← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ya kama hanyar zuwa gidansa yake jin farinciki don yana son ba marar ɗa kunya a wannan ƙarin auren da zai yi, musamman da Kuluwa take son hana shi rawar gaban hantsi tana son shige masa hanci da ƙudundune. Shi kuma bata san hakan ƙara rura masa wuta take ba tana ƙara zuga shi domin ya saka a ransa cewar zai yi abin da zai shallake mata tunani abib da bata zata ba, sai ya cusa mata takaici tun da shi bai saba idan zai yi ƙarin aure mace ta takura masa ba ko ta nuna rashin amincewar ko ta ɗaga masa hankali sai a kanta, don ita Haule in don ta ita ne duniya ta zauna lafiya.

Ko da ya ƙarasa gidan tsaye ya tarar da ita tamkar tana jiran dawowarsa. Yana sallama amma bata amsa ba sai Haule ce ta amsa masa daga cikin ɗaki. Zai wuce ta sha gabansa ya ƙara ratsewa ta sake shan gabansa a ƙufule ya ce

"Mene ne kuma?" Tana masa kallon raini ta ce

"Duk abin da ka zata shi ne, ko in ce duk abin da kake ji da shi ni ɗin ma shi nake ji" Kallon ta ya yi ya a ransa ya fara tunanin anya wannan za ta bari ya ci amarcin nan a kwanciyar hankali kuwa? Zuciyarsa ta fara raya masa cewa ko dai ya aikata gidansu amma ba da zummar saki ba, tun da ya saka a ransa ba zai sake ta ba sai ya gama amfanar kuɗinsa amma dai yanzu tun da tana son kawo masa cikas gwara ya ce ta tafi gidan, sai dai ya ƙudiri cewa ba zai dawo da ita ba sai bayan wata biyu wataƙila ma lokacin ya saki Hadiza ya fara neman wani auren.

Gyaran murya ya yi ya ce

"Kuluwa abin naki ya fara yawa, ke baki san mace mai kishi fita take daga zuciyar miji ba?" Ta kama ƙugu da hannu ɗaya tana jijjiga jiki ta ce

"To na nawa kuma? Ai na san wannan bazawarar da kake kira mai jiran gado ta daɗe da yin fatali da ƙaunata daga zuciyarka, shi ya sa baka ganin kaina da gashi"

Haule da ta fito daga É—aki ta mata kallon É—aya saura kwata ta ce

"Kuluwa ya kamata ki wa kanki faɗa, ki yi karatun ta nutsu, shi mijin da ya damu da kai shi kake kishi a kanka, kuma wa ya ce miki akwai ɓurɓushin ƙaunarki a zuciyar Malam da har kike ikirarin wata ta tunkuɗe son naki, idan baki sani ba in faɗaa miki, daga lokacin da mace ta sako ƙafarta a cikin gidan Malam Nura daga ranar duk wata ƙaunarta take bankwana daga zuciyarsa shi ya sa zaman ba ya iya zuwa ko ina ake rabuwa domin daga ya hango wata zancen ta cikin gida ya ƙare amma kin ɗauki kishi kin hana rai da zuciyarki sakat ki kafa faɗin wai mai jiran gado shin ke idan ta jira gadon sai me? Kafin ta jira gadon mata nawa ne suka jira dan Allah ki sauƙaƙawa kan ki amma shawara....

Cike da masifa da kallon raini ta ce

"Haule ki kama girmanki idan ke bakya son Malam ni ina son shi, dan haka babu ruwanki da ni ki riƙe shawarar ki"

Haule tana kwashe kayan shanya ta ce

"Allah baki haƙuri" Daga haka ta kama kanta bata ƙara cewa komai ba ta ci gaba da sabgar gabanta.

Malam Nura ya ce

"Matsa in wuce" Ta yi ƙememe ko gizau bata yi ba. Hannu ya sanya ƙiii ya yi gefe da ita, da fisge ta sake shan gabansa cike da ƙosawa ya ce

"Mai kike so ne wai?"

A zuciyarta tunaninta masifar da ta addabe shi da ita ce ta yi tasiri dan haka ta sake tamke rai ta ce

"So nake ka fasa auren wannan amaryar taka" Baki sake yake kallonta sai kuma ya fashe da dariya ya ce

"Tambaya É—aya zan miki idan bar kin amsa to"

Ta ce

"Ina jinka"

Ya ce

"Kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo?" Tana masa kallon rashin fahimta ta ce

"Ban gane ba"

Ya ce

"Idan har wanda ya mutu yana dawowa to haka za a fasa auren" Kallon ƙurilla ta masa don ta san kawai raina mata wayo ya yi hakan ya sa ta ce

"Mai kake nufi?"

Ya ce

"Ba zai taɓa iyuwa ba ke ni da a ce auren nan an fasa to gwara aurenki da ni ya mutu" Yana faɗar haka ya juya zai tafi ta kamo rigarsa daga baya ta janyo shi ƙiiii tamkar wanda daman tigar tasa take jiran a ja haka ta shiga yagewa domin daman kayan sun ga yau sun ga jiya sun gaji fa shiga ruwa. A ƙufule ya juyo ya kai mata mari ta sunkuye ya mari iska yana zare ido ya ce

"Kama hanya ki tafi gidanku" Gabanta yana bugun uku-uku ta zaro ido don tunanin ta sakin ta ya yi hakan ya sa ta ce

"Ban gane in tafi gidanmu ba"

Cike da É—aga murya ya ce

"Eh ki tafi sai na neme ki"

Ɗan sanyi ta ji a ranta a ƙalla ba sakin ta ya yi ba.

