Sashe 4
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan ma ban baki ba ke ba a cin arziƙin ki ne, wata shegiya miya ba za ki nema ki yi ba a miki ciki a miki goyo, wato na nemi hatsin tuwo na baki na miyar ma ni kike so na nemo" Hannu ta saka da buga ƙasa ta ce
"Wannan ne baka isa ba wallahi, ni ba wahalalliyar mace ba ce, idan kanka zafi yake to ni nawa hayaƙi yake, masifa wane shege ta kashe, miya ce baka bada kayan yi ba ni kuma wacce na yo billahillazi ba zan bada ba, ɗumamen tuwo zan yi da ita gobe, nima gari na siya nasha da daren dan haka ka ɗauki tuwon ka fita min a ɗaki" Ganin ba zai iya masifarta ba ya miƙe tsaye ya saka ƙafa ya buge robar tuwon ya ce
",Aikin banza gayyar na ayya gayyar tsiya, ɗanyen tuwon, abin da har yau baki iya tuwo ba sia ɗanye, kana ci yana maka dariya, ai an kusa yin ta ta ƙare wato zan auro galleliyar amarya Hadiza mai iya girki da iya tafiya ta zo ta kawo sauyi a gidan nan" Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga ɗakin.
Cikin É—aga murya take faÉ—in
"Idan har tusa tana hura wuta za mu gani, lokaci zai nuna ai daman duk wanda ya ce bai iya kuka ba uwarsa ce bata mutu ba za mu jira zuwan amarya mu ga yadda za ku ƙare! Daman yanzu za a yi amarya mu za a shuka mu kamar dusa" Yana jin ta ya yi dogon tsaki har zai shige ɗakinsa ya dawo da baya ya zo ya ɗaya labulen ya ce
"Kin ba kanki amsa" Yana faÉ—ar hakan tafi ya shige É—akinsa.
Tun da ya kwanta yake juyi yunwa ta hana shi ya runtsa ya ɗakko waya ya kira Hadiza suka yi hira suka yi sallama yana jin suna hira tana tauna, alamar tana cin abu kuma yana jiyo muryar Zainaba tana batun akwai daɗi ya san kuwa nama da lemon da ya saya ne suke ci, shi an bar shi da ciki yana masa ƙugi.
Bayan sun gama wayar ya buÉ—e wani jug, gayan fura ne a ciki haka ya É—akko ya ci ya sha ruwa ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi da mafarkin an kawo amarya Hadiza gidansa.
Washe gari da safe yana fitowa ya ga yaran suna shan koko da waina, gaban Kabiru ya je yana faÉ—in
"Kabiru ina kuka samu waina?" Yaran suka haÉ—a baki wajen cewa
"Iyarmu ce ta saya mana" Baki ya washe ya kalli Haule da take gyaran wake ya ce
"Ku dai mata sai kuke kukan babu kuÉ—i alhalin kuÉ—i suna wajenku a nannage, ban san mai ya sa kuka fi kula da Æ´aÆ´anku sama da mazan ku ba, yanzu maimakon ki cika kwanon samira da wainar nan ki cika dogon kofi(Jug) Da koko ki kai mini É—aki in saka miki albarka amma kika yi mirsisi tusar ango" Kallo É—aya ta masa ta É—auke kai ta mayar da hankali wajen yin abin da take yi.
Yana tsaye ya ce
"Haule ba magana nake miki ba?" Kuluwa wacce take wajen murhu tana iza wuta ta ce
"Shiru ma ai amsa ce ga mai hankali" Cike da jin haushin ta ya ce
"Ni dai Kuluwa kin zame mini ƙarfen ƙafa wallahi, ina dalili ana magana da kishiyarki amma kina tare mata faɗa" Banza ta masa ta fara waƙa tana faɗin
"Wani mijin namiji ne wani kuma sauna ne" Kasaƙe ya yi yana cika yana batsewa ya ce
"Da wa kike?"
Tana É—an É—aga kai alamar mai jiran faÉ—a ta ce
"Wanda yake tsoron ta mutu... Kafin ta ƙarasa maganar fuuuu ya yi hanyar ɗakinsa ya fito da ledar kayan aron da ya je hira da su jiya ya zo a fita daga gidan.
Bayan ya mayar da kayan ya wuce wajen mai shayi ya sha shayi da biredi ya ƙoshi. Yana shigowa gida ya ce kira su ya ce
"Yau saura kwana shida ɗaurin auren nan, ina so in faɗa muku bakin ku ya ƙare" Haule ta kalle shi da mamaki ta ce
"Ban gane ba?" Ita daman Kuluwa kai ta É—auke gefe bata ce komai ba.
Ƴar dariya ya yi ya ce
"Ina nufin na sallame ku zuwa turaka!. Wato duk wani tanadi da zan yi nan gaba na amarya Hadiza ne" Su duka cike da rashin fahimta suke kallonsa yana tsaye hannayensa a cikin aljihunsa yana murmushin jin daÉ—i shi kaÉ—ai ya san irin amarcin da zai kwasa.
Kuluwa a harzuƙe ta ce
"Kamar ya wai?"
Ya nuna É—akinsa da hannunsa ya ce
"Ina nufin daga yau duk wacce take da girki to iya girki za ta yi babu ruwanta da zuwa turakar miji da daddare, yanzu lokacin amarya ne!"
