Sashe 3
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Au baka bani kuɗin karin safe ba, ko goben da tuwo kake so na karya" Yana kallon yadda ta masa wani farfari da idanun ya saka hannu a aljihu, dubu biyu ya ɗakko ya bata ko godiya babu ta karɓe, juyawa ta yi ta fara takun nan nata da yake so ya saki baki kamar dolo yana kallon ta tana dab da shigewa ta jiyo tare da masa bye-bye, shi ma hannun ya ɗaga mata ta shige ya juya ya fara tafiya ransa a matuƙar ɓace, don ko hirar kirki basu yi ba ga asarar nama da lemon kwalba.
Tun da ya kama hanyar gida ya tsinewa Zainaba ya fi cikin carbi, ya ƙosa asabar ta yi a ɗaura auren Hadiza ta koma gidansa ko ya huta da ganin wannan fitsararriyar yarinyar. Kayan jikinsa ya duba ko zai ga datti a jiki domin so yake ya je ya cire ya haɗa da na jiya ya mayar inda ya karɓo, saboda tsabar maƙo ba ya iya ɗinka sutura ta kirki amma yanzu da yake neman auren Hadiza shi ne yake arowa yana sakawa dan gudun kar a raina shi.
Da sallama ya shiga gidan babu kowa a tsakar gidan sai Kuluwa, ita Haule tana ɗaki ita da yara tana musu tatsuniya, Kuluwa jin muryarsa sai ta ji tamkar ya caka mata mashi a maƙoshi, ta yi banza da shi ta buɗe randa ta ɗakko ruwa a kofi, tahowa ta yi lokacin ya zo daidai saitin ta zai tafi ɗakinsa, buguzum-buguzum ta zo wucewa kaɗan ya rage ta bangaje shi. Tana shiga ɗaki ya tsaya gyaran murya ya yi a saita bakinsa yadda amon muryar zai isa ga kunnen ta ya ce
"Kai gaskiya mace ƴar duma-duma mai diri ta yi, ko tafiya take sai ka ga ɗagwas-ɗagwas, ,gwanin sha,awa na yarda mata suna suka tara, amma wata macen idan ta taho yadda aka san motar tantan za ta wuce... Kuluwa wacce tun da ya fara magana ta tsaya tana huci kamar zakanya domin a take zuciyarta ta raya mata cewa da ita yake wato amaryarsa wacce ya kira da suna mai jiran gado ita ce ta iya tafiya, tun da dai ta san duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake, rai a ɓace ta dangwarar da kofin hannunta wanda ta ɗauki ruwa, ta taho a sukwane don zuwa a yi wacce za a yi ita da Malam Nura don ba za ta bar wannan maganar ba, ta sanya a ranta ita da amaryarsa shege ka fasa domin za a yi zaman doya da manja!.
MAMAN AFRA
09025576222
[4/6, 5:18 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿ï¸2ï¸âƒ£
Malam yana tsaye sai ganinta ya yi kamar an jefo ta, ta fito ta tsaya tana huci kamar zakanya, da kallo ya bita yana aro jarumta ya tsuke fuska amma alamu sun nuna Kuluwa bata lura da tamke fuskar da Malam Nura ya yi ba don idanunta sun rufe da kishi hakan ya sanya ya zuba mata na mujiya. Sai da ta tsare shi da ido tq ce
"Nura wace ce take tafiya kamar motar tantan ɗin? "Ta faɗa yana kallon yanayin ta ya gama gane ta haɗa kanta da baƙar wahala don baƙin kishi mugun ciwo ne musamman na mijin da bai damu da kai ba, kuma ba ya ɗaukar duka ɗawainiyarka.
Sai da ya danne dariyar da ta so ƙwace masa ya sassauta murya ya ce
"Haba Kuluwata, ni a wa zan kira ki da motar tantan ki duba kanki da kyau ai idan diri ake nema da iya tafiya sai dai mata su take miki baya, amma ai ke tafiyarki kamar ƙirga sawun ki kike" ,Shiru ta yi tana binsa da kallo amma ƙwaƙwalwarta tana raya mata avubuwa da dama ciki kuwa har da nuna mata raina mata hankali ya yi hakan ya sa ta ce
"Ka ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, ai ni na san ba a sakewa tuwo suna, mai hali ba ya canjawa, ai duk wannan maganganun naka ba ganewa zan yi ba wai an yi yamma da kare, tun ba yau ba na san cewa kai munafukin mata ne k... Hannu ya ɗaga mata a ƙufule cike da faɗa ya ce
"Dakata! Kuluwa, ni nan da kike ganina na fiki hawa tamfar ɓacin rai don haka ki taka a sannu ko na shuka miki rashin mutunci, ni yanzu hankalina a kan sabuwar amaryata yake dan haka a halin da ake ciki yanzu ina kan bakana na cewa mata suna suka tara! Kuma Hadiza ita ce zara a cikin matan" Yana faɗar hakan ya juya ya yi hanyar ɗakinsa ya barta a tsaye tana jin tamkar ya watsa mata wuta da ya ce Hadiza amaryarsa ce Zara kenan su duk suna suka tara wato ba mata ba ne su.
Har ta kama hanyar ɗakinsa ta fasa ta juya ta shige ɗakinta tana jin tamkar ana hura wuta a zuciyarta, tana shiga ta kwanta tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa lamarin ta yadda za a fasa wannan auren domin ita bata fatan Malam Nura ya ƙara auro kowace mace har duniya ta naɗe!.
