← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 27

Sashe 20

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hummm ba Hadiza ba ko Hadizo ce ta zo ina nan ina jiranta, tun da dole a ci kasuwa da maƙiyi, kuma hangen dala ba shiga birni ne ba, in da Malam Nura ne kaska ne raɓi mai jini ki bar shi da gashi, ai mai kashe miciji sai ya yi niyya zai ɗauji sanda, a yi dai mu gani idan tusa tana hura wuta, mu dai mazaunai ne ko dan zama za a neme mu, mu zuba mu gani, matuƙar ta shigo gidan na ƴar kallo za ta zama, don ni ce da ragamar mijina, an aure min miji maimakon ta koma gidan mijin ta shi ne aka ƙi cin biri aka ci dila" Duk wannan karin magaanar da take Haule tana jin ta bata taka mata ba.

Malam Nura yana fita ya amsa kiran Hudu nan ya faÉ—a masa gasu nan zuwa, haka suka zo da wasu abokan nasa guda biyu suka É—unguma zuwa gidan su Hadiza suna ta zuzuta irin kyan da ya yi.

Malam Nura ya murmusa ya ce

"Ni fa daman na faɗa maka Hudu sai na daka shaddar nan, amma dai har yanzu ina kan bakana idan ka samu mai saye ya zo na fansar masa" Hudu ya yi ƙasa da tashi muryar kamar yadda Malam ya yi lokacin da zai faɗa masa ya ce

"Waye zai sayi wannan shaddar wando da É—ori É—ori" Shiru ya yi sai kuma ya ce

"Ai idan aka samu mai son banza tsaf zai saya yake maleji, tun da nima ai sauƙi zan masa tun da na san wandon haɗi-haɗi ne wato yadi da shadda, wa ya ga haɗin gambiza" Ya ƙarasa faɗa yana dariya.

A ɓangaren Hadiza ita kaɗai ta san irin ɓacin ran da ta ƙunsa, ranta ya sosu game da abin da Malam Nura ya mata abin ya fi mata ciwo ma da ya kunyatata a gaban ƙawayen ta bayan ta gama shirga musu ƙarya. Ta san ko ƙaramar hauka za ta yi Malam Nura ba zai sake ta ba amma dai ta ƙudurta a ranta cewar ba za ta tare yau ba ko ana muzuru ana shaho,a ƙalla sai ta shafa satika ba ta tare a gidansa ba sai ta gama bashi wuju-wuju sai ya san ita ya tozarta.

Haka ta wuni suƙuƙu ranta a ɓace, don Zainaba ma sai da ta ce mata

"Inna wai ya na ga angon bai saka sabon kaya ba, kika ce tare ya siyo mana shaddar, wallahi ko kaɗan bai yi kyau ba kamar dai ba ango ba, sauran abokan nasa duk sun fishi yin kyau, ai daman babana ya fishi iya gayu shi ya sa na ce ki koma amma kika ƙi" Harara ta zabgawa Zainaba kamar idanun ta za su faɗi, da sauri Zainabar ta bar wajen tana ƙunshe dariyar ta.

Da yamma kasancewar ta yi gayyata hakan ya sa ta sake sabon ɗauri inda aka mata kwalliya da ɗaurin ɗankwali, haka suka fito ana ta gaisawa da muyane da suke Allah sanya alkairi. Kamar an ce ta waiwaya idanunta suka sauka a kan su Hudu da sukw tahowa, tabbas ta gane su Hudu domin Hudu bai sauya kayana jikinsa ba, sannan sauran abokan ma duk ta gane su tun da da su aka zo ɗazu, wato ta shaida kayan jikinsu duk da cewar daga ɗan nesa ne ta hango su. Na huɗun ne bata gane ba, mai kalar shaddar irin ta jikin ta, wani ɗan gayu ta gani amma da yake ta san Malam Nura bai zo ɗaurin aure da shadda ba ma, shi ya sa bata ma yi tunanin shi ba ne. Ranta ne ya ɓaci domin ta san abokansa ne ya aiko su zo su bata haƙuri a kan yana ya kiranta bata ɗauka, kuma ta san dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, ma,ana duk a kan maganar tarewar ta ce yau, za a kafa mata ƙahon zuƙa, ita kuma ta saka a ranta daidai da zamanin su take, wato sai ta musu tatasss sannan ta faɗa musu ba za ta tare ba sai nan da sati biyu kuma sai idan ya cika sharuɗɗan da za ta gindaya masa, juyawa ma ta yi daga kallon nasu ta ci gaba da gaisawa da mutane don ma kar su ga fuska su yi zaton za su samu sassauci daga gare ta.

Malam Nura ganin an kusa zuwa wajen da sahibar tasa take sai wani bubbuɗawa yake shi ala dole yana son kashe ta da mamakin wankan da ya yi. Sai da suka zo dab da su Hadizar ya mayar da wayarsa aljihu ya sanya hannayensa duka biyu a aljihun rigar ya tsaya daga gefe irin tsayuwar nigogin nan yana son ya mata ba zata don ya san ranta a ɓace yake tun daga batun shaddar nan. Shi kuma yanzu so yake a daidaita ta tare a yau domin ya gama shiryawa yau a matsayin ranar tariyar ta, kuma ranar amarci.

