Sashe 15
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka ce yau zan yi kwalli, don kafin ka ƙarasa wajen ɗaurin auren ka fara zuwa mu ga juna" Ƙulululuuuu cikinsa ya bada wani sauti don ya san tana son ɓallo masa ruwa ne, matuƙar ta ganshi da kayan nan ya san sai dai wani angon amma ba shi ba.
Yana ƙirƙirar dariyar yake tamkar wani sabon mahaukaci ya ce
"Haba Hadizatuwata, ni yanzu duk na matsu in ga an ɗaure mu da igiyoyin nan guda uku ki jira ni idan aka ɗaura sai in zo yau sai kin gaji da ganina don kanki" Ya faɗa yana aikawa Hudu harara wanda yake ƙunshe dariyarsa.
Ta yi ɗan shiru, Malam Nura yana ta addu,ar ka ta ƙi amincewa ko kuma ya masa masifar nan tata, kamar daga sama ya ji ta ce
"To shikenan sai an ɗaura ɗin ka zo, mai hoton ma yana nan yana yi a cikin gidan amma ni na ƙi yi na fi so sai mun yi tare kar kwalliyata ta ƙoƙe" Yana godewa Allah a zuciyarsa da cin nasarar da ya yi ya ce
"Yawwa haka nake so, ai ana shafa fatiha zan garzayo nan" Ya faÉ—a yana sauke ajiyar zuciya ya san dai duk tsiya in aka É—aura aure ba za ta ce a warware ba, ko ta ce sai ya sake ta ai dai ganin damarsa ne tun da sakin a hannunsa yake.
Yana yin wannan tunanin ya ji ta ce
"Ai ba zan jure ba, tahowa zan yi in tsaya ta windown gidanmu in hango ka, ka ga na yi kwalli kenan" Malam Nura wata wahalalliyar ajiyar zuciya ya sauke, jin wata lukutar masifar.
Bai gama tunani ba da ya ji ta sake cewa
"Dan Allah idan kun zo wucewa ka ɗago min hannu" Cike da ƙoƙarin danne damuwarsa ya amsa mata, amma a ransa yana raya cewa ba zai taɓa yin abin da ta ce ɗin ba saboda kar ta je ta ganshi komai ya caɓe.
Yana shirin datse kiran ta ce
"Ni yau duk kishin ka ma nake ba na so ake gani min kai, domin ko matanja ba don matanka ba ne da basu fara gane min kwalliyar ɗaurin aurena da kai ba" Dariya ya yi amma a zahiri ta ji sautin a baɗini kuwa dariyar yaƙe ce ya ce
"Daman na yaga buhu na rufa a kaina yadda babu kowacce mace za ta gane miki ni, ko wajen É—aurin auren sai na je da buhun rufe a kina" Dariya take sosai ta katse wayar bayan ta faÉ—a masa tana jiran wulgawarsa.
Tana katse wayar ya kalli Hudu bayan ya sanya hannu ya goge gumi, ya ciro hularsa ya shiga fifitawa a kansa da shi ma tuni ya jiƙe da gumin yana ƙasa da murya ya ce
"Hudu ina cikin talatainin masifa, Kuluwa ta cuceni, yanzu ga Hadiza can a windon gidansu in za mu wuce in É—ago mata hannu ta ga kwalliyata" Hudu ya bushe da dariya ganin gabaÉ—aya jama,ar fa suka taho tare kowa sabgar gabansa yake ya ce
"To mene ne abin tashin hankalin sai ka É—aga mata hannun ai" Harara ya aikawa Hudu bai sake cewa komai ba, har suka kusa shiga layin gidan su Hadiza gaban Malam Nura yana dakan lugude.
Tun da aka shiga layin ya kutsa tsakiyar mutanen da suke tafiya, ya dunƙufar da kansa yake kallon ƙasa, Hudu ne yake faɗa masa cewar ya hango ta tana leƙowa daga windown, suna zuwa Malam Nura ya nannaɗe hannun rigar jikinsa sai da ya kai wajen kafaɗa yadda ba za a hango kalar yadin jikinsa ba, yana ɗan sunkuyawa kamar mai ƙusumbi ya shiga ɗaga hannu saitin ƙofar gidan nasu, don shi dai kawai ɗaga hannu yake yana bye-bye yi yake babu ƙaƙƙautawa.
Hadiza wacce ta kira ƙawayenta guda biyu take shirga musu ƙaryar kuɗin shaddar da Malam Nura ya ɗinka musu ita da shi da yaranta, don dai da ta linka kuɗin ta faɗa musu, su kuma suka yarda suna fasa mata kai a kan cewar lallai ta tsinci dami a kala tun da dai gashi har ƴaƴanta ya yi ws kayan fitar biki ba su san cewar dai da aka kai ruwa rana ba ya ɗinka.
Tsaye suke sun zubawa hanyar ido har dai suka fara jiyo tashin kiɗa, Hadiza ta ji kanta ya fashe, ƙawayenta suka ci gaba da wasa ta, musamman da suka ga mutane sun shawo kwanar sai kiɗa ake ana wasa ango, kowa ya gyara tsayuwa don ganin angon Hadiza don ta ce musu ya fi tsohon mijinta komai, gashi da kuɗi kuma ba ya jin ciwon fitar da kuɗi, hakan ya sa suka sake ganin girmanta.
Tun da suka hango mazan suka zuba na mujiya, kasancewar ma su mazan da suka taho tawagar angon daga can tsallaken hanyar suke ba daga saitin inda gidan su Hadizar yake ba, wato daga tsallen dama suke tafiya, gidan su Hadiza daga ɓangaren hagun.