Yana shiga ɗakinsa ya cire kayan jikinsa ya mayar da linkin ya ajiye ya saka wasu kayan, cikinsa ne yake ƙugi yunwa yake ji tamkar ƴaƴan hanjin cikinsa za su fito su nemi abinci da kansu haka yake ji. Tunanin inda zai samu abin da zai saka a cikinsa ya yi jim kaɗan ya fito ya je ya rufe ƙofar gidan, ɗakin Haule ya nufa yana shiga ya same ta a zaune tana lissafa ƴan kuɗaɗen ta lokacin duk yaran sun yi bacci, daman yaran uku ne nata biyu ɗayan kuma wata mai rabon haihuwar ce a cikin matan da ya aura ta haifa ta kawo masa ita ta karɓa take riƙewa.
Kasancewar basu samu haihuwa da wuri ba tun da babbar Æ´arsa Alawiyya tana da shekara tara, sai Kabiru mai shekara shida, su ne Æ´aÆ´an Haule, da kuma Lauwali mai shekara huÉ—u shi ne ba É—an Haule ba. Allah da ya taimake shi duk yawan aure-auren sa matan ba sa samun ciki da yanzu Æ´aÆ´an sun kusa ashirin. Yanzu yana da shekara talatin da bakwai a duniya, inda Haule take da shekara talatin da É—aya, Kuluwa kuwa ashirin da tara.
Haule mace ce mai haƙuri da kawaici abin duniya da duniyar ma basu dame ta ba, inda Kuluwa take masifaffiya da baƙin kishi tana da masifa sannan bata barin ta kwana. Shi kuma Malam Nura mutum ne mai son mata sannan yana da maƙo ba ya ɓanɓaruwa ta daɗin rai kuma mutum ne shi da ba ya sauke haƙƙin iyalansa bayan yana da hali tun da manomi ne sannan yana neman kuɗi amma kulluɓ cikin tarawa da kuma ambaton babu yake.
Yana shiga ta yi saurin ɓoye kuɗin nata duk da bata san cewa ya gani ba, tun da ya san halinsa mutum ne mai son abin wani yanzu yana iya cewa ta ara masa kuɗin. Yana washe baki ya samu bakin gadon ya zauna ya ce
"Haulatuwa uwar gidan ran gida, uwar gida sarautar mata, ke ce ta farko kuma kowacce bayanki take bi" Ɗan kauda kai gefe ta yi tana rayawa a ranta cewa sai yaushe zai daina zambaɗa ƙarya da kuma daɗin baki, ta ɗan saki murmushin irin ta ji daɗin nan a fili ta ce
"Wannan haka yake, kana fasa min kai fa amma" A zuciyarta kuma ta ce
'A haka za ka ƙare kullum cikin daɗin baki abin da za ka faɗawa wannan daban wanda za ka faɗawa wacccan ma daban shi ya sa duk lokacin da gidanka aka ce akwai mace fiye da ɗaya kai kake haddasa fitina amma a guji zuwa rafi wata rana tulu zai fashe!'
Yana É—an washe bakin samun nasara ya ce
"Kin cancanta ne" Dariya kawai ta yi ya É—an sauke numfashi ya ce
"Za a samu wani abu a nan ne?" Tana kallon sa ta ce
"Kamar me?"
Ya ce
"Abin da zan saka a bakin salati yunwa nake ji" Sai da ta karkata kai gefe ta ce
"Ayya daman gayan tuwon da Kuluwa ta bamu na yi miya su kansu yaran bai ishe su ba sai da na siya musu awara suka ƙara" Shiru ya yi yana nazari ya san shi ya bada hatsi kaɗan wanda ba zai isa a ci a ƙoshi ba sannan bai bada kuɗin kayan miya ba ya san kuwa Kuluwa ko da danginsa zai zo bai isa ta bashi miya ba.
Ya É—an yi jim ya ce
"Kuma babu sauran miyar?" Ta ce
"Wallahi babu" Miƙewa tsaye ya yi ya fito ta taɓe baki ta bi bayansa da kallo. Yana fitowa ya nufi ɗakin Kuluwa ya shiga tana zaune ta doka uban tagumi ita kaɗai ta san tunanin da take kusa da ita ya je yw zauna sai da ya zauna ma ta lura ya shigo ɗakin. Wata harara take zabga masa kamar idanunta za su faɗo ya rausayar da kai irin nn ƴan duniya ya ce
"Kuluwa tawa, ni kuwa na Allah" Wani gajeran tsaki ta ja ta ce
"Kanka ake ji mahaukaci ya faÉ—a rijiya" Basarwa ya yi ya ce
"Ki bani tuwo ina jin yunwa" Tana masa kallon tsaf ta ce
"Inda ka je ba a baka ba?"
Yana kawar da maganar ya ce
"Bani da inda ya fi nan, wallahi yunwa nake ji kamar in ci babu" Dariya ta yi mai haÉ—e da shewa ta ce
"Da za ka ci babun ma da ya fi" Ganin abin nata ba na ƙare ba ne ya ce
"Ke Kuluwa abin naki ya isa ba fa tsoronki ake ba, ki É—akko tuwo ki bani tun da ba ke kika noma mini hatsin ba" Kamar jira take ta tashi da sauri ta janyo wata roba da tuwon yake ciki ta turo gabansa ta ce
"Inda wannan gayan tuwon ne gashi nan"
Yana kallon tuwon ya ce
"Ina miyar?"
Ta ce
"Wacce ka bani kuÉ—in cefanen na yi?" Yana zare ido ya ce