← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iya ƙarfin ta ta bada himma da ƙaimi wajen danne gudawar da take son ɓata mata wandon Malam Nura da ta saka wanda take ganin shi ne makamin da za ta ja hankalin sa har ya kai ga cikar burinta wato kwana a turaka, sannan ya zamana bata yi asarar kuɗin magungunan da ta saya ba. Fasa rarrafen ta yi ta koma daɓas ta zauna ta muskuta mazaunanta a ƙasa tare da sake murza su a ƙasan duk don ganin ta mayar da gudawar da take son ƙwace mata, domin iya tunanin ta ta fara hasashen ba za ta iya matsewa ba. Sau uku tana murza mazaunan duk da faɗuwar da gabanta ya yi musamman da ta ji aljani har ya san sunan ta, duk da tana tunanin ko dai ya haddace sunan nata ne lokacin da ta ce ita ce Hauwa Kulu da aka fi sani da Kuluwa.

Duk da gudawar bata koma duka ba amma dai da dama dama wai kibiya a ido, domin kuwa ta daina matsar ta kamar ɗazu. Hannu ta kai jikin bokitin ta shiga kokawa ita da bokiti saboda tana so ta ɓanɓare shi ko ta samu damar gani da idon ta domin idan tana gani za ta fi samun hanyar tsira saɓanin idanun a rufe.

Ta ja bokitin amma ta ji ya kama kan sosai, ta sake ja ta ji babu alamar zai fita a fili ta ce

"Na shiga uku ni Kuluma(Ta ce Kuluma a maimakon Kuluwa) Ya na ji abu ya zama tif da taya da gashin kaina?"

Malam Nura jin ta kira kanta da Kuluma a zuciyarsa ya ce

'Ai sai kin kira kanki da sunan maza yau, idan aka jima farkon sunan naki ma ba za ki tuna ba sakaryar banza da wofi mai almubazzaranci, haka kawai shaddar dubunnai kika ƙona'

Daddagewa ta yi ta shiga ƙoƙarib miƙewa tun da ta ji ɗif babu motsin kowa, amma sai dai mai tana miƙewa ƙafafun ta hagu da dama santsi ya kwashe su ta koma ta yi zaman ƴan bori a cikin lakar a fili ta ce

",Na ga ta kaina yanzu kayan nan da na saka a raina zan wanki Malam da shi, zan ɗauke masa hankali daga sabuwar amaryar nan Hadiza shi ne nake faɗuwa a cikin laka ya zan yi da raina" Ta faɗa tana shafo jikin wandon domin jin inda lemar ta taɓa.

Malam Nura ya shiga jijjiga kai yana bin ta da kallon tsana a ransa ya ce

"Wato ni za a cuta da wannan wandon da ya miki kamar ƙafar tattabara, ai gashi nan kin zama kamar wacce ta yi nutso a ruwan kwata, amma za ki gane shayi ruwa ne'

Yana faɗar hakan ya zo bayanta ya riƙo rigar daga baya ya shiga jan ta ƙiiiii amma ba wai gaba yake jan ta ko baya ba, kawai yana gewayawa da ita ne, wato round yake yi da ita, Kuliwa wacce ta fara saka rai a samu salama jin bata jin komai tunanin ta aljanin ta gama wadaƙar da zai yj da ita amma sai ta ji ana jan ta ana juya ta tamkar fanka, a gigice ta shiga faɗin

"La haula wala quwwata" Ita kawai take maimaitawa a kiɗime domin zuciyar ta ta gama bata cewar ko dai wani jirgin aljannu ne zai tashi da ita zuwa garin aljannun shi ya sa ta ji yana juyawa hakan ya sa hanjin cikin ta ya karkaɗa da ƙarfi. Malam kuma ƙaimi ya bayar wajen juya ta a cikin lakar nan da cakwalin ruwan alwalar wajen.

Tun tana la haula wala quwwata har ta dawo tana cewa

"Wa qulna ya naru kuni bardan wa salaman ala ibrahim" Haka ta shiga maimaita samu fatiha.

Sai da ya ga ta jigata sosai sannan ya sake ta, saka ta ɗin da zai yi tamkar ya tura ta suuuu ta bi caɓalin santsi ya kai ta dab da banɗakin ta rarrafo tana son guduwa ɗaki, jin ta samu bango ta dafa ta tashi tsaye ƙafafun karkarwa kawai suke kamar mazari, ganin hakan Malam ya juya ya ɗakko fanteka a ƙofar ɗakin Haule ya haɗo da wata bulallar maina.

Yana zuwa lokacin ta ji tsoro da tsurewar da ta yi ba za su bar ta ta iya tafiya da ƙafafun ta ba, hakan ya sa ta durƙushe yana zuwa ya saka fantekar ya buga a saman bokitin, wani sauti ya bada wanda Kuluwa ta zaci aljanin yana adawa da kan ta ne, bayan abun da aka kifa mata hallaw ake son raba kanta da jikin ta. Hakan ya sa da sauri ta rarrafa kamar irin guragun nan masu laulayayyar ƙafa idan suna rarrafawa suna wani irin sauri, haka ta shiga sauri tamkar ana tura ta. Malam da sauri ya bi bayan ta ya ɗaga bulallae ya tsula mata, cike da yadda bulallar ta shige ta ta mata shigar sauri ta miƙe tsaye babu shiri, da ta tuno yadda lakar take taɗe ta da yadda ta ji an jujjuya ta ɗazu da sauri ta sake tsugunnawa sai kuma ta sunkuya kamar mai naƙuda tana jiran tsammani don ita gabaɗaya an dagula mata lissafi.

Malam tuno da Hadiza ta ƙi tarewa ne saboda abin da Kuluwa ta masa ya sake ɗaga bulalar ya zabga mata.

