Sashe 96
Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Abida,wajen azahar sai ga su ya Aisha da kololin abinci kala kala lemuka daman da ruwa tun jiya aka Sauke su nan da nan aka fara Cin abinci Daman tuni kowa yayi wanka ya Shirya kansa Yakaka da Safe gidan Baba mallam ta koma tace bazata iya ba ta bar ma su Abida gidan su shakata.. Abun da ya bama Amina mamaki Sai ga Sa"adatu da ya Sadiya har da ya Jidda sun zo mata suna abun Sai da ya bata mamaki ammh bata nuna ba ta Saki Fuska suma sauran yan"uwa suka karbesu hannu Biyu da suna Dari Dari Daga baya suka shige Cikin yan"uwana ana ta Hiran masu Ciki su ya Abida da su ya Zeenatu har ya Zulaihat duk ciki garesu su ya Ikram kam yama tsufa tana ta fama dashi Chan da yammah sai ga su mariya da Samira yan makarantar Haddarsu Amina baki ta rike tana kallonsu tace"Su Mariya ne da su Samira. ! Suna dariya Mariya tace"Wlh mune su Amina..! Sai dukkansu sukayi Dariya Hamida ta Fadama mariya Dayake suna Chart ai sukace sai sunzo sun ga Amina da abunda ta haifa aiko sun sha kallo Amina ta zama zara aciikin wata Duk inda tabi ita ake kallo ta zama abun Sha"awa kuma duka taron Saboda itane nan suka Hade dasu Hamida suna ta Hiran baya da irin abubuwan da suka faru Lokacin suna makaranta Har Sa"adatu ta shige Cikinsu Dayake abun na malamai ne ba Kida ba wani Hayaniya ko Hotuna ta wayoyinsu suka taru yan"uwa suna ta Daukan kansu ya Danmallam kuma yayi walima achan masallacin Baba mallan anyi wa"azi sannan an ci an sha an raka yara da addu"a da Fatan Allah ya rayasu. Aliyu na Tare dashi a matsayinsa na Amini sai su ya jafar da suka Dawo Daga wajen aiki da yammancin ranar tunda matan suna chan gidan Amina sai suka Sauke gajiyarsu Shashen Mallam nan sukaci abinci suka cigaba da Hira. Aliya kuwa sai haba haba take da Amina abu kadan tace Amina kaza amina na yankwanata sai da Hanne ta mata mgana Amina ta mata wani kallo kafin tace"Ke ni fa na tsani Cusa kai..Ni ba kawartace ta kama kanta..! Hanne tace"Kodai yaya ne ki mata uzuru ai don ke tazo.! Amina ta bangaje Hanne tana Fadin"Naji..! Hanne ta Bita da kallo Baki Bude akwai Hallayan Amina da Har Abada bazata iya sauyasu ba ance Hali ai Zanen Dutse ne. Su mamaki ma ta basu da suka ga suna mgana da Sarood Cikin Harshen Labarci wayar Sarood din DanMallam ya Kira yace ta kaima Amina saboda ya yi ta Kiran wayanta bata Dauka ba Shiyasa ta kawo ma Amina ta karba sukayi mganar yace ina ta Jefar da wayarta tace bata sani ba suna cikin kaya mganar komawarsu asibiti yayi bayan yace mata sun yi mgana da Hajiya in sukaje kawai za"ayi ma yaran kaciya ne su Huta Amina tace ba Matsala Duk yadda suka yanke har ya bata Aliyu ya kara mata barka Sannan sukayi sallama ta fita Falo ta Nemo Sarood ta bata wayarta.. Hamida ce sai da tayi mgana ta kalli Amina sanda ta shigo Tana Fadin"Lalle Matar ya Danmallan kece kika kware da Labarci haka sai yarata kuke ke da yar Balarabiyar kishiyarki..! Amina ta harareta Saboda su Sa"adatu na wajen yasa batayi mgana ba ammh ina ita ina wani Sakin jiki da Sarood ai kishiya sunanta Kishiya duk da tana da Kirki ammh dai kowa yayi ta kansa abunda ya faru agidansu ai Ishara ne ga masu sakarma Kishiya Ragamar gidansa da ya"yansu duk da ba Duka aka taru aka zama Daya ba akwai nagari acikin na banzan ammh Dai na banzan su sukafi yawa. Sai dare ya Danmallam suka zo da Aliyu da su ya Jafar suka Dauki yaran su ya Aisha na fadin ayi ma yaran alkunya Danmallam yace kul..Da Mallam da Aba za"a dinga kiran su sune