Sashe 2
Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haramun ne dai mace ta nemi saki, sannan ki sani babu saki tsakanina da ke har sai kin zauna na tsawon lokaci a gidan nan, in kin manta in tuna miki, auren biyan bashi aka mini da ke, ina bin mahaifin ki dubu takwas ya hanani ya bani auren ki, aka ranta masa dubu takwas na cika dubu biyu aka biya sadaki dubu goma dan haka ba zan yi asarar dubu goma ba duka watan ki biyu fa a gidan nan" Ya faÉ—a yana mai juyawa ya kama hanya zai fita domin zuwa hira wajen annurin zuciyarsa amaryarsa wacce yake kan ganiyar soyayyarta da kwaÉ—ayin auren ta.
Yana dab da shiga zauren gidan, Kuluwa wacce ya bari da ƙamshin turarensa ta ɗaga murya cike da takaici ta ce
"A haka za a ƙare dai!. Da wani turare mai warin gawa, ai wallahi amaryar ma bata da aji tun da ba a shafa turare ɗan fesawa sai madarar turare" Har zai tafi, sai kuma ya juyo yana nuno ta da yatsa ya ce
,"Ki taka a sannu bar ganin kin tara ki kiyayi mai nema, kuma ba don biyan bashi aka mini da auren ki da tuni na sake ki wallahi dan ni sakin mace tamkar in je jigon dabobi ne in since rago daga É—aurin da aka masa" Yana faÉ—a ya fice .
Kuluwa wani takaici ne ya mata dirar mikiya, kallon ɗari biyar ɗin da ta yaga ta watsar ta yi haushi ya sa ta juya da gudu gudu ta shige ɗakin ta taje take kuka dan hatta garin kwakin da take sha ji ta yi duk ya fita daga ranta, ƙafa ta saka ta yi ball da kwanon garin, tamkar dai shi ya mata laifin sai da kwanon ya kife garin ya malale a ƙasa ta yi zaman ƴan bori a tsakiyar ɗakin tana tunanin mafitar hana auren Malam Nura dan tana ƙaunarsa kuma ba ta so ya auro wata ta hana ta rawar gaban hantsi, daman ta daɗe tana jin raɗe raɗin yana neman aure duk da shi daman auri saki shi ne sana,arsa.
Malam yana fitowa ya nufi, wajen Idi mai gashin tsire sai da aka cika masa ƙatuwar takarda da tsiren ya cake kuɗin ya bayar, ya ratsa shagon Abbati mai kayan sanyi ya sayi lemon kwalba guda biyu masu sanyi. Yana ta jin daɗin zuwa ya ga masoyiyarsa ya kama hanyar yana hango irin cin tsiren soyayyar da za su yi da bazawarar tashi, domin shi ya sa ma ko tuwon gidansa bai ci ba.
Sallama ya sa aka yi da ita dan yana ta kiran wayar ba a ɗauka ba, gabaɗaya sai haɗiyar yawu yake kasancewar ƙamshin tsiren da cika masa hanci alla-alla yake ta fito. Jim kaɗan babu ɓata lokaci kuwa sai gata ta bayyana. Tun da ta fito ya mata ƙuri da ido har ta ƙaraso, irin takun da take yi shi ne yake ƙara narkar masa da zuciyarsa a kanta yana son ganin mace cikakkiya, ɗaurin ɗankwalin ta turo ka ga tsiya shi ne ya fi tafiya da Malam Nura bai san ya washe haƙora ba sai da ya ji muryarta ta karaɗe kunnuwansa da faɗin
"Kallon fa?" Da sauri ya dawo hayyacinsa yana faÉ—in
"Ai ke ɗin ce kullum kamar sake miki halitta ake yi" Ya faɗa yana kafe ta da kallon ƙurilla.
Dariya kawai ta masa ba tare da ta ce komai ba, shi ya gaishe da ita ta amsa a maimakon ta fara gaishe da shi, kujerar da ta fito da ita a hannunta ta zauna a ka shi kuma yana rakaɓe a jikin katangar, har ya saba idan dai zai zo zance ba ta bashi abun zama. Ledar hannunsa ya ajiye ya ɗakko wani dutse a can gefe mai ɗan girma wanda zai isa ya zauna a ka ya zauna, har lokacin yana ta washe baki.
Sun ɗan fara taɓa hira kenan ya janyo ledojin ya fito da lemukan tare da takardar yana kallon ta ya ce
"Wannan tsaraba ce siyowa na yi dan na birge ki... Tun kafin ya ƙarasa maganar Hadiza ta saka hannu ta dafe takardar ta saka a leda bai ankara ba ta saka lemukan a leda tana faɗin
"Ina godiya sosai, shi ya sa na fitar da kai tilo a cikin zawarawana, saboda kai na fasa komawa gidan tsohon mijina dan na san zan huta za ka gwada mini gata" Dariyar yaƙe ya yi ya ma kasa furta komai dan ya ga ƙarfin halin nata shi da ya siyo su ci tare shi ma ya mayar da mugun yawu amma ta tattare, a zuciyarsa ya ce
'Aikin uban me kika mini da zan ciko miki takarda da tsire haka, to wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa' Ganin yanayinsa ya sauya ta ce
"Ka yi shiru" Da É—an sauri ya ce
"Daman siyowa na yi mu ci tare muna hirar soyayya"
A zuciyarta ta ce
'Tashin balagar tsintsaye, idan ka ci nama da lemon nan ka ce ba sunana Hadiza ba'
A fili ta ce
"Ka ji ɗan aljanna bari na buɗe mu ci, ai ina ta jin labarin yadda kake farantawa iyalinka ma" Ya washe baki yana tuna yadda ya biya wanda suka shirya mata ƙaryar nan tun da asali ba a garin suke ba dawowa suka yi.
