← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 105

Sashe 54

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin Satin kamar yadda Danmallam ya Tsara jirgi ya fara yo gaba da kayansu saboda yayi ma iyayansa da matansa siyayya musamman ma Amina Komai ya gani sai yace zai ma masu Ciki kyau harda kayan jarirai masu kyau duk ya siya ammh bai bari Sarood ta gani ba sannan yazo da Ruwan Zam zam mai yawa saboda mallam yamai mgana yana so da Dabinio sai sauran abunda ba"a rasa ba kuma bai sanar da kowa shi da Sarood zai taho ba sai dai agansu kawai.
Kwana Biyu Tsakani kayan suka iso Jafar da Nasir suka je Filin jirgin Kano suka karbo kayan Direct Gidan mallan akayo da kayan Dakin Hajiya Daman kowa yasan in irin wannan ya faru kayan da komai Shashen Hajiya ake ijiyesu kafin ya Danmallam din ya sauka.
Sakina ana chan ana shiri miji zai Dawo tayi gyaran kai tayi kunshi Sannan tayi gyaran jiki da na chan Shawaran Aliya ne ita ta Hadata da mai kayan matan ta siya awajenta.
Miji kawai take jira ta riga ta gama Shiryawanta.

Ko Amina in sukayi mgana in ta tambayeshi yaushe zai dawo sai yace ya kusa bai saka mata rana ba,yaki gayamata ranar da zai dawo so yake ya bata mamaki sai dai ta ga ya Kirata da Layinsa na Nageria.
Haka kuwa akayi Ranar laraba suka sauka da karfe sha biyun Dare,kwana Biyar da sau kan kayansu suka iso a kano jirgi ya saukesu saboda Dare ne yasa bai kira kowa ba suka samu Tashar Mota shi da Sarood sai jakar kayansu suka nufo gumel sai wajen Biyu da wani abu na Dare suka iso gidansa ya wuce kai Tsaye sai dai Sakina taga Bakin Dare sai murnanta ta koma Ciki ganin Sarood sai da ta nuna afuskantar duk yadda taso ta boye hakan Sarood ko Cikin Murna taje ta Rumgume Sakina Tana Murnan ganinta....
Sakina tayi yake kawai tana Tunanin yadda Umar ya maidata banza ai bai gayamata kafarsa kafar matarsa ba Tana jin dadi ta gagari Amina Zama agumel shine zai jajibomata wannan Sakaryan.
Dakin da aka bama Amina ta Zauna Sarood ta shiga sai dai yanayin Dakin da sauran kayan Amina Data gani yasa tasan an zauna adakin Saboda Gajiyan Hanya da kuma Dare yasa sai da Safe ta ma Sakina Zencen tunda suna Dawowa Umar Dakinsa ya nufa yayi wanka ya kwanta Sai barci sai da Safen suna kari Sarood ke tambayan sakina kayan waye tagani adakin ta..?
Sakina Cikin kissa ta ke sanar da ita kayan Amaryan sa ne Amina nan ta Zauna Sarood ta kallesa sai dai batace komai ba ammh ranta ya baci meyasa Sai Dakinta baga Dakinsa ba..?
Sannan wato ita aka raina meyasa bai ce ta Zauna Dakin Sakina ba..?
Kwafa tayi har suka gama karyawa batace komai ba Sakina sai jin Dadi take yi ranta Fes domin da asuba sai da ta ribaci Umar yayi wani abu da ita kuma taga Chanji Sosai yadda ya rikice mata sannan karin jin Dadinta yadda ta zuga Sarood Cikin Ruwan Sanyi batare data gane ba Tunda ita Sakaryace shi kuma Danmallan kunu yasha baisan wata mgana yasan Nufin Sakina tunda ba yau ta saba raina ma Sarood din hankali ba.
Ganin yadda ya Hade rai ne yasa Sarood din bata yi mganar ba Sai dai Daga yanayin ta sha ka matuka da Kishi Sosai.
Suna gama karyawan suka shirya suka suka nufo Gidan Mallam Jafar ya Kira yazo da mota ya Daukesu daman Tun shekaranjiya an san sun iso
Gida ya Rude da Murnan dawowarsa Gabadayansu har da Matan nasa duka Shashen Hajiya suka fara Sauka Har Sakinar domin ba hanyar da zata fara wucewa Shashen Anty Amarya ganin yadda ya Tsare gida..
Gabadaya matan mallam har da Anty Amarya nan shashen Hajiyar sukazo musu maraba su Hajiya Uwani kada aji labari sai barin jiki take yi Danmallan kallon Anty Amarya kawai yake yi yana Tuna labarin da Amina ta sanar dashi bai san Dalili ba sai yaji bai yarda da ita ba Tun balle ma ganin yadda take ta Kiftama Sakina Ido tana so su kebe suyi mgana ganin wannan balarabiyar da bata san da Zencen zuwa da ita ba, yana ganin su yayi kamar bai gani ba.
Nan ya barsu ya tafi falon mallam shi da Nazeem suka hadu da Aba suka gaisa basu Dade ba suka tafi gidan gona ya Dade shashen mallam suna kara Tataunawa .
Fitarsa ne ya bama Sakina Daman sulalewa ta koma Shashen Anty Amarya suka kebe Anty Amarya Cikin Bacin rai tace"Sai naga kuma wannan Sakaryan. ?
Sakina ta tabe baki kafin tace"Nima yadda kika ganta haka na ganta..Ashe da ita zai taho..!