alkunyansu Daganan sai suka ja bakinsu sukayi Shuru ranar dai gidan Amina ya Cika da Baki duk nan suka kwana Ya Danmallan kuma da Abokinsa Dakin su Nazeem suka kwana.. Washegari wasu har sun yi shirin komawa irin su ya Zulaihat Sai ga Sakon mallam zai yi mgana dasu Dukkansu anjuma sai tafiya ta fasu kowacce ta Share waje ta zauna aka cigaba Da Hira Saboda an Haadu ba"a son Rabuwa da juna...gidan Amina aka kawo kan ragunan da aka gyara suka Dafa suka ci sannan Naman kuma achan su Mamata suka soya sai da aka musu nasu tunda dagachan aka Rabasa yadda kowa zai shaida harta Aba da Baba mallam an yi musu kullin su na Nama Anty Hadiza kuma ita tayi Yajin jego,zuwa yammah duk sun gama gyara ma Amina gidanta Yakaka ta Dawo ita tayi ma ma Amina wankan yammah ko kafin mangariba duk sun watse sun koma gidan Baba Mallam har su Hanne Amina da Farko Har da sa Rigiman ita ma sai taje Yakaka tace da Danyen Jegon ne zata fara yawo Dole ta Hakura ta koma tana ta Faman gunguni. Achan gidan ya Danmallam kuwa Ana Idar da Sallar Isha"i mallam ya Hada Taron daya ce za"ayi Sannan har da su ya Nazeem da Uzairu sun iso aranar dukkansu mallam ya kira su yace yana som ganinsu gabadayansu suna Falon mallam illah banda Amina da ya Akila da bata samu zuwa ba sai ya Jadwa. Ammh harda su ya Danmallan suna wajen,Aliyu dai sun tafi dazu da yammh shi da Aliya,Sai su ya Jafar da ya Nasir ya Nazir shima bashi wajen Tunda bai samu zuwa ba sai Aba sai Jawaad har Anty Hadiza da su mamata mallam yace su shigo Tunda Tunatarwa ne ya kamata suna wajen.. Nasir ne ya Bude taron da addu"an sannan Mallam ya fara jawabinsa da Farko Yayi musu wa"azin riko da Zumuncu da yadda zasu Hada kansu waje Daya su zama Dangi Daya kamar yadda yake fata sannan ya gangaro kan wa"azi kan shirka da azaban da Allah yayi tanadinsa domin masu Hadashi da wasu,Tunda ya fara mgana suka Fahimci inda ya Dosa sai jikin kowa yayi sanyi bai fito ya Fada musu Sakin daya shiga Tsakaninsa da Uwani da Marliya ba ballatana ta Bangaran Aba yadai gyara Zama ne ya Fara karanta musu muhimmancin Uwa ga ya"yanta sannan da irin yadda Annabi ya Fadi Darajan uwa. Mallam ya kallesu Daya bayan Daya kafin ya Cigaba da Fadin"Ita uwa tana Daraja da kima..Annabi ya ambaci abi uwa sau uku kafin yace abi uba kunga ko ta haka kadai ya isa kusan Tasirin uwa..Sannan duk lalacewar Uwa uwace..Domin ta Dauki Ciki na Tsawon Wata Tara ta sha wahala kafin ta Haifi abunda ke Cikinta ga azaban Radadin Naguda wanda aka Fadama cewa acikin Azaban mutuwa ne aka Dibosa kadan..Kuma dukkanku kusan mutuwa tana zafi da azaba Saboda Alokacin da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam zai bar Duniya Sai da ya ce Lalle mutuwa tana da zafi tana azaba da magagi Annabi ma kenan wanda ya kasance Shugaba ne na Hallitun Duniya ya Dandana azaban mutuwa ballata mu bayi da kowa kowan ba..? To acikin wannan azabar ne aka Dandana ma uwa wajen Haihuwa bayan ta haihu kuma ta fara Wahalan shayarwa da Reno walwalun duniya akanta suka kare taki ci taki sha Duk domin ta inganta rayuwarka Sannan ta Jajirce wajen tarbiya bata barci Saboda ganin ta inganta Rayuwarka komai lalace uwa komai nata kan ya"yanta ne,kuma komai zata aikata mai kyau ko mara kyau ne to bazata Fara Duba kanta ba sai ta Duba ya"yanta ku Saki ranku ku Bude zuciyarku..Ku sani Cewa Uwa ta wuce wasa komai ta Zama awannan Duniyan bai kamata ta Fuskanci Tsagwamma da Kyama awajen ya"yan data Haifa bq ..Ko kuwa kowa zai gujesu bai kamata ku ya"yansu ku juya musu baya. !