Sashe 7
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ÆŠaki ta shiga ya bi bayanta, rigarta da zani na kan gado da ta ajiye ta É—auka ta saka, yana zaune a bakin gadon yana mata daÉ—in baki, ta É—auki mayafi ta yafa kasancewar ko drower kayanta bata buÉ—e ba shi ya sa bata san ya kwashi kayan ta ba.
Sai washe baki take suka fito ta rufe É—akinta, shi ma ya rufe nashi É—akin suka fita ko sallama ba su yi wa Haule ba, Kuluwa jin ta take a sama don miji yana yayin ta.
A jere suke suna tafiya sun kama hanyar gidansu Kuluwar, suna tafiya suna hira Kuluwa ta ce
"Nurana na kaina"
A fili ya ce
"Ke kaÉ—ai kuwa"
A zuciya ya ce
'Sakarya za ki gani shayi ruwa ne, banbancin suga ne kawai da lipton'
Tana washe baki haÉ—e da kafe shi da ido ta ce
"Haulen fa?" Hararar wasa ya mata ya ce
"Ke wai sai kike maganar gawa shin gawa tana da amfani bayan san cire mata rai?" Ta yi shiru don bata gane ba ta ce
"Gawa dai kake nufi" Haushi ya kama shi don Haule ta fita saurin gane zance ita kamar kidahuma sai an mata ɓaro -ɓaro.
Cike da ƙosawa ya ce
"Ina nufin ita bata da amfani ne a gidan" Ta ƙyalƙyale da dariya har wasu ƴanmata guda uku da za su wuce ta kusa da su suka bita da kallo.
A sake kallonsa ta ce
"Hadizar fa?"
Ya yi tsaki irin na gajiyawa da maganr wasu matan da take masa ya ce
"Na ce Haule ma bata da amfani bare wata Hadiza da bata zama matata ba"
Allah ne kaÉ—ai ya san daÉ—in da take ji a ranta ta washe baki ta ce
"Zan iya zaginta baka ji komai ba?" Kafin ta yi zagin shi ya fara kama sunan Hadizar ya zaga yana faÉ—in
"Ƙarewa ma ai kin ji na zage ta da kaina, ni fa bana ganin kowa sai ke"
A zuciya ya ce
'In dai zan ci amarci bakya gidan nan gwara ko me zan yi in faɗa ' Ƙaran wayarsa ce ta katse musu maganar ya dakata da tafiya bayan ya fito da wayar daga aljihu ya ga sunan Hadizar ya ce
"Hudu ne yake kirana" Ya faɗa yana ja gefe ya ɗaga wayar haɗe da ƙasa da murya ya ce
"Amarya bakya laifi ko kin kashe É—an masu gida, amarya mai maganar zuma" Bata amsa masa ba ta ce
"Maganar kayan da zan yj fitar biki ne, na ga yau baka zo ba yau na so mu yi maganar, ka ga lokaci yana wucewa saboda É—inki ga kuma su Zainaba ba kai kuma uban nasu baka ce komai ba kan kayan namu" Shiru ya yi kansa yana juyawa shi ya ma rasa abin faÉ—a, abu na farko yana tunanin shi da ya cake kuÉ—i ya bata dubu É—ari biyu bayan kaf kauyen nasu dubu É—ari biyu da hamsin ne kuÉ—in budurwa ma bazawara dubu É—ari amma ta matsa masa ya bata dubu É—ari biyu kuma yanzu take masa maganar kayan fitar biki? Har tana ambaton wasu agololi shi ina ruwansa da kayan da Æ´aÆ´anta za su saka shi da burinsa bai wuce a É—aura aure ya É—auke ta ta koma gidansa ya daina ganin Æ´aÆ´an nata ba don ko gidansa ba zai ke basu fuskar suke masa difdiftu ba.
Sai da ta sake magana ya dawo hankalinsa ya ce
"Yanzu ina gidan Baba Ramma muna magana zan kira ki in na koma gida" Ta amsa masa tana yanke kiran, ya kara wayar ya taho yana É—aga murya yana cewa
"Haba kaima Hudu na faɗa maka ni da rabin raina ne Kuluwa za mu je gidansu mu gaishe da su, to sai na dawo ma ƙarasa" Kuluwa sai wani washe baki take, haka ya ƙaraso suka ci gaba da tafiya tana masa magana ta ji ya ce
"To kayan uban me zan saya kuma" Kuluwa ta tambaye shi sai lokacin ya gane ɓaranɓaramar da ya yi, don ya gane maganar zuci ce ta fito fili ya ce
"A,a daman Hudu ne yake cewa na fasa sayan kayan amaryar na ce kayan uban me zan saya ni da na fasa auren" Dariya ta yi ta ce
"Ai ni so nake idan muka dawo daga gidanmu mu biya gidansu Hadizar nan a kira ta ta fito in zage ta tassss in faÉ—a mata daman bakin rijiya ba wajen wasa makaho ba ne, in ce a bi wani sarkin amma ba wannan ba" Gabansa ne ya faÉ—i amma da ya tuna cewa a gidansu zai barta shi kaÉ—ai zai dawo sai ya yi dariya ya ce
"Nima zan taya ki" Dariya suka yi su duka, lokacin sun ƙaraso gidansu Kuluwar.