Anty Amarya tace"To me kika fahimta da Zamansu tana nan a Hotonka ko kin Fahimci sauyi. !?
Sakina tace"Anya..?nidai ban Fahimci komai ba..!
Anty Amarya tace"To ki saka musu ido duk nasan aikin mallam na Dadewa yana Tasiri..!
Da toh sakina ta amsa mata suka Ciga da Kulle kullen su tana bata Labarin Tambayar da Sarood tayi na wacce ta Zauna Adakinta da abunda Sakinar tace mata Anty Amarya na Dariya tace"Gwara da kika fadamata haka..Sakaryan sai ta bisa da tsiya..Ai Amina ba zaman gidanki ba ma Mijin da garin gumel gabadaya ne ya gagareta. waya gayamata Barno gabas take..!
Sakina Tayi dariya kafin tace"Wlh kamar fa anyi ruwa an Dauke ko mganar fa bayayi..!.
Anty Amarya tace"Ai bazai yi ba..Wayama sani ko auran ya Dade da Mutuwa fasawa ne ba"ayi ba kada aji kunya su Hajiya an yi Zani an yi Riga. !
Sakina tace"Zai iya yuyu wlh Anty..!
Allah ma yasa hakan ne..!.
Ta amsa mata da Ameen suna Dariya Ranar dai suna gidan har Dare wannan karon Sarood Shashen Hajiya ta Zauna tare da su Hanne tunda suna gida basu da Jarabawa wannan karon Sakina taji Haushin zuwa da ita da akayi yasa bata jata ajiki kamar baya ba
Sai Dare suka koma gida,Washegari shi kadai yazo su suna gida Shashen Hajiya ya yada Zango aka Bude kaya ya bama Hajiya Tsarabanta na Turaren da Hijabin larabawa na mata sai Dogayen riguna guda Biyu masu kyau da Tsada da takalmi haka ma Anty Amarya da Haj.Nasara da Haj.Uwa dogayen riguna da Turare,Wannan karon har Hanne da Hamida yama Tsaraba domin bazai manta da kaunar da Amina ke musu ba, waya goma sai ta ambace su shiyasa daya siyo mata suma ya siyo musu Ya kuma nuna mata tsaraban Amina da Siyayyan kayan Jariran Da yayi,Hajiya Taji dadi sosai ta dinga yabawa sai dai Bata ga Tsaraban Mamanmu ba Tunda Har Aba ya yoma Tsaraba Sai alokacin ya tuna ma da ita Har ga Allah bai yi niyyar bata bane kawai Saboda tundaga Labarin da Amina ta basa yaji matar bata kwanta masa ba sai bai nuna ma Hajiya ba yace ya manta ne sai Hajiya tace bari ta bata Cikin nata.
Sai ta hada mata da Ruwan Zam zam da Dabino.
Hajiya ta aika ma su Haj.Nasara da Tsaraban Danmallan suna ta godiya haka su Hanne suka yi ta Tsallen murna,Ganin har dasu a Tsaraban Hamida da Hannen ma suka kai ma Mamanmu nata ta karba tana ta godiya da Santi tana auna kanta in tayi ma Aba kwaliya da ita..
Mallam dai Turarensa ne na Arab sai Zam zam da Dabino.
Tsaraban sakina gida yakai mata nata Sai jin Dadi take yi ganin har da takalma ga kayan masu kyau da Tsada
Na Amina kuma wajen Hajiya ya barsu su hanne kuwa tunda suka ga basu ga Amina ba kwana uku da Dawowar ya Danmallam ba labarin Dawowar Amina sai suka cire rai da Mganar Hajiya da kullum take sanar dasu Amina zata dawo nan kusa sai suka Sare..
Gashi har sun yi nisa a jarabarwarsu suna gabda gamawa gabadaya sai basa jin Dadin zama,ba Amina suma sun yi ahuru kamar basu agidan da ko da Amina ke nan wlh sai su shiga gidan mallam sau goma gidan Aba ma haka Rashin jinsu kawai yasa Dole ma asan dasu ammh yanzu sai a kwana awuni ba ba"aji ko motsinsu ba.
Islamiya da Boko ma an gaji da Cigiyar Amina Daga baya ma su Hanne cewa kawai sukayi an cireta Daga mkaranta bata agarin harta mariya abokiyar fadanta da malaman makarantarsu Mallam Datti da kansa ya Kira mallam ya tambayesa Amina Mallam yace mai Amina bata gari ne shiyasa..!

Kwana hudu da dawowarsa Ranar yazo Gidan da Safe Ya shiga shashen Hajiya suka gaisa da sauran matan Sannan ya koma wajen mallam to basu Dade da Mallam ba aka kirasa agidan mai anguwa Idi ya tafi kaisa Aba kuma baya nan sai ya tafi Dakin Nazeem ya dan kwanta ya Huta Sarood Tun abunda Sakina ta Fadamata take shamai kamshi sai bai Biye mata ba Sakina kuma kamar rana Daya zai mata Ciki takuranta ne ya Ishesa,yake barin mata gidan ita da Sarood din su ci kansu.
Amina kuma tun washegarin ranar daya sauka daya Kirata bayan ya saka Layinsa na nan ya fadamata ya Dawo suka gaisa har take fadamai sun je asibiti ta fara awo sannan an mata Scan,basu wani jima suna mgana ba yace zai sake kiranta,kuma bai Samu Lokaci ba,Basu zauna sun yi mgana da Hajiya bane yana so yaje ya ganta kafin ya koma tunda ba wani Dadewa zai yi ba Sati Biyu ne zasu yi,zasu koma.
Chapter 54 · 0% Book details