Sashe 21
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malam Nura sai ya tsinkayi muryar amarya tana faɗin a kirawo Zainaba da Shafi,i nan fa aka kira su, amma Zainaba dakyar ta zo tana ta kumbure-kumbure don ta tsani Malam Nura babanta take tayawa kishi, shi ma Malam Nura a nasa ɓangaren haka ne, burinsa kawai ya ɗauke Hadizarsa a bar waɗannan ƴaƴan musamman ma Zainaba. Ko da aka jeru za a musu hoton da yaran kowa yana ta washe baki amma Zainaba ta cukule fuska ban da harara da take aika musu babu abin da take, sai za a ɗauki hoton ango da amarya suna kallon juna cike da soyayya shi kuma Shafi,i shi ma dariyarsa yake amma Zainaba sai ta shiga banka musu harara kamar idanunta za su faɗo!.
A hakan ne cike da rashin sa,a Malam Nura ya ji tazugen wandon jikinsa ya cire daga cikin wandon. A take ya ji tsantsar wandon ta masa yawa, daman ya san ya yi kaɗan tazugen dakyar ma ya ɗauru saboda ƙanƙantarsa, shi kuma garin sauri bai tsaya ya canza wani ba, idanu ya ɗan zaro a ɓoye yana ɗan yatsina fuska kamar mai jin kashi a zuciyarsa ya ce
"Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahima, li,ilafi ƙuraish, ilafihim rihlatash shita,i wassaif fal,ya,abudu rabba hazal bait allazi aɗ, amahum min ju,in wa aamanahum min kauf" Ya faɗa wani gumi yana karyo masa. Da sauri ya saka hannunsa a cikin aljihun rigarsa, ya riƙe saitin ƙugun nasa ta yadda wandon ba zai zame ya faɗi ba, tun da yanzu babu inda yake a riƙe sai hannunsa da ya riƙe shi.
A zuciyarsa ya ce
'Allah ka taimakeni kar wandon nan ya faɗi, kar ya tsinkani a idon jama,a, ya Allah yadda aka taru ake kallonmu ni da amaryata muna birge mutane Allah kar ka saka wandon nan ya rusa farincikin nanu, Allah kar ka ba wandon nan ikon ya kunyatani, yadda kowa yake kallona kamar wata ɗan daren goma sha uku ka sa abun nan ya ɗore' Ya faɗa yana sake bada ƙaimi wajen damƙe tsantsar wandon.
Mai hoto cike da bada umarni ya ce
",Amarya kama hannun angon" Amarya tana murmushi ta miƙa hannu ta riƙo hannun Malam Nura da yake cikin aljihu yana riƙe da wandon, ta riƙe tana faɗin
"Cire hannun mana ya ka saka shi a aljihu?" Malam Nura idanu ya shiga rabawa a zuciyarsa yana faÉ—in
'Shikenan asirina a tonu, ya zan yi idan wandon nan ya zame Hadiza ta ga haÉ—e yake da tsohon wandona na yadi aka yi faci' A fili ya ce
"Ai na fi ganin kyauna idan hannuna yana cikin aljihu" Ya faɗa cike da ganin vata kunyata shi ba. Bata kawo komai a ranta ba ta riƙe hannun ana ta musu hoto shi kuma ya riƙe wajen gagam, don Hudu yana lura da shi ya ga hatta wajen da ya riƙe ƙafar wandon har tattarewa ta yi, shi kaɗai yake dariya a ransa duk da bai san mene ne ba amma banya raba ɗayan biyu matsala ce domin ya lura gabaɗaya abokin nasa ya fita hayyacinsa ba kamar lokacin da ake hoton ba duk ba a nutse yake ba.
Dabara ce ta faɗo masa yana cikin tunanin yadda zai yi ne wayarsa ta shiga ƙara, ya fito da ita ko gama ganin waye bai yi ba ya raɗawa amarya cewar Goggo Ramma ce take kiransa, haka ya ɗan ja gefe yana wayar ƙarya, da ta faki ido sai ya sha wata ƴar kwanar lungu, a kan wani dogon tsumma ya yi wa idanunsa masauki, da sauri bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ɗauka ya ɗage rigar ya zare mazugin cikin, ya gyara wandon ya saka tsumman da ya tsinta ya ɗaurew wandon daga sama wato daga ƙugunsa wandon ya tsaya ya saki rigar yana sakin wani gauron numfashi. Fitowa ya yi daga lungun ya dawo yana ta jin daɗin ya tsira da mutuncinsa, amma dai alla-alla yake ya bar wajen tun kafin a yi abin da zai kunyata.
Haka dai aka sha hoto sai wajen ƙarfe shida saura ango za su tafi, abokan sun ɗan yi gaba sun tsaya shi zai yi sallama da amarya, yana tsaye yana washe baki ya ce
"To mu za mu tafi"
Amarya ta ce
"Tohm kuɗin karin nawa fa" Yawun bakinsa ne ya ƙafe ya ce
"Wane kuɗin kari kuma, ke da za ki kwana a gidana ai akwai su Haule a gida sai abin sa ranki yake so za a girka da safe" Ranta ne ya ɓaci ta ce
"Ai na faÉ—a maka ba yau zan tare ba ko?" Idanu Malam Nura ya zaro a zuciyarsa ya ce
'Ashe kuwa wanda ya mutu zai falko, duk wannan wankan da na yi don kin raina mini hankali, to ai kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba mai kaza ya tashi da fifike' A fili kuma ya ce
"Amma dai wasa kike ko Hadiza?"
