Sashe 91
Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajen kwana Biyar Aba yana cin Amarcinsa hankalinsa kwance ya samu natsuwa da Anty Hadiza fiye da yadda ya Tsammanin samunta. Bai taba zaton balaraba tana cikin gidan nan ba, bata kara gaba ba,saboda Dakinta yana rufe ne sannan bata fitowa yayi zaton tayi ma kanta Hisabi ne ta kara gaba Acikin ransa kuma wannan kuncin da bakinciki da Tsanar Balaraba baya jin zasu sake shi nan kusa yana jin har duniya ta Nade bazai iya Yafe mata ba. To shi kanshi baisan tana cikin gidan ba,ballatana Anty Hadiza da bata Dade agidan ba,Sai ranar kwana na shida ne Wari ya rika fitowa Daga Dakin da Kakarin mutum kamar zai yi Amai Lokacin Aba ya fita gidan Gona Anty Hadiza ke tsakar gida tana Shara taji wannan abun sai hankalinta ya tashi ta tsorata sai dai bata bar kiran sunan Allah ba Mayafinta ta Dauka ta je gidan mallam Shashen Hajiya ta gayamata abunda ke faruwa ita kuma Hajiya ta Sako Hijabi ta Biyo bayanta. Koda suka zo Dakin yana rufe ne ta Ciki ba yadda zasu yi su shiga sai an balle kofar sannan Hajiya tana da Tabbacin Balaraba na ciki Saboda ai ita tayi waya da yan gusai a manganganunsu bai nuna balaraba ta koma chan ba sannan tana da yakinin kunya da Nadama ne suka sakata ta kasa fitowa kamar yadda ya Kanannaye Marliya itama ko Kamshinta bamai ji itace ma Sarkin Tsausayi take umartan su Lami da in sun gama girki su shigar mata dashi Cikin Shashenta kada yunwa ta mata Illah. Hajiya mallam ta kira awaya bai yi nisa ba yana makarantar Haddar su Amina suna taro yace ga shi nan zuwa Daganan sai ta kira Aba tace ya Dawo gida shi har ya rude ya zata ko wani abu ne ya faru da Hadizar shiyasa yazo Hankalinsa tashe ko kafin ya kariso Mallam har ya dawo sannan ga Jafar ga Nasir su suka kira mai Balla kofa kafinta yazo ya Balle kofar Gabadayansu sai da suka toshe Hanci suka samu shiga Dakin Halin da suka Iske Mamanmu aciki Dole bawa ya kara Tsoron duniya.. Tana kwance a kasa inda ta Fadi Jiki ya jirkice Baki ya karkace Anan tayi kashi da Fitsari bazata iya tsshi ba Idanuwanta sun kafe saboda kuka sannan ta galabaita da yunwa da kishi Tana ganin Hasken rana ya shigo ta Fara laluban inda zata Hango mutane sai idonta ya koma yana ganin Duru Duru bakinta ya bushe ba"a kajin me take fada sai mgana take yi ba wanda ya Fahimta ashe ruwa take fadin a bata Anty Hadiza ce ta karkata kunnenta har taji abunda take fadi ta Ruga Kitchen ta Dauko ruwa Tsausayinta har ya kamata Idanuwanta ya ciko da Hawaye ta kasa ma Daga kanta ita kadai kuma ba wanda ya taimaka mata hakanan ta Zuba mata ruwan wani ya shiga Bakinta wani kuma ya Zube a kasa. Hajiya ta kalli mamanmu ta kara kallanta kawai sai ta gyada kai ta Girgiza kafin tace"In bawa bai ji Tsoron wannan rayuwar ba yayi asara..Allah ka Tsare mana Imaninmu..! Aba ko na tsaye yana kallonta aransa yana jin Dadi samnan yana mata Fatan abunda zata gani sai ya fi haka Ya Jafar ko nadaga bakin kofa bai ma kariso ba domin in akwai Hallitar Daya Tsana to ya ga mamanmu ne yanzu nan komai zai Dawo mai acikin kansa Nasir ne ke gefen Aba Mallam kuma Duke yake gaban Mamanmu ya kasa mgana Acikin ransa kuma Kabbara da Kirari yake ma Allah yana Tunanin yaushe