Ko da suka zo su Hudu ne ya yi musu sallama, suka je gaban su Hadiza, shi kuma ta bashi baya don haka bata ganshi ba. Hudun yana mata magana amma ta kauda kai gefe sai su Bintu ne suka amsa sallamar, yana dariya ya ce

"Ni da ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Cike da masifa ta ce

"Malam Hudu to na ga dai aure ne an ɗaura, to yanzun mai zan muku da kuka zo kuka tsaya mini, baka ga ina tare da mutane ba? Idan ma batun jere kuka zo ku koma ku faɗawa Malam Nuran ni Hadiza gayu na ce tariya ba yau ba, sai nan da sati biyu zan tare!!!" Malam Nura da yake bayan ta tsaye bai san lokacin da ya gyara tsayuwar nigogin da ya yi ba, gabansa yana faɗuwa ya haɗiye wani yawu muƙut, ba komai ne ya sanya shi wannan fargabar ba sai tunawa da ya yi da cewar ya shanye maganinsa da zai fito wanda aka ce kuma sai ranar da amarya za ta tare zai sha, daɗin daɗawa ma maganin kaf cikin magungunan Hudu ya ce masa ya fi kowanne tsada ya fi kowanne aiki.

Su Bintu da suke kusa da ita su biyu É—aya tana bata baki, da yake sauran matan da suke wajen ganin zuwan mazan sai suka É—an basu waje, amma Bintu da yake tafiyarsu É—aya daman kamar yadda hausawa suke cewa sai hali ya zo É—aya ake abota, Bintu ta ce

"Ina bayan ki ƙawata, ai kina da ƴancin ki yi yadda kike so, auren zawarci ne fa ba wai na budurci ba, kin ga kenan ko wata biyu kika ɗauka ba sati biyu ba kin da fiye da wannan damar...

Kafin wani ya sake furta komai Malam Nura ya yi taku ɗaya biyu sai gashi a gaban amarya, yana zuwa ya ja ya tsaya hannuwan nan biyu a aljihu yana kashe ta da wani murmushi, don ba zai tsaya a masa sakiyar da ba ruwa ba, yana kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa gwara dai ya yi duk yadda zai yi ganin bai yi asarar wannan ranar ba, bai yi asarar kuɗin maganinsa da ya bankamawa cikinsa ɗazu ba.

Tsayuwarsa ta dakatar da su Hadiza da maganar ka ce na ce idanu ta zaro baki sake ita kanta ganin irin kan da ya mata bata san bakin ta ya furta

"Angina malam Nura?" Kansa ne ya ji ya masa gingirim daman kuma ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, ya san in har ta ga wankan nan nasa ƙarya take ta ce bai yi mata kyau ba, shi ya san wanka iya wanka.

Yana murmushi ya ce

"Na,am amaryata Hadiza" Daɗi ne ya baibaye mata zuciya musamman da ya zo a wannan daidai gaɓar da wurin yake a cike, kowa dai zai ganshi ya san ba ƙarya ta yi ba.

Tana kallonsa ta ce

"Wannan kyau haka" Ya gyara tsayuwa ya ce

"Ai daman na faÉ—a miki zan baki mamaki"

Bakin ta har kunne ta ce

"Ai kuwa ka bani ina sonka Malam Nura"

Allah ne kaɗai ya san daɗin da Malam Nura ya ji musamman da ya ga ta mayar masa lulluɓin da ta cire masa ɗazu a gaban ƙawayenta da abokansa, amma yanzu gashi ta sake rufa masa bargon mutunci.

Da kanta ta matsa kusa da shi suka jeru, a take abokansa suke musu kirarin sun dace, ƙawayen nesa sukaa matso kusa ana ta sakin guda Malam Nura a zuciyarsa ya ce

'Ai Kuluwa ba ƙaramin cutata kika yi da kika ƙona wandon nan ba, Allah ma ya taimakaeni an mini dibara da yanzu kin jaza mini tsiya, to amarya tana ba za ta tare yau ba ai ɗan jijjiɓin bala,i kenan"

Hadiza ta fito da wayarta daga jaka ta shiga kiran mai hoto yana É—auka Malam Nura ya ji tana faÉ—in

"Ka zo yanzu ango da abokansa sun ƙaraso za ka mana hoto" Malam Nura ya ciro hannayensa daga aljuhu ya shiga gyara hularsa, suka haɗa ido da Hudu da yake ta faman doka murmushi ganin sun samu karɓuwa.

Daga ɗaya ɓangaren mai hoto ya ce

"Ba kin ce shikenan ba?"

Kamar ta falla masa mari haka ta ji da ya yi wannan furucin ta ce

"Na faɗa maka ka zo yanzu" Da to ya amsa mata, nan ta kashe wayar tana aikawa Malam Nura kallon soyayya shi kuma gogan sai wani kashe mata ido yake ransa fari ƙal.

Shi Malam Nura yanzu maganar hoto ce a gabansa, shi dai a musu hoton nan da amarya wanda za su kafe a É—akunan su. Yanzu babu batun ya yi maganar tariya a nasa ganin tun da daman fushin rashin saka kaya mai kyau ne ya janyi cecw ku ce É—in da ta ce ba za ta tare ba yanzu kuwa ai babu wanna batun.

Mai hoto aka sauke a mashin nan ya shiga aikin sa babu ƙaƙɗautawa don su Hudu gefe suka koma suka zubawa sarautar Allah ido, mai hoto yana ta basu style ɗin yadda za su yi, yana ta walla musu hoto, ya musu ya fi kala goma sha biyar, nan suka nuna masa wanda za a musu na bango.
Chapter 20 · 0% Book details