Sashe 24
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuluwa jin sallamar Haule ta buɗe baki kamar ƙaramar yarinya tana faɗin
"Taho Haule, taho ƴar uwata ta jini ba kishiyata ba, zo ki ga yadda na yi arangama da mutane ɓoye, wallahi na yi zaton alƙiyama ta ce ta tsaya ashe dai za ki zo ki same ni da rai" Ta faɗa tana sharɓar kuka tana miƙa hannayen daga zaunen da take ko sallamar bata amsa ba.
Haule cike da tashin hankali ta ƙarasa shigowa da ɗan gudu ta nufi inda Kuluwar take, a daidai nan Malam da yake laɓe ganin ta bashi baya ya suɗaɗe ya saka takalmansa da abubuwan sufagilu ɗin ya bar gidan. Tana zuwa ta kwashi salati ta salance ya ce
"Kuluwa aljannu kuma mun shige su, ai daman ina faÉ—a miki idan na fito fitsari da dare sai na ga kamar wulgawar mutum amma kika ce babu wasu aljannu a gidan nan,... Kafin ta rufe bakin ta Kuluwa ta ce
"Kaico! Haule, taimaka ki gani abun da suka rufa mini yadda kika san an haɗa mayen ƙarfe da jikin ƙarfe haka ya haɗu da gashina ya ƙi ɓamɓaruwa, gashin nan da na tsefe zan ke yin kwalliyar da shi idan amarya ta tare amma kin ga sun maƙala shi a wani abu" Haule da ta ƙaraso cike da rikicewa ta ce
"Kuluwa ai bokiti ne a kanki" Kuluwa ta ce
"Haba Haule wane irin bokiti dan Allah ki taimaka a san yadda za a rabani da wannan abun na kaina, ni ba na ganin komai sai duhu, zatona ma ko matatar man aljannu ce"
Haule ta ce
"Ba waji matatar man fetur ɗin aljannu wannan bokitin naki ne baƙi" Shiru ta yi rana nazarin shin daman bokitin ta ne aljannun suka ɗauka kenan suka rufa mata amma ta kasa gane dalilin da ya sa abin ba ya ɓaaruwa.
Haule ta ce
"Ni na tasa garin yaya ta faɗa tana yaɓa bokitin amma sai ta ji shi ƙamƙa a kan Kuluwa, nan ta shiga ƙoƙarin ɓanɓarewa amma abin ya ci tura!.Tun tana ja abin yana bata mamaki har ya fara vata tsoro.
Tana kallon Kuluwa cike da tausayawa ta ce
"Kuluwa bokitin nan kamar dai tare da kanki aka yi su a mannr domin ya ƙi fita fa" Kuluwa kamar za ta yi kuka ta ce
"Dan Allah ki cire mini, yanzu idan Æ´an kawo amarya suka zo sai a mini dariya fuska a rufe," ,Amsa mata ta yi na Kuluwar ta ce
"Bari in dafa ƙasa ki dage ƙarfin ki na bara ki cire mini amma kar ki bari daidai da ƙwayar gashina ɗaya ya tsige garin cirewa, kin san dai gashi shi ne adon mace" Banza Haule ta yi da ita ta shiga ƙoƙarin raba ta da bokitin amma ta ji shi gamgam idan ta ja da ƙarfi sai Kuluwa ta shiga zandama ihu tana faɗin wayyo gashin ta. Ta jima tana abu ɗaya amma ta kasa gane mene ne ya riƙe gashin daga cikin bokitin ganin abin ba na ƙare ba ne sai ta cewa Kuluwa bari ta je ta dubo Malam Nura a waje, har tana tambayar kuluwa daman bai dawo gidan ba ta ce ai ban da aljani babu wanda ya zo tun bayan fitar su, ba ta san cewa Malam ne aljanin nata ba.
Haule hanyar waje ta kama da sauri tana jin Kuluwa tana rangaÉ—a mata kira amma ta yi banza da ita, don tana faÉ—ar wai kar fa ta tafi ta bar ta aljanin ya dawo ya ida nufinsa na cire mata mashaya, wai ta kama hannun ta su tafi tun da ita ba gani take ba yanzu.
Malam yana fitowa ya watsa gidan sufagilu ɗin a kwata, ya tafi wata majalisa wajen mai siyar da biredi ya zauna suna ta tsokanarsa mai zai kawo sabon ango majalisa shi da zai tarɓi amarya nan dai ya sanar da su cewar sai gobe ne tariyar. Haule tun da ta fito take ta duba shi bata gan shi ba. Tafiya ta shiga yi tana dubawa wani saurayi ɗan maƙotansu ta tambaya ya ce ya gan shi a wajen me shayi da biredi, nan ta ce ya kira mata shi. Tana nan tsaye sai ga Malam ya taho yana ta sauri tamkar bai san mai ya faru a gidan ba yana zuwa cike da nuna damuwa ya ce
"Haule lafiya dai? Ko ƴan kawo amaryar ne suka zo?" Ya faɗa kafin ya ƙaraso, Haule ta ce
"Malam mutanen ɓoye ne suka yi wa gidanka kutse wallahi suna can sun rufewa Kuluwa kai" Idanu ya zaro kamar dai ba shi ya aikata ba ya ce
"Subhanallahi, subhanallahi mutanen ɓoye kuma? Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, wane irin rufe kai, ya subhanallah wayyo Kuluwa" Ya faɗa don ba ya ma son ya nuna cewar yana jin haushin ta a kan abin da ta masa shi ya sa ya nuna tausayawa don idan ya sake Haule da shegen wayo za ta iya hango jirginsa.