Haule ta ce
"Sabon salo kiran sallah da usur, wannan amaryar da abin da za ta zo kenan?" Yana kaÉ—a kai ya ce
,
"Eh akwai wasu Æ´an magungunan gyara da zan fara sha to bana so maganin ya salwanta" Kallon -kallo aka shiga yi tsakanin Kuluwa da Haule Haule tana Æ´ar dariya ta ce
"Toh Malam ai abin wannan ba komai ba ne, idan ka ce a baka wata biyu ma sai mu baka ka gama cin amarcin...
Kuluwa ta bugi ƙirji ta ce
",Sannu Haule dami sarkin haƙuri, wallahi ba zan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine mini, wato ke saboda baki san ƴancin ki na mace ba za ki bar kwananki tun amarya bata tare ba namiji yake mata tanadin jikinsa, to ni dai ba zan yarda ba, tun da yau ma baki kwanana ne kuma bani da wani wajen kwana da ya wuce turakar Malam a yau, haka idan kwanan ya zagayo ma sai na je... Wani haushi da tsanar Kuluwa ce ya cika Malam daman ita take kawo masa cikas a kowane abu shi ya rasa wannan jaraba da ya je ya kwasowa kansa biyan bashin auren ta gashi ta addabe shi.
Ganin tana masifa shi ma ya ce
"Haule Allah miki albarka ai shi ya sa kika daɗe a gidan nan kika yi ƙarko"
Kuluwa ta yi karaf ta ce
"Ai ciwon kanta ne bata sani ba shi ya s... Haule ta haÉ—e rai ta ce
"Kuluwa ki taka a sannu fa, shiru -shiru ba yana nufin gudun magana ba, kawai kyalewa ce da son zaman lafiya, kuma na san ciwon kaina kawai biyayyar aure ce da bin maganar miji, ni nan da kika ganni ina iya sadaukar da duk wani abu don farincikin mijina, ina iya haƙura da jin daɗina don in faranta masa" Baki sake Kuluwa take kallonta ba tare da ta ce komai ba ta ɗauke idanunta daga kallon ta ta mayar kan Malam, don ita idan ta tsaya maimaita magana da Haule hawan ruwa ne zai kamata.
Tana kallon Malam ta ce
"Na faÉ—a maka ba zan yarda ba, kuma da ka saka mata albarka nima ai ba tsine mini aka yi ba"
Da yatsa ya nuna ta ya ce
"Ai duk ƙwawarki kwanan turakar miji ya barki Kuluwa ki ɗauki na annabawa... Tana tafa hannuwa ta ce
"Wallahi yau ma kwanana ne a É—akinka zan kwan...
Ya katse ta da faÉ—in
"Ga fili ga mai doki, in dai za ki je É—akin ki kwanta ga wurin nan, ni dai sunna ce ba zan aikata ba tun da na faÉ—a miki tanadin amarya Hadiza ne, ban da neman jaraba ma ke da kika kwana jiya a É—akin ki amma yau shi ne don na nemi ku bani lokaci shi ne kika hau dokin zuciya kike sukuwa" Banza ta masa ta juya ta ci gaba da aikin ta.
Hannu ya saka a aljihu ya ciro naira ɗari ya miƙawa Haule ya ce
"Ungo nan Haule, ai ke kam kina cin ribar zaman aure daman mai haƙuri shi yake cin ribar zaman duniya, kin ga jiya ga ɗari biyar ɗinki ta faɗar kishiya, yanzu ga naira ɗari ta haƙurin bin maganar miji ɗari shida me kika manta" Tana dariya ta ce
"Allah amfana, Allah barka da Hadiza amarya"
Ya washe baki kamar gonar auduga ya ce
"Amiiiiiin Haulen arziƙi"
Kuluwa ta É—ago daga sharar da take ta ce
"Ina tsiya ina wata ɗari shida, kamar wata matar kyankyaso zan ke karɓar wannan kuɗin ai wallahi sa,a ka yi da sai na ɓare maka kai a biyu"
Tsaki ya yi ya ce
"Ai duk namijin da ya auri mace mai baƙin kishi bai yi dace ba, gashi nan bakya cin ribar zaman auren kina zaune miji yana yi wa kishiya kyautar kuɗi"
Ta ce
"Ai ko ni zan iya kyautar sama da naira dubu ba wai naira É—ari ba" Ita dai Haule bata tanka musu ba, haka ya shige É—aki ya bar ta tana ta kumfar baki, sai ta yi shiru kamar an tsikare ta sai ta ci gaba da masifa ita kaÉ—ai.
Da yamma Kuluwa ta shirya ta nufi gidan Baba Ramma mahaifiyar Malam Nura da sallama ta shiga bayan an amsa ta same ta tana tuƙa tuwo, tabarma ta shimfiɗa mata suka gaisa Baba Ramma ganin ran Kuluwa a ɓace ta ce
"Kuluwa ina fatan dai kuna lafiya kuma kuna zaune lafiya" Kamar mai jira ta ce
"Ina fa zaman lafiya gidan kamar filin yaƙi"
Baba Ramma ta ce
"Ya subhanallahi mai ya yi zafi shi ba wuta ba?"
Kuluwa ta ce
"A kan wannan neman auren da yake yj ne sai tauro da abubuwa yake yana kafa mana dokoki a gidan duk sai kambama amarya yake yana nuna ta fimu matsayi"
Baki sake Baba Ramma take kallon Kuluwa cike da kasa ɓoye mamakin ta ta ce
"Ke yanzu Kuluwa a kan ƙarin auren ne kika kawo ƙaran mijinki?In ce dai ba ke kaɗai ba ce ita Haulen fa?"
Kuluwa ta ce
"Ita bata san inda yake mata ciwo ba"