ba?" Jin tambayar ya yi kamar ta rainin hankali shi gabaɗaya hankalinsa yana kan ɗaurin auren da Hadiza ta ce za ta fasa da shi idan bai yi sauri ba, ga wayarsa da Hudu yake kira. Kamar ba zai duba ba tun da dai ya san ya saka wandonsa, amma sai ya kalli ƙafar abin mamaki babu alamar wandon, da sauri ya janye rigar daga gaba, ƙwabrinsa ya gani zangar -zangar a waje, gabansa ne ya faɗi, domin abin da ya fara zuwa ƙwaƙwalwarsa shi ne aljannu ne suke son raba tsakaninsa da Hadiza in ba haka ba shi da ya san ya saka wandon ya za a yi ya ga babu.

A kiÉ—ime ya É—age rigar har saman gwiwarsa amma sai fatar jikinsa yake gani bai ga shaddar ba. Haule tana dariya ta ce

"Ka koma ka sako" Shi dai har lokacin yana cikin ruɗani, jin furucin ta ya yi saurin ɗage rigar gabaɗaya, gajeran wandonsa na shadda iya cinya ya bayyana ƙasan da alamar ƙonewa. Idanunsa ya zazzaro tamkar za su faɗo ƙasa, ya lailayo wani uban ashar mai maiƙo ya fara narkawa yana faɗin

"Uban waye ya ƙona wandon shaddar nan?" Kuluwa wacce muryarta ta fara dishewa saboda jiniya, ta jiyo sautin maganarsa, gabanta ne ya bada sautin rass domin ta san mai rabata da Malam Nura yau sai Allah matsawar ya gano gaskiya.

Haule salati ta hau yi tana kallon yadda aka yi wa wandon ƙunar wulakanci kamar ma ƙafa ɗaya ta fi ɗaya. Ba komai ne ya zo ƙwaƙwalwarsa ba sai tunowa da ya yi cewar kayan siyar da su zai yi idan aka gama sabgar biki, sannan ya tuno wayar da suka yi ɗazu da Hadiza a kan za a musu hoto a tare da shaddar nan iri ɗaya, hankalinsa bai kai ƙololuwar tashi ba, sai da ya tuna cewar ana can wajen ɗaurin aure ana jiransa, kuma kaf kayansa banu wani mai abin arziƙin da zai iya shiga taro, taron ma na ɗaurin aurensa!.

Tunowa da magaar Hadiza na cewar idan ya ƙara daƙiƙu bai je ba za a ɗaura mata aure da wani, shi ne lamarin da ya saka shi cikin firgici. Haule da take kallonsa cike da mamaki ta rasa ma wane tunani za ta yi. Kamar wanda aka cakawa mashi ko kibiya hular ya wurgar wayarsa ma a wajen ya sake ta, Haule ta fara tunanin ko dai aljannu ne suka sauka a gidan ko kuma jifa ne aka yi wa Kuluwa da Malam ɗin, domin yanayinsa ya nuna ba a hayyacinsa yake ba, hankalin ta a tashe ta fara masa kallon ko dai hauka ya fara.

Malam Nura kuwa, zuciyarsa ta gama faÉ—a masa wanda ya masa wannan aika-aikan, sannan a take ya gama gane dalilin jiniyar Kuluwa kenan.

Haule sai ganin Malam ta yi ya falfala da gudu takalman nasa kowanne ya kama gabansa, saboda yana fara gudu ya cire su, Kuluwa kuwa gabanta yana faɗuwa tana jin tamkar ta fito da gudu ta bar gidan, amma tunowa da ta yi idan ta tafi za a kawo amarya bata nan sai ta fasa, don daman ƙannenta ma sun ce za su zo yau ɗin.

Jin ƙaran gudun Malam ta yi saurin sauya akalar jiniyar tata zuwa carar zakara. Haule da take tsaye tana jin kamar na fita waje neman taimako, amma tana tsoron tijarar Malam jin Kuluwa ta daina jiniya ta tsiri carar zakara sai lamarin ya sake cunkushe mata.

Ganin ya je tsakiyar gidan ya tsaya yan waige-waige, idanunsa suka sauka a inda aka ƙona wandon, yana dubawa ya ga sawun takalmin Kuluwa zarginsa ya zama gaskiya daman ya san babu mai wannan ɗanyen aikin sai ita, gaban Haule ya shiga faɗuwa, domin gabaɗaya gumi ya wake masa fuska ga sheƙin man fuskarsa ga tsantsar tashin hankali da ya bayyana, wata kaza da ta taho da ƴaƴanta za ta shiga ɗakin ta, ganin zai bige mata ƴaƴa ta kai masa cako, haushi ya sa ya shura ta da ƙafarsa, da gudu ta yi hanyar ɗakinta.

Dubawa yake mai zai yi wa Kuluwa ya huce duk da ya san ko mai ya mata ba zai huce ba amma dai yana so ya mata abin da za ta san ta taɓo gidan rina!.

Ɗakinsa ya juya da gudu sai gashi ya fito da adda, kiran sunansa Haule ta shiga yi tana tsoron tunkararsa don gani take kamar ya haukace, wajen murhu ya nufa inda Haule ta hura wuta, ya ɗakko wani ƙaton faskaran icce mai wuta a jiki, kafin ta ƙifta ido ya yi wa ɗakin Kuluwa tsinke, yana kwaɗa mata gigitaccen kira.