Haule ta ce
"Wallahi nake faÉ—a maka bokiti ne suka rufa mata, kuma cikin ikon Allah bokitin ya manne da jikin kanta yadda ka san tare aka halicci bokitin da kanta ko alamar fita ba ya yi"
Hannuwa ya tafa yana salallami ya nuna damuwa, a daidai na Hudu da ya zo zai je neman É—ansa da aka aika bao dawo ba ya gan su tsaye cike da zolaya ya ce
"Sabon ango mai tariya gobe" Amma ganin Haule duk a ruÉ—e sai ya ce
"Ya na ganku carko-carko lafiya dai?" ,Malam ya ce
"Ina fa lafiya kukar bulukiya a gidana" Ya faÉ—a yana kwashe abin da Haule ta faÉ—a masa ya faÉ—a masa, sosai a jimanta abin suka É—unguma zuwa gidan Haule ce a gaba kamar za ta ci da ka.
Kuluwa da take zaune inda aka barta kamar an dasa ta bakin ta yana ta faman kai da komowa na addu,ar da duk ta ci nasarar cafkowa a bakin ta jin takunsu kafin su yi sallama ta sake rikicewa tunanin ta aljanin ne sallamar su ta sanya ta sauke ajiyar zuciya. Ko amsawa ba ta yi ba ta hau faÉ—in
"A kawo ɗauki jama,a idan aka ce a haka zan rayu ni Kuluwa aljanin nn ya shiga haƙƙina" Harara Malam ya aika mata a ɓoye don har yanzu bai ji ya huce daga abin da ta masa ba.
Hudu salati yake ba ƙaƙƙautawa shi ma Malam yana taya shi gudun a zarge shi. Hudu ya kama bokitin ya ja, amma gabaɗaya a manne yake Malam ma ya ja ya ji babu alamar zai fita, hakan ya sa cike da mugunta ya ja da ƙarfi ai kuwa Kuluwa ta zandama uban inu tana faɗin
"Da ciwo waye wannan mai É—anyen aikin?" Malam ya sanyaya murya cike da nuna damuwa ya ce
"Waye kwa banda mijin ki Kuluwa ni ne nan damuwa na yi da wannan takunkumi da jinnu suka miki, Allah sa dai abin nan ba da shi za ki rayu b... Bai kai maganar ba Kuluwa cike da jin haushi ta ce
"A bakin ka wallahi, wannan ai mugun fata ne, wato in zauna a haka ka ji daÉ—in rabuwa da ni ka ce na zama makauniya, ko idan baka rabu da ni ba ma " Haule ta ce
"Haba Kuluwa kina kife kamar ƙwarya amma bakin ki ba zai mutu ba" Banza Kuluwa ta yi da ita Hudu ya ce
"Wannan aikin fa ba ƙarami ba ne kawai a kira malam me ruƙiyya" Kuluwa ta ce
"Haba Hudu ni ce fa ba aljannu ne a jikina ba, kawai ɗanyen aiki suka mini idan ka kira mai ruƙiyya zai dakeni a banza ne"
Haule ta ce
"Wannan bokitin babu mai raba ki da shi in ba malam me ruƙiyya ba, idan aka musu karatu dole su saki bokitin"
Malam ya ce
"Kawai a kira shi" Ya faɗa a zuciyarsa kuma yana ayyana Allah sa ya mata dukan kawo wuƙa ko banza ya sake rama masa. Fita suka yi suka je gidansa aka kirawo shi, tsoho ne don har ya fara ranƙwafawa ma, sai wani mayashi da yake riƙe da hiramin nasa, Hudu ya wuce neman yaron nasa don haka daga Malam Nura sai Malam mai ruƙiyya da wannan matashin. Ko da suka shigo Haule tana tsaye a gaban Kuluwa, Kuluwar ta saka hannu biyu ta riƙe ƙafafun Haule wai tsoro take ji kar fa a je aljannun suna jikin bokitin.
Ko da Malam mai ruƙiyya ya zo hannunsa riƙe da carbi mai dubu, yana zuwa da ya gama zagaya Kuluwa buɗar bakinsa ya ce
"Aljanin me a cikin bokitin shi ne ya zama tsani tsakanin kanta da bokitin idan ma ba a yi a hankali ba yana iya raba kanta da jikin wuyanta" Kuluwa fitsari ne ya ƙwace mata jin wai aljani a jikin bokitin da yake manne a kanta da kuka ta rushe tana faɗin
"
"Malam ka yi addu,a su fita daga jiki, wallahi ban san inda zan saka rayuwata ba in suka rabani da kaina ba na so in mutu in bar Malam Nura ya rayu da amarya su soye ni ina can kwance cikin ƙasa!"
Malam Nura a zuciyarsa ya ce
'Ƴar baƙinciki sai mun yi soyayyar kuwa da zamanki da tafiyarki babu abin da za mu fasa' A fili ya ce
"Kuluwa ko kina raye ko kina mace ai zaman Hadiza matsayin matata babu fashi tun da an ɗaura aure, ki ji da wannan abun na kanki don idan har aljannun nan basu yarda an ɓamɓare miki wannan bokitin ba, ni fa kaina zan sa a yi yekuwa a gari, jama,a su zo a kwashe ki a baro a kaiki can dokar daji bakin ruwa, ƴan ruwa su ɗauke ki don ba za mu rayu da rabi da rabi ba domin kin zama rabi aljan rabi mutum" Baki ta buɗe za ta yi masifa duk da maganarta idan ta yi amsa kuwwa take kasancewar kanta a cikin bokiti yake. Malam mai ruƙiyya ne ya kai hannu yana mai yin bismillah ya ranƙwashi saman bokiti sannan ya saka hannu ya ja amma ya ji babu alamar fita.
Yana kallon Haule ya ce
"Babu wani ɗan icce ƙarami haka?" Da sauri Malam Nura ya ce