← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kawai ka haƙura da shaddar nan ka samu wani kayan ka saka" Yana masa kallon ka janyo ruwa ya ce

"Haba Hudu ka hana ni sakat da maganganun da ka san amsar su, yanzu a kaf suturuna ina na ga wanda zan shiga taron jama,a, babu wani kayan kirki fa ka sani, a ce kamar aurena da Hadiza amma ban saka kaya na kirki ba, ni wallahi damuwata ma idan har ba da shaddar nan na je wajen Hadiza ba wallahi ba za ta ɗauki hoto da ni ba, har fa cewa ta yi za ta kafe hotonmu a ɗakin ta, wallahi Kuluwa idan muka yi gaba da gaba ni da ke ina ga ba wai ƙafafu kawai zan datse miki ba, gunduwa-gunduwa kawai zan yi da ke" ,Ya faɗa kamar an caka masa wani abu ya zabura ya koma ya buga taɓaryar hannunsa da ƙarfi a jikin ƙofar ɗakin nata, da yake ta san ƙofar tana da ƙwari ta ce

"Lokacin da zan fito ma baka gidan nan, kuma dole ka aika mini takardar sakina... A masifance ya ce

"Ƙarya kike mai mugun hali, ai wallahi ba zan yi asarar kuɗina ba da aka ɗaura mini aure da ke, ba yanzu zan sake ki, bare ma ke da kika mini aika-aika ai ko a gurguce kike sai na ci gaba da gana miki azaba a gidan nan, ke Hadiza ma a kan bayanji za take zaunawa tana tuƙa tuwo, kuma dole ki sunkuya ai sai kin karɓi ukuba...

Saboda ta sake cusa masa haushi ta ce

"Haule miƙe mini wannan rigar shaddar da ya cire, miƙo min ita ta window in ƙarasa babbake ta, in ya so sai ki ara masa riga da zani na atamfa tun da neman aron zani yake" Da sauri ya kalli igiya ya ga rigar tana nan a rataye. Bai ce komai ba domin shi kaɗai ya san irin haushin da yake ji a kan Kuluwa baki ba zai misalta ba.

Wayarsa da take ta neman ɗauki Haule ta tafi ta ɗakko tare da hularsa da Hudu ya take ta lotse, ta haɗo kan takalmansa, wayar ta miƙo masa ya karɓa ya kalli sunan Hadiza ne ɓaro -ɓaro a jiki ya rasa ma ya zai yi Hudu ya ce

"Ka É—aga wayar mana, wai ni yaushe ka zama matsoraci ne wai? A ce kana tsoron mace haba abokina" Malam Nura kamar zai yi kuka ya ce

"Baka san so ba ne Hudu, so ne ya mini raga-raga da zuciya ni ban san ma akwai so ba sai wannan karon, ni dai na san masoyina kuÉ—i amma ban san ana son É—an adam ba... Hudu ya ce

"Taɓɗi ai daman idan mutum ya ƙi sharar masallaci ta kasuwa yake yi, yanzu ai ga ta inda jarabawarka ta fito, idan ka saki mata ba har kuka suke ba ka mayar da su saboda suna sonka amma ka ce musu son banza... Kiran da ya shigo ne ya datse maganar haka ya yi ta maza ya ɗaga yana ɗauka ta balbale shi da masifa kamar uwarsa ta ce

"Nura ni za ka wulaƙanta a idon duniya? Tun ɗazu lokacin ɗaura aurenmu ya cika, amma dai baka duba lokaci ko? Tun daɗewa sha ɗayan ta wuce yanzu Babana ne ya ƙara awa ɗaya ɗaya, idan har awa ɗaya ta cika akwai mazan da zan sa su hau layi duk wanda na ga wankansa ya mini shi zan zaɓa...

Sai da ya gyara muryarsa ya ce

"Haba masoyiyata gani nan fa ai kaf garin nan babu wanda zai kai ni ɗaukan wanka, in kin ga yadda shaddar nan ta karɓe ni zaki yi mamaki su Hudu ma sai yabawa suke, abin da ya tsayarmu abinci ne da naman da aka dafa na ɗaurin aure ake zubawa a kwanuka za a raba in mun dawo, shi ne ya tsayar da mu amma gamu nan" Hudu da yake jin ƙaryar da Malam Nura yake shararawa ya kalli kan murhu ya hangi wata tukunya ce da alama ma ruwa ne kawai yake dahuwa babu wata alamar za a yi girki barw har a samu nama, shi da ya tambaye shi mai za a ba abokai ma cewa ya yi daga wajen ɗaurin aure kowa ya kama gabansa shi babu kuɗin da zai kashe, ya maido da dubansa zuwa jikinsa da babu kaya sai ƙonan nan gajeran wando, shi da wandon ma babu wanda zai saka amma yana batun wai ya yi kyau.

Hadiza daga ɗaya ɓangaren ta ce

"Yawwa nawan, ai shi ya sa ina nan ina faɗawa ƙawaye da ƴan uwa cewar su jirayi zuwanka, domin kowa idan ya ce mini kin yi kyau sai na ce masa ai iri ɗaya muka ɗinka da angon shi har ya fini yin kyau ma" Hudu da Haule da Kuluwa duk sun jin abin da take cewa kasancewar a handsfree wayar take, kamar zai yi kuka ya juya ya kalli rigar shaddar ya daure ya ce

"Abin ba a cewa komai sai ma kin ganni hula ta zauna daram" Haule ta yi saurin kallon hularsa da karin da aka mata ma ya ɓaci saboda taka hular da Hudu ya yi.

