← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni dai tun da Nura yake aure-aurensa Haule bata taɓa kawo ƙaransa ba amma ke kin zo kina ba kanki wahala, shin baki san cewa shi namiji idan zai ƙara aure sai mace ta kawar da kai ba, sannan duk wani rawar kai da wulaƙancinsa sai a lokacin yake tsurowa, duk da ba kowane namiji bane yake haka amma yawanci mazan duk haka suke"

Kuluwa takaici ne ya cika ta hakan ya sa ta ce

"Ni dai Baba dan Allah ki bashi umarni ya fasa auren nan ji nake kamar zuciyata ,a ta buga... Baba Ramma ta ce

"Inyeee lallai fa, sannu Kuluwa, wato in hana shi rawar gaban hantsi bayan da ransa da lafiyarsa da ƙarfinsa a jikinsa ai daga nan in aure hamsin zai ƙara ba zan hana shi ba, komai lokaci ne wataran ko an ce ya yi ma ba zai yi ba"

Kuluwa ji ta yi tamkar ta shaƙe Baba Ramma har sai ta bar numfashi, duk da ba wannan ne auren ta na fari ba amma bata san mai ya sa ko mijinta na fari bata son sa kamar yadda take son Malam Nura ga wani kishi da ta ɗorawa ka ta yake ɗawainiya da ita. Tana so ta faɗa mata har ƙairace musu ya ce zai yi wai tanadin amarya zai yj amma kunya ta hana ta magana haka ta taso ta baro gidan tana da na sanin zuwa tun da babu biyan buƙata!.

Yau wani yadinsa da yake ganin ya fi kowane yadi kyan gani a cikin kayansa duk da shekara ta uku kenan da É—inkawa ya gyara tass ya saka saboda ya gaji ya biyan kuÉ—in aro kaya.

Hadiza ko da ya zo yau ta ga hannunsa babu komai hakan ya sa ta ƙi sakin jiki take wani kumbure-kumbure shi ma yana ganin yanayin ta ya san dalilin fushin amma haka ya basar don shi a nashi ganin ya gaji da nomawa jaki ciyawa yana kawo kayan daɗi don su ji daɗin hirar soyayya amma tana ba ƴaƴanta ita cw kaza uwar son ƴaƴa a zuciyarsa ya ce

'Idan aka É—aura auren ai na huta sai su koma gidan ubansu, ko ki bar su a gidan kakannin nasu ina dalili'

Hira yake jan ta da ita tana basarwa ya gaji ya ce

"Hadiza yau ko bakya jin daÉ—i ne?"

Ta yatsina fuska ta ce

"Ƙalau" Fitowar Zainaba daga gidan tana riƙe da hannun Shafi,i shi ya katse musu maganar. Zainaba ce ta tsaya shi ma ya tsaya kasancewar hannunsa cikin nata, ta sunkuyo ta masa raɗa a kunne. Kai ya gyaɗa ta saki hannunsa ya taho da gudu yana cewa

"Oyoyo baba" Yana zuwa ya haye cinyar Malam Nura ya ƙanƙame shi, kasancewar yana cin tuwo Zainaba ta je ta kamo shi suka fito. Dariyarta ta shiga dannewa ganin haƙarta ta cim ma ruwa, daman tun da ta ga Innarsu ta fito, ta saka a ranta yau ma sai ta masa abun da zai masa ciwo, hakan ya sa ta saka luda ta kwalfo miyar kuka ta ƙara a kwanon da Shafi,i yake in tuwo da yake miyar ta huce, ta ringa ɗaukan miyar da ludan ta zuba masa a jikin kayansa da duka hannuwansa har bayan hannun. Shi ne da suka fito ta raɗa masa cewar ya je ya haye cinyar Malam Nura duk ya ƙanƙame shi.

Malam Nura gabaÉ—aya ya rasa ma ya zai yi, jikinsa jaga-jaga da miya gashi kuma miyar manja ce yadda fari yadin ya sha miyar tamkar ya saki kuka.

Cikin yaƙe don kar ta ga kamar ba ya son ɗanta ya ce

"Oyoyo Shafi,i ɗana na kaina" Ya faɗa yana ƙoƙarin ɓanɓare yaron don ya maƙalƙale shi, hannuwansa suna maƙale a wuyansa hatta wuyansa da gefen fuskarsa sun san Shafi,i ya ci tuwo. Dakyae ya ciro shi yana faɗin

"Duk ka ɓata ni da miya" Ya faɗa yana kallon jikinsa. Hadiza ta haɗe rai ta ce

"Haba Malam Nura to mene ne don ya goga maka miya kai baka san yaro ba" Gudun ɓacin ranta ya sa ya washe baki ya ce

"Haba Hadiza amaryata ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, ina ni ina masa faÉ—a ai ba miya ba ko kashi ne ya goga mini ba zan ji komai ba ai É—ana ne" Dariya ta yi tana faÉ—in

"Shafi,i jeka gida ka wanke hannunka" Don ita ba ta san duk shirin Zainaba ba ne, Zainaba kuma ta ce

"Kake kamshin miya a maimakon ƙamshin turare " Ta faɗa tana dariya, don ita Hadiza ba ta son a kwaɓi ƴaƴanta bata ganin laifinsu. Ta kalle su ta ce

"Innata yau ba a kawo nama ba?"

