← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ya shigo gidan, matan nan duk sun watse sai kaɗan, bai ga Kuluwa ba, shi ma bai nemi inda take ba saboda daman ba nemanta yake ba, a cewarsa tauraruwa mai wutsiyaci ganin ta ma ba alkairi ba ne. Ɗakinsa ya nufa ya rufo ƙofar cike da hanzari ya cire kayan jikinsa ya saka wandon ya ɗora rigar ya kalli jikinsa ya fashe da dariya a fili ya furta

"Hadiza daman rashin wando ne ya mini cikas yanzu za ki tabbatar da cewa wanka iya wanka Malam Nura ya iya" Ya faɗa yana sake kallon wandon tabbas ba a ganin saman yadin da aka haɗa daga sama, sannan waje da aka yi ɗinke-ɗinken ma ba a gani sai dai wanda ya yi kallon ƙurilla. Kayan ya cire ya linke, ya ɗakko wani kayansa ya saka don bai mayar da yadin Hudun ba saboda haushin yadin ma yake ji.

Ya gama kenan, Haule ta zo ta buga ƙofar ya ce

"Waye?"

Ta ce

"Ni ce fa ango na amarya Hadiza" Wani daÉ—i ne ya baibaye shi jin kiran da ta masa, duk da yana jin haushin yadda Hadiza ta masa a gaban mutane amma kuma da yake bahaushe ya ce, so hana ganin laifi, sai ya fara ganin laifinsa ne ba laifin Hadizar ba.

Yana washe baki ya buɗe ƙofar yana faɗin

".Na baki É—an mutum da uwarsa" Dariya ta saki tana faÉ—in

"Ai ka cancanta ne ango, Allah dai ya sa an É—aura a sa,a ya bada zaman lafiya" Da amin ya amsa har ya yi shiru ya ce

"Haule anya kina sona?"

,Haule ta ce

"Mai ya kawo wannan maganar?" ,

Malam ya ce

"To ai ke É—in ce sai kike ta nuna kamar dai bakya kishina, amma ko kaÉ—an ne ai kya É—an gwada min kishi" A fili ta ce

"Ai ka san ka so abin da mutum yake so ma yana cikin so"

A zuciyarta ta ce

'Ku maza mace ma ta yi kishin ku ta haÉ—a kanta da wahala, yanzu ba ga Kuluwa nan daga yin kishi kake neman nakasta ta ba, haka kawai ai gwara ma mace kar ta É—ora namiji a ranta hakan zai sa ta zauna lafiya'

Malam ya É—an yi shiru ya ce

"Kuma fa haka ne"

Haule ta ce

"Yawwa, daman na ce ko a kawo maka abinci na ga baka zauna ba ma bare ka saka wani abu a cikin ka, ni kuma duk na damu" Dariya ya yi ya ce a zuciyarsa

'Namiji É—an gatan mata, wato dai kai idan matarka É—aya ce shikenan ba kowacce mace ce take bada kulawa ba, amma idan sun haura É—aya sai abin da ka gani kowacce sonka take' ,A fili ya ce

"Barni Haule ai no yau ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, babu batun cin abinci har sai na je na yi hoto da Hadiza kin san ranta ne ya ɓaci da bamu yi hoto tare ba da ta ganni da wannan yadin" Haule ta ce

"Ba dole ya ɓaci ba wataƙila ta shiryawa ranar ne"

Malam ya ce

"Shiri ma ai in kin ji É—aya kenan, in banda wannan Kuluwar Æ´ar wahala ta kawo mini cikas har akwai wanda zai kaini wanka" Shiru ta yi bata ce masa komai ba, saboda ba É—abi,arta ba ne yi da kishiya a bayan idanunta.

Sallama ta masa ta ce sai ya fito. Tana fita ya fito ya ga wani bokiti cike da ruwa, lokacin tsakar gidan ma babu kowa sai su Alawiyya suna cin abinci. Yana É—aukan bokitin ya yo hanyar banÉ—aki, ya shiga ya rufo, Kuluwa tana kallonsa kuma ruwanta ne amma sanin akwai wata wutae tsakaninsu ya sa bata fito ba, domin ita hankalin ta kwance an yi É—aurin aure ya je da tsohon kaya, kuma yanzu ma don zai je ya yi wanaka ta san sai dai ya saka wasu kayan aron.

Yana shiga ya yi wanka ya fito, ya shiga ɗakinsa ya saka sakata, yana goge jikinsa ya saka singlet, ya ɗakko rigar shaddar nan ransa fari ƙal ya saka ta ya saka wandon da ya zo ɗauree mazugin sai ya ga ƙarami ne Ibra ya saka masa, ɗazu ma da ya gwada saboda a ruɗe yake shi ya sa bai lura ba, wata zuciyar tana faɗa masa ya cire ya saka wani wata tana faɗa masa kawai kar ya ɓatawa kansa lokaci ya bari.

