← Book details Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

Uwar Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[4/5, 3:04 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=gi_t

*UWAR AGOLA*

NA

MAMAN AFRAH

Labarin mai cike da abin dariya

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222

🅿️1️⃣

Malam Nura ne tsaye a tsakar gidansa ya sha babbar riga yana baza ƙamshin turarensa da ya bankaɗa, sai wani ɗaɗɗaga kai yake tamkar ƙadangare, taku biyu ya yi ya ja ya tsaya yana hura hanci ya shiga kwaɗawa matarsa uwar gidan kira.

"Haule" Kira É—aya ya yi a na biyu ta amsa ta fito daga É—aki ta zo ganinsa yana cika yana batsewa ta nemi kujera Æ´ar tsugunno ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido. Ko kallo bata ishe shi ba ya shiga kiran É—aya matar tasa.

"Kuluwa, Kuluwa, Kuluwa" Shiru kake ji wai malam ya ci shirwa tamkar ma bata gidan, kallon Haule ya yi ya ce

"Kuluwa ta fita ne?" Wani takaici ne ya turnuƙe ta amma ta danne abin da ta ji ta ce

"Haba Malam ka tambayi agwagwa hanyar rafi, ai kaza za ka tambaya kansha labari" Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka ya zaburo ta da masifa yana faÉ—in

"Dakata Haule ni fa Kuluwa kawai na tambaye ki ba wai baƙar magana ba, ke ga mai bakin aku daga an tambaye ki abu sai ki tsiri karin magana ke ga wacce ta yankewa ƙasar Hausa cibiya" Banza ta masa kamar bata ji ba, ganin haka ya ƙara cewa

"Wai ba magana nake miki ba Haule? Wai ku mata mai ya sa bakwa kiyaye aljannarku da za ku samu a ƙarƙashin ƙafar mijinku ne? Yanzu ya kyautu ki wofantar da ni?" Haule a ƙufule ta ce

"Ka tambayeni na baka amsa ka ce baƙar magana na faɗa maka, kai ba kuturu ba ba kuma makaho ba, ba gaka ga ɗakin Kuluwar ba baka zuwa ka duba ko tana nan, a ce kana mijinta amma kana tamabayata ko ta fita, idan fitar ta yi ma ai kai ba za ka kasa sani ba, dole za ta sanar maka... Tun kafin ta kai aya ya tari numfashin ta da faɗin

",Ai ka ji, to ni bani da lokacin ɓatawa taɗi zanje wajen amarya dan haka idan neman magana kike sai ki yi ke kaɗai tun da kare ma ba ya haushi shi kaɗai" Ya faɗa yana juyawa ya shiga baza babbar rigarsa ya nufi ɗakin Kuluwa tun kan ya ƙarasa yake ci gaba da kiranta tun yana faɗin Kuluwa, har yake kiran ta da sunan ta na gaskiya wato Hauwa amma shiru.

Kuluwa kuwa duk abin da ake tana jin su kawai niyya ce bata yi ba shi ya sa bata amsa ba, yana zuwa ya É—aga labulen É—akin idanunsa suka sauka a kanta tana zaune a tsakar É—akin da kwanon silba a gabanta hasken fitilar ta ya gauraye É—akin. Kallo É—aya ta masa shi ma na raini ta sauke idanunta a kan kwanon gabanta, garri ne take sha da gyaÉ—a a ciki dan haka sai da ta ciko luday ta kai baki ta sha, kafin ta haÉ—iye ya ce

"Kuluwa yaushe na zama sa,an ki ne?" Bata ce ƙala ba sai da ta haɗiye ta saka ludan a kwanon ta miƙe tsaye ta ce

"Wallahi idan ka sa na ƙwaru sai na kai ƙaranka wajen mai gari ka biya ni diyya?" Saroro yake kallon ta ya ce

"Kashe ki na yi da zan biya diyya" Tana muzurai ta ce

"Ni dai na faÉ—a maka hawainiyarka ta kiyayi ramata wallahi, dan ... Hanzari ya katse mata da faÉ—in

"To uwar ƴan kishi ki fito ina da magana da ku, ita ta fito amma ke da bakya iya danne baƙin kishi shi ne za kike ɗaga jijiyar wuya, to dan ki sani aure babu fashi, da ba a aure ba zan aure ki ba" Yana faɗar hakan ya juya fuuuu ta biyo bayansa ranta in ya yi dubu ya ɓaci, daman ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya!.

A daidai inda Haule take zaune ya ja tunga ya tsaya ita ma tana ziwa ta kama tsantsa da hannu biyu ta tsaya tana wani karkaÉ—a kai, irin na mai jiran kule ta ce casss. Malam Nura bai yi wata-wata ba ya ja wata doguwar gyaran murya ya ce

"Ba tare da ɓata lokaci ba dan ina da wajen zuwa, domin wajen amarya mai jiran gado zan je, yauwa na tara ku ne a kan na faɗa muku sati mai zuwa ranar asabar za a ɗaura mini aure, kuma ina ƙara jaddada muku duk mai son zaman ta ya ci gaba da wanzuwa a cikin gidan nan to ta tabbatar ta yi biyayya ga maganata sannan ta shirya tarɓar sabuwar amaryata" Ya faɗa yana washe baki a daidai inda ya ambaci amayarsa tamkar an masa bushara da gidan aljanna.