Dakatar da ita ya yi ya ce
"Na saya klin da sabulai na wanka da wanki da za ki kai musu, bari na kira a kawo mana sai mu shiga da ƙwarin gwiwa" Sosai ta ji daɗi, wayarsa ya ɗauka ya kira wanda ya ba ƙullin kayan Kuluwa, ya ce ya kawo masa gidansu Kuluwa yana ƙofar gidan. Amsa masa ya yi da to gashi na zuwa.
Saboda ya san halinta matuƙar ta ga kayan ba lallai ta shiga gidan ba, hakan ya sa ya ce ta shiga gidan ta faɗa musu zai shigo, da murna ta shige gidan shi kuma a take ya kira Hudu abokinsa yana labarta masa maganar da Hadiza ta faɗa masa yana ta kumfar bakin cewa son samun ta ya yi yawa kar fa ta fara tunanin za ta wanki aljihunsa ne, Hudu yana ta bashi haƙuri domin ya bi komai a sannu haka ya kashe wayar ransa yana ƙuna ya tsani duk wani batu da za a yi na taɓa kuɗi amma ya ga Hadiza idanunta idon kuɗi.
Kashe wayar ya yi daidai da zuwan mai kawo kayan haka ya karɓa ya kutsa kai cikin gidan ya tsaya a zaure wani ƙaninta ya zo ya ce an ce ya shigo. Kuluwa tana zaune a kan tabarma kusa da mahaifiyarta mahaifinta yana kan tashi tabarmar yana sauraren rediyo sai ƙannenta mata guda biyu suna cin tuwo. Da sallama ta shigo aka amsa masa ana masa faram-faram mahaifinta zai iya cewa tun da aka ɗaura auren bai sake ido huɗu da Malam Nura a gidansa ba, sai dai su haɗu a hanya haka ma mahaifiyarta sai dai idan ta je gidansa amma yau gashi dan badangarci har cikin gida ya zo, kuma tare da ƴarsu wannan abin farinciki ne musamman da Kuluwar ta ƙyanƙyasa musu cewar klin da sabulai ya tsaya a wajen za a kawo masa wanda za a basu tsaraba, ta faɗawa mahaifiyarta hatta auren ma ya fasa, daɗi sosai uwar ta ji domin a tarihin aure-auren Nura kowa ya sani a ƙauyen Shabaru bai taɓa nemab aure ya fasa ba!.
Maimakon su ganshi da leda riƙi-riƙe sai suka ganshi da ƙullin kaya, ita dai mahaifiyar Kuluwa saboda son samu tunaninta ɗinkuna ne ya musu aka ɗauro a zani, amma Kuluwa da ta yi wa zanin da aka ɗaure kayan ƙuru tabbas ta gane kamar dai atamfarta!.
Malam Nura ya zauna a kan tabarmar da aka shimfiɗa masa daga gefe kusa da ta mahaifin Kuluwa duk da daman babu wani ganin girman juna tsakaninsu tun da akan biyan bashi suka yi ta ɗauki babu daɗi har dai ya bashi auren ƴarsa a kan hakan. Ƙullin ya ajiye a gabansa ya shiga gaishe da su suna amsawa, amma Kuluwa ta yi mutuwar tsaye sai dai hasashenta bai kai kan gaɓa ba, domin iya tunaninta bata taɓa kawo cewa zai ɗakko kayanta ya kawo ta gida ba, da a ce ta yi wannan tunanin da ta tabbatar cewa Malam Nura ba ƙaramin ɗan duniya ba ne, sannan da hankalin ta ya fahimtar da ita cewar maganganun da Haule take faɗa masa gaskiya ne sun ishe ta ɗaukan darasi sai dai ba haka ba ne, ranta ya kissima mata cewar ko dai ɗakkowa ya yi ya kawo a bayar zai ɗinka mata wasu, amma mai ya sa bata ga kayan ba sai yanzu, sannan ina ledar sabulan, wannan tambayoyin take ta yi a zuciyarta.
Mahaifin Kuluwa ne ya ja shi da zance yana tambayar Baba Ramma inda mahaifiyarta ta yi ƙasa da murya ta ce
"Kuluwa ko dai É—inkuna mijin naki ya iyo mana? Gaskiya yarinyar nan kin samu mazaunan zama a gidan miji" DaÉ—i ne ya kashe Kuluwa ta murmusa bata ce komai ba.
Sai da ya gama gaisawa ya kira ɗaya daga cikin ƙanen Kuluwar, tasowa ta yi ta zo wajensa su Kuluwa sai washe baki ake, ya ɗago ƙullin ya ce
"Mariya ungo wannan kayan yayarku ne ki kai mata ɗaki" ,Daga mahaifin Kuluwa har mahaifiyarta mutuwar zaune suka yi, Kuluwa kuwa zigidim ta tashi tsaye tana zaro ido bata san lokacin da magana ta suɓuce ta fito ba ta ce
"Kayana kuma? A kai min wane É—aki, mai zan yi a gida?" Ta shiga jero masa tambayoyin domin abin ya razana ta da yawa.
MAMAN AFRAHðŸ˜
09025576222
[4/8, 6:27 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Bu295Z6iGnL3SoKYtgqnbZ?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
🅿ï¸4ï¸âƒ£
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*
*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿ï¸4ï¸âƒ£
Malam Nura ya kalli Kuluwa sheƙeƙe ganin ta hayayyaƙo masa ya ce
"Zama za ki yi a gidan mana" Hankalin iyayenta ya tashi Babanta cike da hasala ya ce