Ɗaya daga cikinsu har ɗaɗɗage take tana son hango angon, Hadiza tana hararta tana cewa za ta gane mata ango. Amma maimakon ango ya fito fili a ganshi tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu, sai ya ɓace a cikin mutane tamkar kifin da ya nutse a ruwa, hannunsa kawai ake hangowa, a haka yake tafiya a dudduƙe tsoronsa ɗaya ma kar ya yi tuntuɓe ya je ya faɗi a shiga uku don idan ya faɗi ya san dole Hadiza ta ganshi don daga ya faɗi za a fara cewa ango ya faɗi dole a ganshi kuwa. Hudu ztsabar dariya har da hawaye, mutane kuwa babu wanda ya lura da abin da yake faruwa.
Ƙawayen Hadiza ne suka ce
"Kin ce mu zo mu ga ango zai É—ago hannu, amma mu babu wani ango da muka gani bare mu ga kwalliyarsa, kawai iya wancan hannun da ake É—ago daga cikin jama,a tamkar shamuwa tana É—aga fiffike shi kaÉ—ai muke gani"
ÆŠayar ta ce
"Ni hannun ma kamar wanda ya ji uwar wuya, duk kawai kamar dai ana rauda hannun ne ba wai ana É—agoshi ba"
ÆŠayar ta ce
"Ni fa yadda ta ce ya saka shadda irin tata kawai zatona zan hango haɗaɗɗan hannu ake hango shadda a jikin hannun, amma wannan babu abin da ake gani na shaddar fa, kawai sangalalin hannun ne ake gani tamkar wanda singileti ce sanye a jikin mai ɗago hannnun babu kaya" Ran Hadiza ne ya ɓaci da tsiyar da suke mata ta fara tunanin ko dai sun ɗauka ma ƙarya take bai ɗinka musu tare da ganin hakan ya sa a zuciye ta ce
"Wallahi duk cikin ku kun san na fi ƙarfin in muku ƙarya, idan har ba shi ya saya mana ba babu dalilin da zan sa in ce shi ya saya, kuma har shi ya siyo ya ɗinka, amma tun da har kuka musa bari na kira shi ya fito gefe guda daga cikin ayar mutanen, ku hango shi" Ta faɗa tana doka masa waya.
Malam Nura da ya kusa tsallake rijiya da baya wato gani yake an kusa wuce saitin gidan su Hadiza ya huta da wannan jarabar ta ɗaga hannu, ya san dai idan an je an ɗaura aure in ta ganshi kowacce jaraba za ta yi sai dai ta yi tun da an ɗaura. Amma me yana cikin wannan halin wayarsa ta fara neman ɗauki, saboda tsoron abin da zia biyo baya ƙin ɗagawa ya yi da ya ga sunan Hadiza hannunsa ne kawai yake karkarwa domin hatta hularsa da ya cire yakw riƙe da ita a ɗaya hannun neman suɓucewa take amma har lokacin bai daina ɗaga hannun ba.
Hudu ne ya kalle shi ya ce
"Dan Allah ka daina É—aga hannun nan, kamar wani mai É—aga tutar nigeri,a"
Malam Nura ya ce
"Wallahi wanda yake É—aga tutar ma ya fini Æ´anci nidai wanna aure na Hadiza ya wahalar da ni" Hudu ko tausaya masa bai yi ba ya shiga masa dariya don shi kaÉ—ai ya san waye abokinsa da irin tsiyar da ya shuka, ya san yanzu kawai abin da ya shuka ne bai ma fara girba ba.
Ran Hadiza ne ya ɓaci ganin ɗaga daga cikin ƙawayen nata ta yi tsaki ta ce
"Ƙaryar banza" Tana faɗar hakan ta tafi, ɗagar ta tsaya tana mata dariya, Hadiza tana kallon aminiyar tata ta ce
"Kema Bintu baki yarda da ni ba?" Bintu tana dariya ta ce.
"Ina fa zan yarda sai na ganshi ido da ido, wannan mazan na yanzu masu shegen son kuɗin tsiya har zai tsaya kashe miki kuɗi a kayan fitar biki ke da shi da ƴaƴan da ba ma nashi ba, bayan kuɗin da kika ce ya baki" Ƙwafa Hadiza ta yi ta bar wajen cike da haushin Malam Nura da bai ɗauki waya ba, tana saƙawa a ranta cewar zai zo ya same ta.
Sai da ya ga sun gota wajen yadda ba za a iya gane shi ba tun da sun É—an yi nisa ya É—ago yana sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ce
."Haba ina dalili gabaɗaya wuyana ya ƙage a sunkuyon nan, hannuna ma da nake ɗagawa haka" Ya faɗa yana mayar da hularsa ya ɗora a kansa ya danna ta sai kuwa ya zama kamar wani maroƙi!.
A haka suka ƙarasa wajen da aka tanada don ɗaura auren, Malam Nura yana ta sauke ajiyar zuciya, ana ta kaɗe-kaɗe har dai aka saurara aka yi abin da aka taru dominsa, wato aka ƙulla aure tsakanin Hadiza da Malam Nura!. Maroƙa suna ta cewa
...."Aure ya É—auru, Allah bada zaman lafiya"
Malam Nura ya ce
"Hudu babu pure water a nan wajen ne?" Ya faÉ—a yana waige-waige.
Hudu ya ce
"Mai za ka yi da pure water?"
Malam ya ce
"A ƙasa zan zuba in tsotse, wallahi ƙirjina tun da na fito daga gida kamar ana bubbuga kalangu, har sai yanzu da auren nan ya ɗauru duk da har yanzu ina jin tamkar mafarki ne" Tsaki Hudu ya yi ya shiga gaisawa da jama,ar da suke musu Allah sanya alkairi, bakin Malam Nura har kunne yana ta washe bakin murna.