← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 27

Sashe 25

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akwai wata ƙatuwar sanda ta dukan ɓarawo da na ajiye a ɗakina" Kuluwa wacce ta san girman sandar cike da ƙaraji ta ce
"Mai za a yi da sanda? Ana batun icce kana batun sanda, kaima malam mai ruƙiyya ina laifin ma ka ce a baka tsinken kwakwa tun da yanzu dai ni ce ba aljani ba kuma duk abin da za a yi ni zan ji a jikina"

ÆŠan rakiyar malam ya ce

"Ai dole sai an basu tsoro in ba haka ba ba za su fita ba" Wani yawu ta haɗiye tana jin babu daɗi Malam Nura wani daɗi yake ji a ransa ya ɗakko sandar ya kawo, Malamin ya ce tun da shi ya manyanta ba ƙarfi ne da shi ba, shi ɗan rakiyarsa ya karɓa ya buga a jikin bokitin, amma Malam Nura ya ce
"Malam ita mace fa a ko ina mijinta ne a gaba ka bari na buga mata ina kishin wani ya mata ab... Kuluwa ta katse da faÉ—in

",Malam kar ka yarda babu wata soyayya da kishi tsabar haushina ne da yake ji wallahi kana bashi sandar nan ba iya bokiti zai rotsa ba har da kaina zai raba a biyu"

Haule ta ce
"Kuluwa mene ne haka ana son nema miki lafiya" Tsaki ta ja ta ce
"Ai kin san akwai takun saƙa tsakanina da shi"

Malam mai ruƙiyya ne ya karɓi sandar ya shiga karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi yana tofawa a jikin sandar sai da ya gama sannan ya nannaaɗe hannun rigarsa ya buga sandar Kuluwa ji ta yi kamar a kanta ne aka buga, Malam yana ci gaba da karanto addu,oi, yana tofawa yana buga sandar lokaci zuwa lokacj ganin yadda take zabura kamar mai farfaɗiya ya sa yake danne dariyar muguntar sa tun da shi ya san mene ne ba aljannu ba ne.

Bokitin ya tsaye a biyu amma ƙasan yana manne da gashin, aka yi aka yi ya fita amma ya ƙi, sai da aka duba ta inda aka tsaga domin yanzu tana iya ganin mutane ma tun da an fasa bokiti daga saitin idanunta.

Kuluwa jin Mama mai ruƙiyya yana jan bokitin tamkar wanda yake jan gashin ta ta ce

",Malam gashin nan fa ana gama cire mini bokitin nan zan yi fakin É—insa da ribbon ka ga kuwa ka bishi a hankali" Takaici ne ya ishi Haule na maganar da Kuluwar take ita ana so a ceto ta amma ita tana ta gashi duk don saboda ta birge mijin da ba ita ce a gabansa ba.

Malam iya yinsa ya yi amma ya kasa fitarwa Kuluwa bata ankara ba ta ji ya ce

"Kun ga dai duk na cire bokitin gefe da gefe kawai iya tsakiyar kanta ne bai fita ba, shi kuma kamar ma tare aka yi shi da gashin kanta don haka mafita da shawara É—aya a kira Usaini wanzam mai aski... Tun kafin ya gama magana Kuluwa wacce gabanta ya bada sautin rassss jin an ambaci wanzam ta yi saurin faÉ—in

"Malam mai ruƙiyya aska zai ara maka ka yanke bokitin?" Malam mai ruƙiyya ya ce

"A,a ni da ba aikina ba ne riƙe aska, shi dai zai so ya saka askar ya askr gashin kanki shi ne mafitar...Tsaye Kuluwa ta miƙe tana faɗin babu wanda zai masa aski babu mai raba ta da gashin kanta ko ziri ɗaya!"

Malam mai ruƙiyya da ɗan rakiyarsa suka fara yi wa Malam Nura sallama za su tafi, Kuluwa har ta kama hanyar ƙofar ɗaki ta shiga ta je gaban mudubin ta ta duba ta ga babu alamar zai fita sai gata ta fito da sauri ta ce

"Haule na shiga uku za a mayar mini da kai babu maraba da na Malam Nura" Haule ta yi tsaki ta yatsina fuska ta ce
.
"To ai sai ki zauna a haka" Tana faÉ—a ta yi hanyar É—akin ta, Malam Nura ya ce
"
,Malam tun da fita za ku yi mu je fita zan yi nima na je masallacin isha,i daman amarya sai gobe za ta tare, Kuluwa ta ji daÉ—i da aka ce sai gobe amarya za ta tare, tana ganin za ta ci karenta babu babbaka tun da ta yi gyaran jiki, duk da tana jin haushi ta so a ce a gaban amarya za ta shige É—aki da angon ta cusa mata haushi.

Kuluwa ganin za a barta da rufaffan kai ba don ta so ba ta ce ta amince a kirawo shi. Tun da suka fita ta zauna tana garƙama kukan za a raba ta da gashin ta, gashi aljannu ne tana son zazzagin su da musu Allah ya isa tana tsoron sakamako ya biyo baya.

Suna fita Huale da ta fito daga É—aki ta shiga bata baki, har tana tambayarta mai ya sa ta saka wandon malam amma ta mata banza tana ta kuka, don ta so take taje gashin nan tana cusawa Hadiza haushi, duk da an ce Hadizar tana da gashi kasancewar mahaifiyarta buzuwa ce.

Haule tana gefe zaune a kan kujera zuciyarta cike da jimami kawai sai ta ji Kuluwa tana faÉ—in

"Wayyo gashina, wayyo zan zama warewa a cikin matan gidan nan, wata ma da gangan za take tamayar fita kitso don in ji haushi" ,Haule tsabar takaici banza ta mata saboda ita a ganinta ita da ta haÉ—u da iftila,in aljannu ai murna za ta yi da za a raba ta da bokitin.