Kuluwa ambaton sunan ta kaɗai ya isa ya sanar da ita ya gano tsiyar da ta shuka masa, bata san lokacin da carar zakaran da take ya tsaya cak ba, a sukwane ta nufi ƙofar ta saka sakata.

Mutuwar tsaye Haule ta yi jin Kuluwa tana faÉ—in

"Haule kira jama,a a waje, ki ce gida babu lafiya" Ta faɗa don ita a tunaninta madoki ya ɗakko zai mata dukan mutuwa bata ma san abin da ya ɗakko ba. Haule ta shiga ruɗu lallai wanda ya ƙona icce shi ya san yadda toka take tsada, in ba haka ba ashe dai duk abin da Kuluwa take ba aljannu ba ne iya shege ne kura a rumbu!.

Da ƙafa ya buga ƙofar ta yi wani ƙara, Kuluwa ta koma ta manne da jikin drower ta tana ciccira ido, ya dawo ta windo ya leƙa idanunsa kamar garwashi ya ce

"Wallahi wallahi karambanin akuya ya sa ta leƙe ɗakin kura, amma za ki gane shayi ruwa ne, ni kika ƙonawa shaddar kusan dubu talatin?"

Kasancewar bata hango abin da yake hannunsa sai fuskarsa, ta ce

"Ina sane wai karuwa ta taka matar aure! Ai a ganina ba raini ba ne don an ce wa karuwa hayo gado don abin da ta saba ne kuma sana,arta...

Addae da ya ɗago da faskaran icce mai wuta a jiki shi ya sa jikin taƙaura ya yi la,asar wato bakin Kuluwa ne ya rufu ruffff

Malam Nura ya ce

"Yadda kika datse ƙafafun wandon shaddar ɗaurin auren Hadiza, haka zan datse ƙafafunki da wannan addar ki koma gurguwa, sannan na saka bakin wutar nan a dungulumin ƙafar taki yadda za ki ji a jikin ki, kin maida min wando gajere na maida ki gurguwa, ramuwar gayya ai ta fi ta gayya !" Haule sai yanzu gabaɗaya ta gane inda aka saka gaba da gudu ta tsallake wayarsa da take ƙara ta yi hanyar ƙofar gidan don a kawo ɗauki.

Kuluwa ido ya raina fata a yadda yake magana rai ɓace ta san zai iya aikata komai ma, tun da ransa a ɓace yake ƙololuwa iya zamanta da shi bata taɓa ganin wannan ɓacin ran ba, kuma ta san duk a kan Hadiza ne yake wannan shi ya sa ita kuma ta riƙe ta abokiyar adawa ta har abada ba za ta daina kishi da ita ba.

Hannu biyu ta ɗora a ka tana tunanin kar fa ya ɓalle ƙofar ya aiwatar da ƙudurinsa, kafin a zo a kawo ɗauki cike da magiya ta ce

"Gida zan tafi"

Yana mata kallon tsana ya ce

"Sai dai a kai ki gida a baro, don sai na mayar da ke gurguwa!."

Ƴar uwa ban hankalinki minti biyu,,, kina son sayen kayan kicin? Ko zannuwan gado kike so? Leshi,,, shadda atamfa kayan yara,,, takalmi da jaka,,, ko kina son siyan abaya,,, mayafai huluna da sauransu ki tuntuɓeni 09025576222

MAMAN AFRAH
09025576222
[4/11, 5:14 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t

*UWAR AGOLA*

🅿️6️⃣

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*

*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*

*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*

*UWAR AGOLA*

NA

MAMAN AFRAH

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222

🅿️6️⃣

Kuluwa jin furucinsa na cewa sai dai a kai ta gida a baro domin zai gurgunta ta ne, sai ta ji gabaÉ—aya hankalin ta ya tashi musamman da ta san daga ita sai shi ne yanzu a cikin gidan Kuluwa ta fita samo masu kawo É—auki.

Cike da yaudara ce

"Na ji zan biya ka shaddar gabaɗaya... Ai furucin ta ƙara hasala shi ya yi hakan ya sa ya ajiye addar da faskaren iccen, saboda ya ga ita Kuluwa kamar ta ɗauki abin da wasa bata san irin baƙinciki da ƙunci haɗe da takaicin da ta ƙunsa masa ba, yana ajiyewa ya shiga buga ƙofar amma ta ƙi buɗuwa Kuluwa gabanta sai dukan tara tara yake tana jin tsantsar tashin hankali da fargaba domin da alama ƙaramar hauka ta samu Malam Nura. Jin ƙofar ba za ta buɗu ba ya yanke hukuncin ɓalle ƙofa, waige ya fara ya tafi a guje ya ɗakko taɓarya duk ya haɗa gumi wuyan rigarsa ya jiƙe. Yana ta saƙa da warwara a zuciyarsa domin yana tunanin idan ya gama nakasta Kuluwa wato ta mayar da ita marar ƙafa to zai haɗa mata da takardar saki, don ya hango wannan ce kawai mafita in ba haka ba idan amaryar ma ta zo babu alamar kwanciyar hankali.
Chapter 11 · 0% Book details