Haule ta yi wata Æ´ar dariyar rainin hankali ta ce

"Ubangiji Allah ya sanya alkairi, ya bada zaman lafiya, ya kawo ta lafiya" Tana kai wa nan ta miƙe abin ta hankali kwance za ta bar wajen, Malam kamar an warto maganar daga bakinsa ya ce

"Haba Haule kamar wani wanda bakya sona, ina faɗa muku batun ƙarin aurena zan muku kishiya amma ke hankalin ki kwance, kamar an tsoma tsumma a randa?"

Wata Æ´ar shewa ta yi ta ce

"Wallahi har ka bani wata Æ´ar bazawarar dariya, haba Malam in da sabo ai na saba, wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, ni kishiyata ai in ban manta ba ina ga goma sha takwas kenan" Da sauri Malam ya ce

"Goma sha takwas fa kika ce?" Tana gyaÉ—a kai ta ce

"Ƙwarai ma kuwa" Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce

"Tabbas na tuna haka lissafinki yake, wallahi na É—auka goma sha bakwai ne, ashe fa sai da na auri Ladiyo sannan na auro Kuluwa, da yake Ladiyo kwanan ta uku a gidan nan muka rabu shi ya sa nake mantawa da ita a lissafin matan nawa...

Haule ta tari numfashin sa da faÉ—in

"To ka ga kuwa wacce aka yi wa kishiyoyi goma sha takwas mai zai ɗaɗa ta da ƙasa? Ai ni ƙarin aurenka shan ruwa ma ya fi shi wahala"

Wani murmushi ya yi sai dai Kuluwa da ta hayyyaƙo masa ya sa maganar da ya yi niyyar yi ta maƙale, tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu ta ce

"Daman ya za a yi ta damu, ai kishiya ko sau dubu aka taɓa maka sunan ta kishiya, kuma dole za ka ji ciwo, ai ta san cewa ba ita za a yi wa kishiya ba ni za a yi wa shi ya sa bata damu ba" Haule ta haɗe rai ta nuna Kuluwa da yatsa ta ce

"Ahir ɗinki ki fita idona in rufe kuma hawainiyarki ta kiyayi rama ta, domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa ni ba kanwar lasa ba ce, sannan bakin rijiya makaho ba ya yin wasa a wajen!" Tana kai wa nan ta juya tana kallon Malam Nura ta miƙa masa tafin hannu ta tana faɗin

"Bani sallama, wato kuɗin toshiyar baki na faɗar kishiya" Kamar wanda yake jira ta tambaye shi da sauri ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa ya ciro dubu ɗaya ƴan ɗari biyar-biyar guda biyu ya miƙa mata guda ɗaya ta karɓa ta juya, ta nufi ɗakinta, Kuluwa yana miƙa mata ta ce

"Dan tsiya naira É—ari biyar ce kuÉ—in faÉ—ar kishiyar?" Yana mata kallon kin rainawa kanki hankali ya ce

"In za ki karɓa ki karɓa ki rage zafi, saboda wannan ma na bada mai yawa ki tambaye ta ki ji wataran idan zan ƙara aure klin nake bata ƙanana ƴan naira hamsin guda biyu kuma ta gode mini" Ya faɗa cike da ƙafafa.

Haule wacce take dab da shiga É—akin ta juyowa ta yi ta ce

"Ai idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, kai kake batun klin ai wannan an bani da daraja, ai in ban manta ba akwai lokacin da ya bani ƙuli-ƙulin naira hamsin lokacin zan yi kwaɗon yakuwa na tambaye shi kuɗin ƙuli-ƙuli ya ce bashi da kuɗi da ya fita ya siyo ƙuli-ƙulin hamsin ya kawo min ya ce in karɓa a matsayin abin faɗar kishiya, lokacin da zai auri Hafiza ƴar gidan ƙanin mai gari, haka na karɓa na masa fatan alkairi, ni da kike ji da gani na ga jiya na ga yau kuma zan ga gobe a cikin gidan nan, ba a banza ba kowace mace take zuwa ta tafi ta barni" Tana kaiwa nan ta bankaɗa labulen ɗakin ta ta shige.

Malam Nura ya dawo da kallonsa kan Kuluwa ya ce

"Idan kin ji ana damo sarkin haƙuri to Haule ce shi ya sa duk auri sakin da nake yi saki ba ya biyowa ta kanta saboda ba ta ɗaga mini hankali idan zan sake aure... Kuluwa wacce tun lokacin da ya ce zai je wajen amarya mai jiran gado ranta ya ƙara ɓaci, tana ganin wato ita yanzu ta zama amarya mai murabus sabuwar amaryarsa ce mai jiran gado, kamar ta kai masa duka ta ce

"Wato shi ya sa ka ce za ta je wajen amarya mai jiran gado, wato an samu sabuwa ni yanzu na zama tsohon hannu, ka gama shanye mangwaro ka yi jifa da shi ƙudaje su baibaye shi ko?"

Yana wani ƙanƙance idanu irin na ɗan duniya ya ce

"Ƙarya na yi?"

Baki ta saki ya layar mai tafiya, kafin ta samu zarafin bashi amsa ya miƙa mata ɗari biyar ɗin, da sauri ta warta tana warta ta yayyaga ɗari biyar ɗin wajen gida takwas ta yaga, da sakakken baki ya bi ta cike da mamaki ya ce

"Kin yi wa kanki amma dai ki sake tabbatarwa aure babu fashi"

Cike da masifa ta ce

"To ni ka sake ni, ba zan iya zama ba"

Yana mata dariyar kin rainawa kanki hankali ya ce
Chapter 1 · 0% Book details