Yana gyara zaman hular kansa wanda duka haya ya karɓo a wajen Iliya me wanki da guga ya ce
"Duk sati sai an yanka É—an akuya, kullum kuma ana yanka kaji biyar" Ta lunshe ido ta ce
"Babu mai raba ni da kai sai mutuwa ina son namiji mai kyautatawa iyali"
Ya kalle ta yadda take farrr da ido ya ce
"Ai ni in dai wannan fagen ne bani da matsala ko kayan faɗar kishiya kowacce akwati guda na mata, yanzun nan sai da na musu kyautar dubu biyar biyar" Ya faɗa yana tuno kuɗin faɗar kishiyar da ta basu ɗari biyar biyar da yadda suka sha daru da Kuluwa wacce takaici da baƙin kishi ya sa ta yaga tata ɗari biyar ɗin.
Tana buÉ—e takardar ta ce
"To ai hakan da daɗi za su ji sauƙin kishin" Ya kyalkyale da wata dariya ya ce
"Ai basu da matsala yanzu ma sai da suka bani saƙon gaisuwa, dan Kuluwa amarya tana ta nannaga cewa kar na manta saƙon gais...
Zuwan Zainaba ƴar kimanin shekaru goma sha uku wajen, shi ya katse masa hanzarin maganar da ya guntso zai fesar, tamkar an jefo ta haka ta musu dirar mikiya, sanye take da atamfa riga da zani, ta ɗaure wani mayafi ƙarami a ƙugunta tamkar wacce aka sakawa wasan dambe.
Zainaba Æ´ar Hadiza ce yaranta biyu zainaba mai shekara goma sha uku sai kuma Shafi,i mai shekara uku, ita kuma Hadiza tana da shekaru talatin cif.
Kamar ya kwaɗawa Zainaba mari haka ya ji, ya lura yarinya bata da kunya ko kaɗan shi kuma son uwarta ya rufe masa ido yana tsoron ya tsawatar mata a samu matsala, hakan ya sa ya miƙa hannu ya ɗakko naman yanka ɗaya dan ya fara jin haushin kar Hadizar ta ɗaukawa Zainabar naman da yawa.
Zainaba wacce babu wanda ta tsana sama da Malam Nura dan ta fi so mahaifiyarta ta koma gidan mahaifinta, gata da shegen kishi kamar ba yarinya ba tsananin kishi take wa ubanta, shi ya sa duk ta tsani zawarawan Hadizar musamman Malam Nura da yanzu shi za ta aura. Da gangan ta je kamar za ta durƙusa ta buge hannunsa naman da yake miƙo mata tsoka guda ya suɓuce ya faɗi, ita kuma Zainaba da sauri ta ce
"Ban gani ba" Ta faÉ—a kamar za ta yi kuka, murmushi Hadizar ta yi ta ce
"Ba komai kin san shi babu ruwanshi" Wani abu da ya tsaye masa ya haɗiye muduk ya ƙirƙiri dariyar yake ya ce
"To waye bai san yaro ba, bare ma bata gani ba" Zainaba ta faki idon mahaifiyarta ta wurga masa wata muguwar harara tare da murguÉ—a masa baki ta sunkuya ta ce
"Innata ashe za ki iya cin daɗi ban da mu?" Hadiza wacce take baƙincikin su ci naman tare da Malam Nura ta ce
"Haba Zainaba daman za mu rage muku ke da É—an uwanki, amma tun da kin zo É—auki kawai mu sai mu ci girma" Baki sake Malam Nura yake ganin ikon Allah, domin kaf Zainaba ta naÉ—e takardar ta haÉ—a da lemukan ta kama hanyar shiga gidan, Hadiza ta É—an É—aga murya ta ce
"Kar fa ki hana Shafi'i" Da to ta amsa mata ta shige gidan, Malam Nura da ƙwallar baƙinciki ta kawo a idanunsa da sauri ya yi hanzarin mayar da ita yana washe bakin ƙarfin hali ba ya so ta gane halin da yake ciki, ga yunwa da take ƙwaƙular hanjinsa.
A zuciyarsa yana faÉ—in
'Wayyo dubu huÉ—u ta da É—ari biyar'
Tana ƙara turo ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi ta ce
"Tun da an yanka kaji ai sai ka ci idan ka koma gidan ko masoyi" Kamar zai yi kuka ya danne ya ce
"Ai kuwa naman kaza yana can don kwanon samira aka cika mini, idan na koma na ci" Ya faɗa yana sauke idanunsa a kan hannunsa ta cikin farin wata sai sheƙin man jikin naman da kuma ɗan burbuɗin ƙuli-ƙulin da ya maƙale a hannun.
Idanunsa ya sauke a kan yankan ɗayan da ya faɗi daga hannunsa wanda Zainaba ta bige masa, kuma shi dai iya saninsa ya san da gangan ta yi don ba sa ga miciji da ita, ido ya ƙurawa yankan naman ya ga ashe har ƙafa ta saka ta murtsuke yadda ba zai amfanu ba, da a nufinsa idan sun yi sallama da Hadiza ta shige gida ya dawo ya ɗauka a ƙalla dai ya rage asara!. Muryar ta ce ta katse masa tunani da faɗin
"Bari na shiga gidan ina son shiga banɗaki" Wani irin washe baki ya yi ta tashi shi ma tashin ya yi ta ɗauki kujerar ta, sallama suka yi ta tsaya masa ƙememe me ta ce