Cike da tsoro ta ce

",Ni dai Kuluwa alƙiyamata ta tsaya, ina zan ga Malam kafin in cika in nemi yafiyarsa a kan wandon angoncin sa da ƙona, Malam ka zo gida ka yafe mini ga aljannu za su yi ajalin Kuluwarka" Ta faɗa bakin ta yana karkarwa, wata harara ya aika mata tamkar tana ganinsa.

Ƙafafun wandon jin ya mata jagafgaf ta shiga naɗewa domin gudu za ta yi ba na wasa ba, ko ɗakin Malam ne ta samu ta tsira da ranta saboda abin da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa. Tana tashi tsaye ya saka mata ƙafa cike da mugunta sai gata ta yi sama ta dawo ta rafku da ƙasa cike da ficewar hayyaci ta ce

"Allah ya isa... Maganar ce ta maƙale kafin ta ƙarasa sakamakon tunowa da ta yi da cewar aljannu ne. Saɗaf saɗaf ta fara rarrafawa tana fatan ba su ji Allah ya isan da ta musu ba.

Rabuwa ya yi da ita sai da ta kusa da É—akin sa tana faÉ—in

"Allah ya taimakeni gwara in je ɗakin Malam" Ta faɗa maganarta tana karkarwa, sai da ta kusa zuwa tana lalamawa ya saka ƙafarsa ya buga a ƙasa sau biyu, Kuluwa jin wani ƙara didif da ƙarfi sai ta ɗauka sakkowar wani aljanin ne, hakan ya sa babu shiri ba zato da tsammani ta miƙe tsaye ta falfala a guje duk da shamaki da bokitin ya mata da ganin gabanta, burin ta kawai ta shige ɗakin Malam gani take za ta tsira.

Malam Nura a zuciyarsa ya ce

'Kaico Kuluwa ai tun da kika taɓa ni kin taɓowa kanki wallahi' Murya ya maƙe tamkar an shaƙewa biri wuya ya kasa magana haka ya mayar da muryarsa ya ce

"Za ki faÉ—a wutar aljannu gata nanta cika É—akin mijin naki sai ci take kamar an watsa fetur...

A zuciyarta kuma ta ce

'Wuta? Innalillahi kar ta kwaile min mazaunai i rasa wanda zan ke juyawa in amarya ta zo'
Ai ba ta jira ya ƙarasa maganar ba ta ja wani uban birki, ba ta san lokacin da ta yi wata kwana ta juyo ba.

Malam a zuciyarsa ya ce

'Wato kwana ba sai mota ba, mutum ma yana ribas kuma ya yi kwana' ,

Kwanar da ta yi ne ta taho a kiÉ—ime ya sake gyara murya ya ce

"Kuluwa za ki faÉ—a ruwan maliya" Da kuka ta fashe bayan ta dakata da maganar don yanzu ta fara tunanin ko dai ba a duniyar mutane take ba a duniyar aljannu take.

Zaunawa ta yi a ƙasa take mismis da baki tamkar mai zikiri amma ita kanta ko wuƙa za a daka mata a maƙoshi ba ta san abin da take faɗa ba. Amma dai da fargaba tana sanya ƙirji ya fashe da tuni nata ratattakewa zai yi domin a matuƙar tsorace take ita ba komai ne damuwar ta ba rashin sanin abin da yake a kanta. Ganin ta zauna ɗam ya taho ya saka bulallarsa ya zane ta tsaf duk ya burɗa mata jiki, idan ya tsula a nan ta saka can ta riƙw can har sai da ya tabbatar da ta jigatu kuma ya ji ɗan sanyi a zuciyarsa dangane da abin da ta masa sannan ya ƙyale ta. Sai faman basu haƙuri take har zai fice daga gidan ya fasa ya juyo dan ya ƙara tsorata ta cikin murya mai ban tsoro wannan karon ya yi magana ya ce

"Yanzu za mu kyale ki, amma dai za mu cire miki mashayar ɗa (Breast) Guda ɗaya" Da sauri ta saki wajen ƙafafun ta da take murzawa ta riƙe mashayar da suka ambata tana zare ido daga cikin bokitin cike da murya kamar za ta yi kuka ta ce

"Ku mini rai komai zan baku amma kar ku cire mini mashaya wallahi ban taɓa haihuwa ba ban shayar da ɗana ba, kuma mijina sabon aure zai yi, idan kuja cire mini kar a zo ake mini gori tun da gidan kishiyoyi ne"

"Malam ya aikawa kirjin nata da ta damƙe gudun kar tsautsayi ya rutsa da mashayar kamar yadda aljanin ya faɗa mata a zaton ta, a zuciyarsa ya ce

"Aikin banza abu ba abu ba, akwai ya babu kakar wajen uba, abu kamar ƙwallon goruba amma tana faman tada hankali'

Jin haka ya ce

"Za a guntule miki hanci da fatar baki" ,

A zuciyarta ta ce

"Wannan aljanin maye ne, ta saka hannunta guda É—aya cikin bokitin ta dafe hanci É—aya hannun yana kan mashayar da ta dafe.

Yana tunano wata sabuwar muguntar da zai mata sai ya ji alamun tahowa za a shigo cikin gidan, da sauri ya zo ya dilliƙa mata wani uban ƙulli har sai da ta gantsare, a zuciyarsa ya ce

'Ko banza kin ci uwar wuya' Yana faɗa ya yi saurin laɓewa yadda mai shigowar ba zai gan shi ba. Haule da ta dawo ta buɗe baki ta yi sallama, kasancewar ta baro su Alawiyya a gidansu sun ce a can za su kwana.
Chapter 23 · 0% Book details