Farrrr ta yi da ido sai da bakin idon ya ɓace ɓat sai farin sannan ta dawo da idanunta daidai ya ce
"Wai wasa an faɗa maka a komai ake wasa ne, wallahi da gaske ba zan rare yau ba, kaima da wata magana yanzu fa batun ƙarfe shida na yamma ake yi ko jere ba a je an yi ba, kuma a yaushe zan tare?"
Malam Nura ya kalle ta ya ce
"To mene ne abin wahala a wani jere, yanzu wasu Æ´anmatan ma sai da isha,i ake tafiya da kayan a jera ai ba wahala ba ne gado ne fa kawai za a ajiye yanzu da gabaÉ—aya ma jeren maza ne suke yi"
Hadiza ta ce
"To bari ka ji ni wallahi kayana suna wajen kafinta da na saya daman sai za a jera za a ɗauke su daga can a wuce gidanka da su, ka ga a yanzu kuwa lokaci ya ƙure"
Malam ya ce
"Ni yanzu daga nan sai na je wajen kafinta a É—oro kayan a baro wallahi ina iya jerasu duka ke kuma in aka yi isha,i sai a kai ki"
Baki ta taɓe ta ɓata rai ta ce
"Kamar wata amaryar kunkuru, to wallahi ba zai yiwu ba so kake ake gulmata ana faÉ—in ango ne ya mini jere, yadda kowace mace ake zuwa a jera mata kaya haka za a mini, kuma in tafi a tsanake, duk ka hana kanka sakat kamar dai baka da mata a gida, ni wanna auren jin sa nake kamar auren farko don haka a tsanake zan tafi"
Malam ya tari numfashin ta da faÉ—in
"To ko amaryar buzuzu ce ba dole a yi ɗokin ta ba, kuma da kike batun matana ai na san da zaman su, ke fa na ce miki wata guda za ki yi kina amarci, babu wacce za ta karɓi bakin kwananki" Fuska ta yatsina ta ce
"Wllahi ko shekara za ka bani ba zan tare yau ba!" Su Hudu ne suka matso ganin abin yana neman wuce makaɗi da rawa, Bintu ma suka matso na aka shiga basu baki, a ƙarshe dai an shawo kan amarya ta ce za ta tare amma sai gobe, nan su Hudu suka shiga lallashin Malam a kan ya haƙura yau da goben ai duk ɗaya ne!. Ba dan ransa ya so ba sai don ba yadda zai yi haka ya haƙura, cikin ransa tsanar Kuluwa ce fal don ya san ita ta haddasa komai, da tun farko ya zo da shaddar a jikinsa daga wajen ɗaurin aure da tuni an jera kayan amarya ta tare a yau, amma da yake ta yi fushi tun da aka ɗaura auren shi ya sa ko shirin tarewa yau bata yi ba.
Haka ya bata 5k don ta ce yau kuÉ—in ba iya na kari zai bata ba har da na abincin dare!.
Ko da suka taho a hanya suna ta zolayarsa amma shi kaÉ—ai ya san halin da yake ciki, banza ya musu kawai so yake ya samu abin da zai yi wa Kuluwa sanadiyyar daren amarcin da ta masa yau!.
A can gida kuwa da magriba Haule ta fito da shirin fita tana faÉ—aw Kuluwa za ta je gidansu duba babanta, har tana cewa Kuluwar ko ita ma za ta je su fita tare. BuÉ—ae bakin Kuluwa ta ce
"Ni in fita yanzu haba Haule ai ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, in ban da ma ke ina za ki samu damar fita ana jimawa fa ƴan kawo amarya za su yi wa gidan nan kutse" Baki ta taɓe ta ce
"To wa ya aikeni bare ya ga na daɗe, ai dubiyar dai ta fiye mini, amarya kuma da ba a kaina za a ɗora ta ba ina ni ina su, kafin dai su kawo ta zan dawo don ba zama zan yi ba, kar a zo a ce kishi ne ya sa na ƙi zama a gidan basu san ni auren Malam Nura ko a gefen takalmina ba"
Kuluwa ta ce
"Ai ni ina nan na kasa na tsare, na je na yi wa baban naki sannu idan ƙura ta lafa don yanzu ba zan iya nisa da gidan nan a mini sakiya da ba ruwa" Da mamaki Haule take kallon ta ta ce
"Ban gane ba, wace ƙura kuma sai ka ce wanda guguwa ta taso, wai ke Kuluwa ba za ki sauƙaƙawa kanki kishin wanda bai damu da ke ba, yanzu ban da Allah ya takaita da ba tuni ya lahanta ki va" Baki ta taɓe ta ce