Malam Nura a fili ya ce

"Yau ba a kawo ba a yj haƙuri ƴar baba"

A zuciyarsa ya ce

'Aikin banza shafa lalle a mazaunai kamar ubanki ne yake nema mini kuÉ—in'

Idanun uwar ta faka ta galla masa harara tare da yatsina fuska ta juya ta nufi cikon gidan Shafi,i kuwa ya ja tunga ya tsaya ya ce

"Alewa" Babu yadda Malam Nura ya iya haka ya ciro 200 ya bashi ya ce ya saya. Bai wani jima ba ya bata dubu biyun ta ta karyawa a zuciyarsa yana faÉ—in

'An kusa ɗaura aure ki tare in huta da wannan jigilar bada dubu biyu ki je can ki haɗu da su Kuluwa, ba kina kyashin cin tuwo a gidanku ba, idan kika je gidana tuwon ma gaya za ki samu sai kin nemawa kanki miya, kafin na gama cin moriyar ganga na hankaɗa ƙeyarki'

Sun yi sallama ya kamo hanya ya tafi gida yana ta jera tsakin wankan miyar da Shafi,i ya masa.

A can gida kuwa Kuluwa ta samu maganin matan ta bita zai-zai ta sha don ita tun da ya ce su bar kwanan turaka ta saka a ranta yanzu ta fara kwanan turaka. Ko da ya zo wanka ya yi ya cire wannan kayan. Tana sane da shi, don biredi da lemo ya siyo ya ci iyalinsa kuwa ko oho. Sai da ta daidaici ya gama komai ta nufi ɗakin tana zuwa ta ji ƙofa a rufe ta tura amma ƙofa bata buɗu ba. Daga waje ta bubbuga tana faɗin

"Ka buÉ—e mini in shigo" Haule tana jinta a zuciyarta ta ce

'Kin haÉ—u da wahala'

Daga cikin É—aki ya ce

"Wallahi sai dai ki kwana a waje amma na haramtw muku kwanan turaka" Tun tana magiya har ta lura abin ba na wasa ba ne. Haka ta raba dare tana zaune a ƙofar ɗakin da ta gaji ta ringa masifa ta koma ɗakinta. Washe gari ta yi ta masifa amma ko kallo bata ishe shi ba.

Zaune suke a kan benci shi da abokinsa Malam Hudu, Malam Nura ya ce

"Wannan dubu ashirin É—on ka siyo mini shadda yadi huÉ—u yar dubu biyar biyar, wannan dubu biyar É—in ka haÉ—o mini magani"

Ya kalle shi da mamaki ya ce

"Maganin mai?"

Yana masa hararar wasa ya ce

"Haba kai ma, maganin maza mana, gyara zan yi fa, ai shi ya sa ma na dakatar da su Haule daga zuwa turaka, saboda gyaran tarɓar amarya zan yi, ka ga kuwa tun da ba su na yi wa gyaran ba babu dalilin da zai sa suke zuwa mini turaka,sai dai wacce aka yi gyaran dan ita idan ta zo ta mora" Da dariya ya fashe ya ce

"Wallahi kaima abokina da wani abu to ina kai ina wani gyara" Yana masa wani kallo ya ce

",Naka wasa ne, ka san dai mata suna gyara to mu maza mai yasa ba za mu yi gyara ba? Gwara ka siyo mini ka ga ai ba raini" Karɓa ya yi yana faɗin

"Gaskiya na yarda amaryar nan ta musamman ce kana son ta, wato shadda ma sabuwa gal aleda mai kyau za ka yi ga magani," ,Shi ma dariya ya yi yana tuna irin son kuɗinsa sai dai ya samu yadika masu araha amma wannan karon dai ya yi ƙuri zai yi mai tsada.

Malam Hudu yana irga kuÉ—in ya ce

",Gobe ai da sassafe zan tafi kanon saboda na kammala abun da zan yi in gama, ni anya wannan Hadizar za ka iya sakin ta kuwa kamar yadda kake sakin sauran matan? Na ga fa ka kamu da sonta"

Ya yi tsaki ya ce

",Ita wa ta fi, ka san ai mace kamar riga na É—auke ta in saka wannan in cire wannan"

Haka suka yi ta tattaunawa abin su suna tsara yadda abubuwa za su kasance, daman ita Hadiza ya sallame ta kuÉ—in da ta yanka masa yanzu kawai É—aurin aure ne za a yi da tarewa

Mu je zuwa ba a fara wasan ba akwai ƙura mai tsakuwa ma kuwa🤔😹

MAMAN AFRAH
09025576222
[4/7, 5:00 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Bu295Z6iGnL3SoKYtgqnbZ?mode=gi_t

*UWAR AGOLA*

🅿️3️⃣

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*

*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*

*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*

*UWAR AGOLA*

NA

MAMAN AFRAH

Labarin mai cike da abin dariya

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222

🅿️3️⃣
Chapter 5 · 0% Book details