Cike da cika baki ta ce

"Ai da ba a kawo ni gidanka ba sai da aka É—aura mana igiyoyi uku dan haka yanzu idan baka warware ba babu inda zan je"

Faɗa aka shiga zabgawa ita da shi amma ta ƙi tafi shi kuma so yake ta tafi ko ya sake idan amarya ta zo don ya lura lamarin Kuluwa babu sauƙi wai ciwon arne.

Kiran Hadiza ya yi a waya ya ce yau ba zai samu zuwa ba, dan haka ta ce ya aiko a kawo mata kuɗin kari, haka ya ba wani dubu biyu ya kai mata, shi kuma ya ƙuduri aniyar kai Kuluwa gidansu tun da ita ta ƙi tafiya, ya kore ta amma ta ƙi saboda naci.

Tana banɗaki ya je ɗakinta ya ɗakko kaya kala goma ya kai ɗakinsa ya zuba a zani ɗaya ya ƙulle, ya fita ya ba wani saurayi yw ce ya ajiye masa zai kira shi, haka ya karɓi kayan shi kuma ya dawo gida.

ÆŠakinsa ya shiga sai da ya ji fitowar ta daga banÉ—akin ya fito, yana fitowa ya washe baki ya ce

"Ina gwanar wani ga tawa, Kuluwa ta Malam Nura bada kanki a sarw ki je gida ki ce ya faɗi, ni da ke amana ce babu rabuwa kowace mace sawu take, take miki" Kuluwa tana dab da shiga ɗakinta ta fara jin wannan batu hakan ya sa ta dakata tare da saurin jiyowa don ganewa idanunta. Rass idanunta suka yi tozali da Malam Nura har ta shuga ƙarewa tsakar gidan kallo tunanin ta ko da wata yake, sai dai ambaton sunanta da ya yi a maganar hakan ya bata tabbacin da ita yake. Wani irin washe baki ta yi tana tunano cewar ɗazu da ta yi salaar magriba ta yi ta addu,ar Allah sa ya fasa auren Hadiza Allah sa ya daina ganin kowace mace sai ita, hakan ya sa ta fara tunanin tabbas addu,ar da ta yi ce ta karɓu.

Haule tana jin su a ɗaki ita da su Kabiru duk da yaran suna hayaniya amma hakan bai hana ta jin abin da Malam ya faɗa ba, sai dai hausawa suka ce sanin hali ya fi sanin kama, shi ya sa aka ce duk daren daɗewa idan ka daɗe baka tare da mutum to ka tambayi komai nasa amma ban da hali domin halinsa yana nan shi hali zanen dutse ne!. Ta san halinsa kamar yunwar cikin ta, kuma ta san ruwa ba ya tsami banza, dole akwai wata maƙarƙashiyar da yake shiryawa Kuluwar amma da yake idanunta a rufe suke ba za ta gane waye Malam Nura ba, shi ya sa har yau tana fata da kuma jiran ranar da Allah zai fitar da haƙƙin matan da yake kansa wanda ya ɗauka tun da ta san matuƙar ana kwana ana tashi zai auro daidai da shi wacce za ta zame masa ƙarfen ƙafa ta ganar da shi shayi ruwa ne!.
Kuluwa ta wani gyara tsayuwa haɗe da gyara ɗaurin ƙirjin da yake jikinta, daman ruwa ta watsa tana ƴar dariya ta zumbura baki ta ce

"Kamar gaske" Danne dariyarsa yake don ya lura har ta bada kai bori zai hau, hakan ya sa ya ce

"To da wasa ne?"

Tana kallonsa don yanzu ta fara takowa zuwa gare ta ta.ce

"Ai ka ce babu kowace mace a gabana amaryar taka mai jiran gado fa?"

Ya ƙyalƙyale da dariya irin ta ƴan duniya ya ce

"Rabu da ita ai da tsohuwar zuma ake magani, ai ni yau babu abin da zai sa ma in je wajenta hira, kin san dai tun da na fara neman auren na kullum sai na je hira ko? To yau ba zan je ba yau ranar ki ce, kuma ina miki albishir da cewa maganar auren ma janyewa zan yi" Ta masa tsuru da ido sai dai da ta tuna cewa addu,a ta yi kuma babu abin da ya gagari ubangiji sai ta yarda da maganarsa.

Ganin hakan ya É—ora da faÉ—in

"Yau gidanku za mu je mu gaishe da babanku sannan mu je duk inda kike so a tare daga haka mu dawo gida" Kanta ne ta ji ya yi wani gingirim ta fara tuno irin tsiyar da za ta shuka hakan ya sa ta ce

"Yau fa bakin girkin Haule ne"
Sai da ya ɗan kalli ɗakin Haulen ya yatsina fuska lokacin Haulen ta taso ta leƙo ta window inda ta ɗaga labule ya taɓe baki ya ce

"Rabu da ita, kin manta daman na ce bakin girki kawai za kuke yi sannan ma ita fa babu ruwanta, to ma ya za a yi ta haɗa kanta da ke, ai ke ce ta gaban goshi" Bakin ta har kunne ta washe, Haule ta saki labulen tana danne dariyarta don ta san wata tsiyar zai shuka amma da yake ita Kuluwa dukan iska ce har yau bata gane inda ya saka gaba ba, bata taɓa tantance waye namiji sai ya shuka mata tsiyar ta zo tana tagumi da balbalin bala,i.
Chapter 6 · 0% Book details