← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fisgar ƙafar ta yi, amma ta kasa ƙwatar kanta, jan ƙafar ta yi da ƙarfi ta zube ta fara rarrafawa da ƙarfin ta na gaske, ƙiii ta fara janyo Malan da addarsa, ganin tana neman kufce masa ya yi ta maza ya miƙe zaune, har lokacin yana riƙe da ƙafarta, wani uban ihu ta saka tana faɗin

"Jama,a ku taimakeni ƙafata, Haule kirawo jama,a a awaje su kawo ɗauki" Malam ya ce

"Ai ba ƙafarki ba yau hatfa wuyanki yankan saniya zan miki kamar yadda kika raba wandon ɗaurin auren Hadiza da ƙafafunsa ta ƙarfi da yaji" Haule ta hau faɗin
"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un Malam kar ka yi haka" Ta faɗa ba tare da jiran komai ba ta yi hanyar wajen, har lokacin mutane suna nan hango Hudu ta yi da ya kama hanyar gidansa ta tura wani yawo ya bi shi da gudu ya taɓo mata shi, ta ɗaga masa hannu, da ɗan gudu ya taho, tun kafin ya ƙaraso ta juya da sauri ta shige gidan, yana shigowa karaɗin Kuluwa ta fara masa sallama a kunne.

Yana shigowa ya hau ƙoƙarin ceton ta don Malam ya fara saita ƙafar, a kwance suka same ta tana fisge-fisge ya haɗe ƙafafun ta waje guda da alama sare su zai yi da gaske. Hudu ya shigo da gudu yana faɗin

"Kar ka yi haka Nura mene ne hakan" Yana zare ido yana faÉ—in

"Ka barni na gurgunta ta, daga yau ba za ta sake wa wani haka ba" Hudu ya tafi bayansa ya shiga janshi, suka shiga kokawa, ai kuwa Kuluwa ta samu sa,ar ƙwace riƙon da ya mata, tana tashi ta zabga da gudu ta ƙanƙame Haule, Malam Nura ya fishe riƙon da Hudu ya masa, ya nufo wajen Kuluwa da Haule, Kuluwa da gudu ta saki Haule ta yi wajen Hudu, a rikice ta kai masa cafka za ta ƙanƙame shi.

Haule ta dage ƙarfin ta faɗi take

"Kuluwa Hudu ne ba ni ba ce, Kuluwa kar ki rungumi na miji ba muharraminki ba ne" Amma Kuluwa bata ma fahimtar abin da Haule take faÉ—a ta ga mutuwa muraran. Hudu ganin ta taho za ta cakume shi ya sunkuya, yana faÉ—in

"Kuluwa alharam giya a gidan liman.

Shigowar wasu mata kusan guda bakwai shi ya dakatar da kowa da abin da yake da wata maroƙiya tana faɗin

"Gamu mun zo cin arziƙi, unguwa ta cika, ɓangaren mata ma yana can ya cika ana ta hidima ango kawai ake jira a ɗaura aure" Malam Nura da sauri ya warci rigarsa siyam siyam ya wuce ɗaki babu wanda ya lura da shi cikin mutanen da suka shigo. Wata nannauyar ajiyar zuciya Kuluwa ta sauke gani ta tsallake rijiya da baya. Haule ta hau yi wa matan sannu da zuwa.

Kuluwa ta fara neman takalmin ta za ta tafi gida, amma shigowar ƙannenta su Mariya ya hana ta tafiya ta wayince tana musu yaƙe, nan ta shiga faɗa musu abin da yake faruwa bayan fitar Hudu. Suka shiga zuga ta a kan ta murje idanunta tw zauna duk kurin banza ne babu abin da zai iya mata kawai burga ce amma ba zai cire mata ƙafafu ba tun da ya san shi ma sai an ɗauki fansar abin da ya yi, da wannan ta ɗan saki ranta.

Hudu ya dawo da wani yadi a goge tass a kawowa Malam ya ce ya saka don ya jima ma bai saka ba, ba lallai a gane cewar na Hudun ba ne amma dai ana iya ganin ba sabo ba ne. Haka ya saka ransa duk ba daɗi ya wanko ƙafafunsa da suka sha ƙasa ya shafa mai ya saka hula da turare suka fito da Hudu. Hudun ne yake raɗa masa a kan ya saki ransa saboda kar hankalin jama,a ya koma kansa. Haka ya shiga washe baki yana yaƙe duk da fargabarsa haɗuwarsa da Hadiza ne, yana tsoron ta gan shi da wannan kayana ta ce masa ta fasa, gashi ma ba ya jin ko ta yarda an ɗaura za ta amince a ta yi hoto da shi.