bawa zai gane cewa Duniya ba matattaba ne. ? Yaushe zamu san cewa rayuwar nan tana cike da tashin Hankali ne..? Kai ya girgiza kafin yace"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un..! Haka kawai yake fada Aba kuma kawai sai ya juya baya zai fice Daga Dakin Mallam ya Daga kai ya kallesa kafin ya kira sunansa shiyasa ya Tsaya kafin ya Juyo yana kallon Mallam din. Mallam ya mike yana Fadin"Ina zakaje..? Baka ga Matarka cikin wani mawuyacin Hali bane..? Kallon Baba mallam yake yi Cikin mamaki kafin ya cije baki yace"Balaraba ba matatace bace..Tun Ranar da nagnee ita wacece na Tsinke saura igiya biyun Dake Tsakanina da ita..! Mallam ya jinjina kai Daman so yake ya tabbatar da hakan duba da yadda Sa"idun bai kara Tadamai da mganar ba,Hajiya tace"To yanzu ya za"ayi da ita..? Aba zai yi mgana kenan Mamanmu ta fara zakuda jikinta tana kuka tana mgana bamai gane me take fadi Sai da Hajiya ta Duka da warin Dake fitowa Daga Jikin Balaraba haka ta Daure tana Fadin"Me kike son kice Balaraba..? Cikin Daba daban mgana tace"Kuu u....yaaaa...fee ee..min..! Sai Hawaye Daga gani ta gama galabaita Hajiya ta Dago tana kallon su Aba kafin tace"Yafi yar ku take nema Sa"idu ni dai na yafe miki balaraba haka ma mallam..Sai dai Sa"idu da yaran nan..! Aba ya juya kawai yana Fadin"Har Abada bazan iya yafe ma wacce ta Cutar da rayuwata ba..Da yardan Allah kin fara gani kenan kafin ki Mutu sai Allah ya Dandana miki azaba mafi muni akan abunda kika aikata muguwa kawai..! Daga haka ya fice Daga Dakin a Fusace Jafar ya mara mai baya domin shima bazai iya yafe mata ba Anty Hadiza na gefe tsausayi duk ya Cikata sannan ta kara jin tsoron rayuwa da Duniya gabadaya. Ba wanda ya iya taimaka mata cikin wannan Halin suka barta Hajiya da mallam a falonsa suka shiga suka Zauna mallam yayi jigum Domin har yanzu abunda ya faru bai sakesa ba,Hajiya ma Tagumi kawai tayi tana kara Jinjina al"amarin kafin ta Daga kanta tana kallon Mallam cikin wani yanayi Tace"Mallan yanzu ya zamu yi da ita..? Ayadda Sa"idu ya fice bazai taba Sauraran kowa ba..! Mallam ya Sauke Numfashi kafin yace"Nima abunda nake Tunani kenan..Bazan taba takura ma Sa"idu akan wannan al"amarin ba kamar yadda ban takura ma kaina ba..Zan Kira chan gusai na Fada musu Halin da ake ciki yan"uwanta da suke Dolenta su zo su tafi da ita..! Hajiya ta jinjina kai alamun gamsuwa nan take ya kira Kawu salisu bayan sun gaisa ya Fadamai abunda ke faruwa shima Dagachan barayin yace kadan ta gani sun yi mgana kan zai Fadama yan"uwanta gobe zasu zo su tafi da ita Domin ta fara girban abunda ta Shuka ne da wuri. Bayan sun gama wayar Hajiya tace"Ya kuka yi dashi..? Mallam yace"Yace zai fadama yan"uwanta gobe zasu zo su tafi da ita.! Hajiya ta Sauke Tagumi kafin tace"AllAh ya kyauta..! Mallam ya amsa da Ameen Cikin wani yanayi Hajiya ta gyara zama tana Fadin"Mallam ya batun yaran nan..?. Kasan dai uwa ba abun wasa bane sannan duk abunda iyayansu suka aikata basu isa su sauyawa Tuwa suna ba..Na lura daga ya"yan Balaraban har na Uwani da Marliya tun da abun nan ya Fallasa suka gujema iyayan nasu kana gani Harta Umaima ina jin yan"uwan sun fadamata tana shashena ko Damuwa da uwar ma batayi ba..! Mallam