Hadiza ta ce

"Shi ya sa nake son miji kerewa sa,a shi ya sa ɗazu da aka ce baban su Zainaba ya zo ya ce in yarda a ɗaura da shi... Gaban Malam Nura ne ya buga da ƙarfi, inda Kuluwa ta carara guɗa. Malam Nura da sauri ya ce

"Ki ce ba za a É—aura da shi ba" Ta yi karaf ta ce

"Ina ni ai sai sabon aure da Nurana, wai burgar kuÉ—i zai yi wa mutane bai san ba cewar kuÉ—i suna wajenka in na aureka ma babu abin da zan rasa gidanka ma sai ya fi nashi sau dubu" Yana gyaÉ—a kai kamar tana ganinsa ya ce

"Shakka babu gamu na zuwa" Kafin ta amsa tashin hankali ya sa Malam Nura katse kiran da sauri ya juya yana kallon Haule ya ce

"Haule dan Allah ki samo mini hayar zanin shadda ko nawa ne kuɗin hayar zan biya, ko siket ne ma, in dai za a samu kalar shadda ta wacce bata ji jiki ba, ko zanen ba ɗaya ba ne, ki samo mini, bari na saka wuƙa na yanka miki gefen wandon nan da Kuluwa ta yi wa lahani, ki tafi da shi ki nuna musu kalar shaddar ko Allah zai taimakeni a samu, a yadda nake jin Hadiza ta ɗauki lamarin saka shaddar nan ta kai shi ƙololuwa, ga hoton nan da take ta ambata idan har babu shaddar nan tana iya fasa auren, gwara ki samo zanin in tsargashi da reza ya yi kamar wando in ɗinke da zare da allura ya fiye mini" Haule da Hudu kawai dariya suka ƙyalƙyale da ita ganin yau ɗaya Malan ya zama kamar wani sauna a kan mace

Malam Nura kuwa harara yake aika musu, a inda Haule ta yi É—iff kawai sai ji suka yi Kuluwa ta carara guÉ—a ta ce

"Duniya juyi -juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi" Wannan kalaman ya yi wa Malam ciwo, hakan ya sa ya ƙara ƙudurtar duk lokacin da ya kama Kuluwa mai ƙwatar ta sai Allah.

Hudu ne ya ce

"Yanzu ka bar batub hayar zani ko siket, don ba samu za a yi ba, bari na je gida a cikin kayana na samo maka wanda za ka samu ka saka mu tafi É—aurin auren nan" BuÉ—ar bakin Malam Nura ya ce

"Akwai sabbi dal wanda baka taɓa sakawa ba?" Yana masa wani kallo cike da gatse ya ce

"A,a akwai sabbi wanda na kawo daga kasuwa yanzu" Malam Nura ya ce

"Ka san dai ai ba zan saka tsoho na je wajen É—aurin auren Hadiza ba"

Hudu ya ce

"Idan ka je da shi a koro ka"

Malam Nura ya ce

"Da in saka tsohon kaya gwara a samo mini aro a wajen wanki da guga"

Hudu ya ce

"Wallahi ka sake ka karɓi kayan wanjen ƴan wanki da guga, za a tsinka ka a wajen ɗaurin aure, wajen ɗaurin aure ai wajen taron jama,a ne ka sani ko mai kaya ya je wurin? Ai wanda kake ara ma saboda hira kake zuwa da daddare shi ya sa asirinka yake rufuwa" Hannu ya sa yana dafe fuska don takaicin Kuluwa ne kawai yake shaƙa.

Haka Hudun ya lallaɓa shi ya tafi gida ya samo masa kayan, Hudun yana kuyawa Malam Nura ya bi bayansa da kallo yana ganin kayan jikinsa saboda kyaun da Hudun ya yi shi tsoronsa ma ɗaya kar abokin ango ya fi ango kyau.

Hudu yana fita ran Malam ya ɓaci ganin ya kashe kuɗi amma zai ƙare a kayan aro, kuma tsohon kaya, a zuciye ya yi wurgi da taɓaryar hannunsa ya fara tafiya da baya-da baya sai kuma ya tafi da gudu ya yi tsalle ya doka ƙofar ɗakin Kuluwa cikin sa,a ƙofar ta ɓalle don ta ya bugu. Kuluwa da take cikin nishaɗi babu zato da tsammani ta ji ya bugo sai ta ga wayam ƙofa ta buɗe, idanu ta zaro domin har ta fara hango tsayawar alƙiyamarta.

Malam Nura wanda ya buga ƙofar jirif ya faɗi a reran saboda tsallan da ya yi amma bai ji ciwon faɗuwar ba saboda ya ga kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Kuluwa ganin ya faɗi ta fara ƙoƙarin tserewa don ta tabbatar ya kamata kashin ta ya bushe sai dai idan tana da sauran kwana ne za ta kai labari, a kiɗime ta kai kallon ta kan ƙafafunta da ya ce zai sare, da gudu ta taho, bai ankara ba ya ji ta taka cinyarsa, ya ji saukar ƙafarta a ƙirjinsa yana ƙoƙari tashi daga kwancen ya ga wulgawarta ta samansa fittt kamar walƙiya. A sukwane ya muskuta, cikin sa,a ya cafko ƙafarta ɗaya, jan ciki ya yi ya janyo addarsa. Kuluwa wacce nufinta ta fice daga gidan amma a lokacin da take dab da cim ma nasara sai ji ta yi an riƙe mata ƙafa ɗaya da ƙarfi irin riƙon da ba za ta iya ƙwacewa ba.
Chapter 13 · 0% Book details