Hadiza tun suka gama waya da Malam Nura take jin wani daɗi a ranta saboda ta san zai zo da kwalliyar kece rainin da kowa ya ganshi ya san bata yi zaɓen tumun dare ba, shi ya sa ma za ta saka su yi hoto ta kafe a ɗaki ta ko da baya nan ta yi baƙi za su ga miji na nunawa sa,a ta aura ɗan gayu mai saka kaya masu tsada.Shi ya sa ma ta yi gyara na musamman Hadiza ta yi amfani da Packages na bazawara wanda na musamman ne ƙawarta ta kawo aiko mata, da kuma cicciɓin garari, tightening set wanda yake haɗe mace, ga wani sanyi fllusher da yake wanko gabaɗaya sanyin mara, sanyin mahaifa, da sanyin jijiya, Hadiza gyaran da ta yi ita kaɗai ta san Malam Nura zai san ya yi sabon aure ba lallai ya bambance cewa ba bazawara ya aura ba saboda ta dawo tamkar sabuwar budurwa, duk abubuwan nan za a same su a wajen surayya halin yau ta wannan lambar 08032773332
[4/12, 7:04 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA*

🅿️7️⃣

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*

*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*

*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*

*UWAR AGOLA*

NA

MAMAN AFRAH

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222

🅿️7️⃣

Hudu ne a gaba lokacin da za su fito daga cikin gidan Malam yana biye da shi, gabaɗaya idanunsa kafe a jikin kayan Hudu ba don kar Hudu ya ce bashi da godiyar Allah ba, kuma bai gode ƙoƙarinsa ba kawo masa yadin da ya yi ba da sai ya ce ya tuɓe kayan jikinsa ya bashi ya saka, don ya hango tsantsae tazara mai yawa tsakanin kyan da ya yi da kuma kyan da Hudun ya yi. A zahiri ma dai sai dai a ce kyan da Hudu ya yi amma Malam Nura ba za a ce ya yi kyau ba za dai a kira abin da ya yi da suna, ba yabo ba fallasa.

Suna fitowa ƙofar gidan inda jama,a suke jiransu, saboda Malam ya yi gayya sosai, ga kuma wanda Hudu ma ya gayyato, tun da ya ga Malam yana ji da auren nan nasa da Hadiza.

Kunya ce ta kama Malam Nura ganin duk kamar ma ido ba ya kansa, sai hannu ake ba Hudu ana gaisawa da shi, sai sun fara bashi hannu sannan ake ba Malam, wannan wai wanda ma suka san shi ne angon bare baƙi kamar makaɗa da maroƙa da suke ta wasa Malam Nura amma kuma Hudu suke kallo alamu sun nuna cewa sun ɗauka shi ne angon. Hudu ganin wannan kara da ake musu ya sanya hannu a aljihu ya ciro yan naira ashirin sabbi yake liƙawa maroƙan kamar wanda suke jira suka shiga ƙara ƙaimi wajen ƙarawa kiɗan nasu da wasawar armashi, shi kuma sai gyaɗa kai yake alamar yana taya Malam Nura farinciki. Malam Nura da bai fito da ko sisi ba, takaici ya hana shi magana sai hannu yake sakawa a kai- a kai yana gyara zaman hularsa, wacce tun lotsewar da ta yi lokacin da Hudu ya bi ta kanta bata dawo daidai ba sai yake jin kamar an kifa masa kwano a kan. Wato ta ƙi zama daidai.

Kabiru da Lawwali Æ´aÆ´an Malam Nura ne suke musu da wasu yara abokansu wanda musun ya sauka a kunnen Malam Nura inda abokin nasu yake cewa.

"Ashe daman ƙarya kuke da kuka ce babanku ne ango, ashe bashi ba ne baban su Ya,u ne(Hudu) Kallu shi ne ya sanya sabon kaya amma babanku tsoho ya saka, ai ango ba ya saka tsohon kaya"

Kabiru ne ya ce

"Wallahi muna babanmu ranar nan ya siyo sabon kaya mai kyau aka masa É—inki, kayan sun fi na baban su Ya,u kyau"

Yaron ya ce

"Ai dai tun da bai saka ba bashi ne ango ba" Malan da yake jin tamkar ya kwaÉ—awa yaron nan mari musamman da yake jaddada cewar Hudu ne ango sai tsumin Malam Nura na kishi ya motsa nan ya ci gaba da cika yana batsewa.

Ayari suka yi don zuwa can gidan matan inda za a ɗaura auren, hakan ya sa aka fara tafiya masu kiɗa suna yi. Malam Nura ne ya ji duk hankalinsa ya tashi domin yana tsoron haɗuwarsa da Hadiza ba ya ma fatan ta gan shi da kayan jikinsa. Hadiza kuwa kamar ta san tunanin da yake ta doko masa waya, jin wayarsa tana ƙara ya ciro ta daga aljihu kamar ya san ita ce kuwa domin a ransa ita ya ƙiyasta za ta kira shi a daidai wannan lokacin.

Wani gumi ne ya karyo masa amma ya yi ta maza ya maze ya É—aga wayar suna tafiya, yana karawa a kunne ta ce

"Ni fa na ƙosa in ganka wallahi, don tun da ka ambata min cewar ka yi kyau na ban mamaki, gabaɗaya sai na ji ka kwaɗaita min son ganinka, don na san yadda shaddar ta karɓe ni kai ɗin ma haka ne a naka ɓangaren" Hannu ya kai goshinsa ya sharce gumi, ya mayar da idonsa jikin kayan jikinsa ya haɗiye wani yawu muƙut ya ce

"Yanzu dai gamu nan za mu je wajen É—aurin auren" Sautin dariyarta ya ji har cikin kunnensa ta ce
Chapter 14 · 0% Book details