na jinta kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Me kike so ayi..? Hajiya tace"so nake ka kira su kayi musu nasiha kan Muhimmancin Uwa awajensu sannan su yi hakuri su yafe musu su tallafesu domin su kadai ne yanzu suka Rage musu..! Mallam yace"Zan yi musu mgana Insha Allahu. ! Hajiya tace"Ya kamata gaskiya..! Gani tayi mallam na nemsn shigewa Ciki yasa ta kallesa tana Fadin"Mallam ya batun Uwani da marliya..,? Gwara Uwani tana gidansu Marliya kuma ta nan ko Fitowa batayi nine ma nake saka su Lami suna shigar mata da abinci..! Mallam ya Dakata yana kallon Hajiya kafin ya koma ya zauna yana Fadin"Duk da Sakin aure ba Dabi"ata bace..Ammh kuma ya zama Dole ne Bazan iya Cigaba da zama da Uwani da marliya a matsayin matana ba..Dukkansu zan tsinke igiyan aure koda Dayan Dake Tsakanina dasu ne Su je na yafe musu ni ban taba Cutar dasu ba..Allah suka ma Laifi sunemi gafara a wajensa..Zan samu Lokaci naje chan Tsafe gaisuwa zan sanar ma ita Uwani marliya ma zan sanar da ita abunda na yanke..! Hajiya sai taji wani iri sai dai tasan mallam ya tsorata da wannan al"amarin yasa kawai tace"Allah yasa hakan shi yafi zama alheri su kuma Allah yasa hakan ya Zame musu izna..! Ya amsa mata da Ameen kafin yace"Me Saratu take yi agidan nan ne..? Bata koma gidan mijinta ba..? Hajiya tace"Na tambayi Danmallam din yace min yamata mgana ta koma taki tace ya barta anan..! Mallam yace"Wannan mganar banzace..Bazai yuyu ba Dole yayi adalci Tsakanin matansa Raba musu kwana zai yi Saboda yayi adalci a Tsakaninsu ki Fadamata ta shirya ta koma Gidan auranta zan kira Umarun zan mai mgana..,! Hajiya tace"Shima yaso ta koma itace taki..Kasan ita kadai ce yanzu ko Rashin Sakina agidan yasa taji wani iri..! Mallam yace"Ita Sakinar tana chan Dutsen kenan wajen Danginta..? Hajiya tace"Eh sadiya ta fadamin tun washegari suka Dauketa Daga asibiti suka tafi da ita..Ta kara barin cikin nata ne.. Mallam ya jinjina kai kafin yace"Allah ya kyauta na gaba..Shi ya matsayin auran nasu da Sakinar..? Ko baku yi wannan mganar dashi ba..? Hajiya tace"Bai taba min wannan mganar ba..! Mallam ya koma ya jinginar da kansa Jikin kujera yana Fadin"bari zan Tuntubesa naji..Bazan mai Dole ba Sai dai zan bashi Shawara a matsayina na Uba a wajensa..Ina Fatan abubuwan da suka Faru su zama izna garemu da yan baya..Sannan ina Rokon Allah ya Tsaremu da zuru"armu gabadaya Daga Fadawa Halaka..! Hajiya ta amsa da Ameen Ameen basu wani Dade suna mgana ba ta koma Shashenta ta bar mallam zai kwanta Saboda tun faruwar abun nan bai wani Cikin natsuwarsa abun ya tabasa sosai,Ita kanta sai a Hankali ta gama tsorata da Duniya da mutanen Cikinta Har ita kanta Nasara sai ahankali gidan gabadaya sai yayi kamar ba kowa,shuru kowa kumazaka gansa baya cikin Walwalarsa. Hajiya bata yima Sarood mgana ba Illah ce mata tayi taje mallam na nemanta Sai da taje ne Mallam yayi mata Nasiha Daga karshe yace tayi Hakuri ta koma Gidan mijinta ta zauna kafin su tafi ta tabbarar mai da Insha Allahu zata koma sannan ya Sallameta Kai Tsaye kuma ya Kira Danmallam yace yazo yana nemansa Tun da yammah bai samu zuwa ba Sai Dare saboda Rigimar Amina wai sai yazo da ita bazata iya zama ita kadai ba yasan in