Maɓallin ya ɓalle ya ɗakko hularsa ya gyara karin ya goga mata turare ya saka, ya sanya turare a kayansa sosai ƙamshi ya cika ɗakin ya saka takalmansa ya je gaban madubi, ba ƙaramin kyau ya yi ba sosai ya yaba yana fatan Hadiza ta yaba fiye da shi a fili ya ce

"Ashe dai ina da fasahar da zan saka shaddar nan a ranar nan amma na zauna na je ɗaurin aure da tsohon kaya" Ya faɗa yana ɗaukan wani tsumma ya sake goge takalmin sa. Ƙaramar ledar da magungunan mazan sa suke ciki ya ɗakko, wanda Hudu ya faɗa masa sai ranar da amarya za tare zai sha, sannan ya ce masa a huɗu zai raba maganin, wata ƙaramar kwalba ce kamar ta magani, a jikinta an sake laulaye ta da leda a cikin ledar kuma wata ƙwayar magani ce guda ɗaya, ita ƙwayar Hudu ya ce masa a biyu zai raba, ita kuma na kwalbar a huɗu. Yana ɗaga kwalbar bayan ya buɗe sai da ya sha ya fi rabi, wanda ya bari bai fi kwata ba, ya ɗauki ƙwayar da aka ce ya raba a biyu ya saka a baki ya tsotse ita ma ya tsotse ta duka, ya mayar da komai cikin ledar ya ɓoye.

A fili ya ce

"Ba a bori da sanyin jiki, ai tun da dai amarya yau za ta tare ina na ga ta zama, ai gwara na shanye duka, shi ma na kwalbar da na rage saura da daddare kafin a kawo ta zan shanye tasss, don ba zan zauna ta raina ni ba gwara ta san babu raini a lamarin"

Ƙofar ya buɗe ya fito yana cikin kullewa Haule ya fito daga ɗaki, wata uwar guɗa ta carara tana faɗin

"Kai ma sha Allah, kyau iya kyau ango, wanka iya wanka, na Hadiza jan gwarzo, na Hadiza mai kyan mamaki" Ɗari biyar ya ciro ya miƙa mata ya ce

"Ki ba su Alawiyya hamsin-hamsin ki riƙe canjin" Karɓa ta yi tana masa godiya, sannan ta ce

"Malam idan an yi sallar magriba zan je gida, baba zan dubo bai ji daɗi ba duk da dai an ce jikinsa da sauƙi amma dai zan dubo shi"

Malam ya ce

"Subhanallahi, a ki je kya masa sannu kafin in samu in ɓulla" Amsa masa ta yi ya yi gaba abin sa.

Kuluwa wacce take ɗakinta jin guɗar da Haule ta yi ya sa gabanta faɗuwa, musamman kirarin da Haulen ta masa ya ƙonawa Kuluwa rai, amma haka ta taso domin ganewa idonta tun da dai bahaushe ya ce baba bori da sanyin jiki, tana leƙowa daga window abin da ya gani ne ya ɗaga mata hankali sa sauri ta dafe ƙirji tana zaro idanunta don su tabbayar mata da abin da ta gani zahiri ne ko kuwa gizo ne. Tabbas shaddar da ya ƙona wandon ta ce sanye a jikin Malam, kuma wandon ne take gani sannan shaddar sak ce a wandon daga gani ba haɗawa aka yi ba wato ba wata kalar shaddar ce aka samu wacce zanen ba ɗaya ba ne.

Ranta ne ya ɓaci sai dai bata da damar amayar da abin da yake cikin ta, tun da ta san yanzu ma da sauran rina a kaba tun da ba yafe mata ya yi ba.

Malam kuwa fita ya yi hannunsa ɗaya a aljuhu ɗaya yana riƙe da wayarsa da take ta ƙara. Yana fita Kuluwa ta fito tana huci kamar zakanya wani uban ƙamshin turare ne ta jo ya ziyarci hancin ta, ko ma ta ce ya buɗaɗe tsakar gidan, tsayawa ta yi ta kama ƙugu tana wani karkaɗa kai ta taɓe baki ta ce

"Oh ni Kuluwa duniya sabuwa Malam Nura sanye da sabuwar shadda mai tsada yana ƙamshi tamkar an yi ɓarin turare" Haule ta yi dariya ta ce

"Wallahi kuwa wai wajen amarya Hadiza zai je su yi hoto... Tun bata ƙarasa ba Kuluwa ta tari numfashin ta da faɗin

"Ke kam Haule Allah yaye miki, yanzu a gabanki mijinki ya fita ya tafi wajen wata banza, amma har kike wasa shi kina ce masa wani na wata can banza, bayan kin san a cikin gidan gani ga kuma ke, ai ko da me -da me biyu ta fi É—aya ko a rabon gado!" Haule ta tsura mata ido ta ce
..."To ina ruwana ita ma ta yi ta kanta, kuma ai na ga matarsa ce, to ya ma kike so na yi cakumarsa kike so in yi mu yi dambe saboda zai je wajen matarsa, to wallahi ni ko wajen bazawara zai je ba zan wahalar da kaina ba"

Kuluwa ta ce

"Ke dai na lura wannan É—an kuÉ—in da yake baki ne suke rufe miki ido sho ya sa bakya samun damar nuna kishin naki"

Haule ta yi wata Æ´ar bazawarar dariya ta ce

"Ai ko da me da me kurna ta fi magarya zaƙi, inaso ki sani ba wai ba na son Malam ba ne kuma ba wai ba na kishin sa ba ne, a,a kaina dai na shafawa lafiya game da lamarin maza, sannan abu na gaa kin san da neman kuɗi nake kaina da ƙafata ina sana,a to kuɗin na nasho da bai taka kara ya karya ba maganin matsalata zai min? Kin ga kenan kawai dai a bar kaza a gashin ta, ke da kika ɗorawa kanki kishin da mai kika tsira, ba don Allah ya rufa asiri ba da yanzu ƙafafun ki biyu ba sa jikin ki" Tana faɗar haka ta juya ta bar wajen.

Ran Kuluwa ya ɓaci jin Haule ta faɗa mata magana, tana yin ƙwafa ta ce
Chapter 19 · 0% Book details