Zuwa jimawa Malam Nura ya dawo yana rafka sallama shi da Usaini wanzam, Kukuwa ta tashi tsaye hannuwanta biyu a saman guntun bokitin na kanta tana kuka shaɓe -shaɓe Malam Nura a zuciyarsa ya ce
'Ke da Allah ya taimake ki ma ba ƙafafu na cirw miki ba, ai gwara gashi sau dubu in kika ɗaura ɗankwali babu mai sani amma aka mayar da ke gurguwa ai kin tagayyara.

Haule ce ta shinfiɗawa wanzam tabarma bayan ta amsa musu sallamar ta gaishe da shi, ya zauna da ƴar zabirarsa (Jaka) Mai ɗauke da kayan askinsa. Kuluwa tana ta ɓare baki ta zauna a gabansa ya cw Haule ta kawo kujera saboda ya ɗan yi sama, haka ya zauna a kujera yana faɗin

"Sannu baiwar Allah,, Allah ya tsayar a haka, wataƙila ma tun askin suna ba a saki miki aski ba amma gashi yau larura za ta saka a yi, Allah sa haka ne alkairi... Kuluwa ta ɗago tana banka masa harara ta ce

"Ina alheri a aske gashin matar da ba iya kaÉ—ai ba ce a wajen mijin ta, wato tana da kishiyoyi, gashin nawa da nake ta cancanawa ina alkin ta shi, ni ko da aka haifeni ba a mini aski ba saboda gashina bashi da yawa mahaifiyata ta ce a bar min amma yanzu za a aske" Usaini wanzam yana fito da kayan aikin ya ce

"Ƙaddarar kenan" Daga haka bai sake cewa komai ba, Malam Nura yana gefe zaune a kan wata kujerar yana danne dariyarsa ya san da a ce ta san shi ne ummul aba,isin wannan lamarin da mai raba ta da shi sai Allah, duk da yana gudun ɓacin rana watarana amma ya san dai ba za ta taɓa ganowa ba.

Bokitin ya ɗan ɓaɓɓalle, ya ɗakko ruwa da sabulu ya ɗan goga a gaban inda bai riƙw ba da yake tsakiyar kan ya fi riƙewa. Babbar askarsa mai kaifi ya saka ya shiga ɗaiɗaye gashin Kuluwa yana zubowa ƙafa tana kallo sai da ya aske duka amma ban da gefe da gefen Kuluwa ta kai hannu ta ji an mata rantal (ƙwal kwabo) A tsakiyar kan ta taɓa inda bai aske ba duk bai fi faɗin yatsan hannun ba ta ce

"Wannan É—in fa"

Wanzami ya ce

"Wai idan kin yi É—aurin É—ankwali sai kike fito da shi kin san gashi adon mace ne!" Kuluwa kamar ta yi kuka ta ce

"Saimka ce wata ƴar bori, za ka bar mini wani gashi kawai ka ƙarasa cirewa" Haka ya cire Haule tana ta jera mata sannu, yana gamawa ya saki kan Kuluwa tana zaune ta shafa da hannu ta ji wayam ta ɗago ta kalli wanzami, ta kalli Haule ta ce

"Haule ki riƙe sannunki tun da ba naƙuda nake yi ba!" Tana faɗar haka ta tashi fuuuuu ta yi hanyar ɗaki, dariyar da Malam Nura yake ta riƙewa ce ta ƙwace tun lokacin da ya yi ido huɗu d akan Kuluwa a hasken farin wata, har ƙyallin haskena farin watan ake gani a jikin kan, tana daidai shiga ɗakin nata ya tsagaita dariyar ya ce

"Kuluwa mai É—akin tsaka, É—akko masa kuÉ—in askin sa" Harara ta juyo ta dallawa Malam ya ce

"Ga ki da riga da wando da askekken kai sai kika yi kamar namiji" Banza t masa ya fita shi da mai askin yana ta dariyae mai askin yana nuna masa rashin dacewar hakan, a fili ya nuna yankarɓa a zuciyarsa ya ce

" Ai baka san wace ce Kuluwa ba shi ya sa'

Haule ma tsintsiya ta sanya ta share gashin ta kwashe ta naɗe tabarmar tana ɗan murmushi ta san da a ce yau ita ce tsautsayin nan ya faɗawa da Kuluwa sai ta yi ta ƙyalƙyalar dariya.

Kuluwa tana shiga ɗaki ta cire kayan ta canja wasu zauna tana ta addu,ar Allah ya sa aljanin nan ya yi wa Haule da Hadiza abin da ya mata don a dawo ɗaya!. Haka ta kwanra cike da takaici haushin Malam Nura take ji can zuwa jimawa ta ɗauro ɗankwali ta fito ta sake alwala ta yi ta yi sallolin ta ta kwanta, don ko sha,awar zuwa turakar Malam ɗin ba ta yi tun da aka mata aski, haka ta ringa murƙususun ciwon marar magungunan da ta sha!.

Malam Nura bayan ya gama komai ya dawo gida, yana ɗan duƙawa, saboda mararsa da take riƙewa cike yake da buƙata amma babu hali tun da amarya tana gidansu, shi kuma don ita ya yi gyara don haka ba zai je wajen sauran matan ba. Haka ya ringa safa da marwa yana neman ɗauki amma daga karshe ya jiƙa jar kanwa ya sha ya samu dama-dama ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi cike da mafaekin tarewar Hadiza.
Chapter 25 · 0% Book details