← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 105

Sashe 13

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Amina bata san wainar da ake toyawa ba,sai da ta gaji da barci sannan ta tatashi shima kiran sallar azahar ya tasheta da ake ta kwalawa a wani masallaci dake kusa dasu sannan ta iya tashi gabbanta duk sun gaji Tsami ma kafafunta ke mata sosai,Dakyar ta iya mikewa taja jiki ta shiga Tiolet ta Sha ruwa a famfo sannan tayi alwala tazo tayi sallah sai dai kuma yunwa take ji,Ammh duk da haka bata fita ba ta koma ta kara nadewa a Tunaninta Sakina zata kawo mata kamar yadda ta saba sai har wajen uku saura na Rana bataji motsin kowa ba cikinta har ya fara Curewa waje daya yana mata Rugugi.
Tunawa da tayi sakina ba Imani gareta ba Daga ita har megidan sai su barta ta mutu basu da asara shiyasa ta mike ta taimaki kanta kayan datayi amfani dasu da safe ta Dauka ta fita zuwa Falo tana leken sakina sai dai bata ganta ba ko motsi ma babu agidan.
Bata gama mamaki ba sai da taga Kitchen a rufe sannan Hankalinta ya tashi,Sai alokacin ta Lura duka Dakunan suna kulle ne mamaki ya kara kamata to ina yan gidan suka shiga ne..?
Tabe baki tayi daga baya aranta tace ina Ruwanta dasu sun dade basu tafi ba suma shekara waya damu..!
Nan saman Dining ta watsar da kofin da Filet din,kamar zata koma daki sai wata zuciyar tace mata bafa kowa agidan ki sha iska tuna haka yasa ta koma falo ta samu kujera ta zauna tana kara bin Falon da kallo tana nazarinsa baki ta tabe ko ajikinta.
Sauran buredin data rage da Safe ya Taimaketa shi ta Samuka ya cikamata Ciki,Har barci ya Dauketa nan saman kujera bata sani ba sai bayan La"sar ta tashi tayi mamakin irin barcin Datake yi kwana biyun nan,Tashi tayi ta koma Daki tayi sallah sannan ta kara fitowa Ciki dai ba abinci shiyasa duk ta kasa sukuni Allah ya taimaketa a saman Dinning Sakina ta manta da kayan Tea su Amina ta samu ta sha da Ruwan Sanyi tunda ba na zafi ta kuma Samu katon Buredi a wajen ta hada dashi taci ta koshi tayi Dam ta koma Daki aranta tana fadin kafin su dawo nayi barci Domin ni bana Tare da yunwa..!
Sai dai kuma har akayi mangariba bata ji Duriyar kowa ba sai Hankalin Amina ya fara tashi Har sake fitowa tayi ta Duba ba wanda ya Dawo ta koma ta zauna tayi Tagumi sai kuka tana Tunanin yadda Sakina da Mijinta suka zama marasa imani suka tafi suka barta ita kadai agida wannan Rashin Imani ne Allah ya isanta Bata yafe ba in wani abu ya sameta su da Allah..!
Bata kara Tsorata ba sai Dare yayi Amina tsoro ya cikata gashi nepa sun Dauke wuta Duhu ya cika gidan ita kuma batasan inda ake kunna Solar ba batama san da ita agidan ba,Ga shi Daga waje Hadari ya Hadu Farkon Damuna,sai ta kasa zama itace Dakin ta ko falo ta kasa zama sai ta zauna motsi kadan dataji sai ta mike tana waige waige ta fara Firgita sai kuka Amina Bilhakki da gaskiya take kuka saboda Tana tsoron saukan ruwa barin ma in ana iska ko tsawa,tana wannan kukan aka fara iska mai karfi winduna na kadawa da Labulai sai Amina taji kamar ta yi iska ta ganta agida Bayan mamanmu ko Hamida saboda tsoro Daki ta koma ta Dunkule kan gado tana Kuka Lokaci daya da makyarkyata Idanuwanta a kulle gam bata so ma ta bude ga ko"ina duk Duhu Hankalinta gabadaya ya tashi banda Salati da wayyo wayyo babu abunda take yi.
Adaidai Lokacin aka tsuke da ruwa mai karfi kamar da bakin kwarya,Ga iska ga Rugugin Tsawa Amina ta rasa ina zata sa kanta taji dadi gabadaya ta Tsorace,ta kamkame jikinta waje daya,ta tusa kanta cikin Filo tana rufe kunnuwanta ga iska sai kada winduna yake yi da Labulai kamar zasu balle Fitsari kamar Amina zatayi a wando Saboda Tsoro hawaye kuwa ya wanke mata fuska da majina bata sanin ma sanda yake fitowa wani na Fitowa wani na Kara fitowa.

Adaidai Lokacin Adaidaitan da Danmallam ya hau daga Tasha zuwa gidansa koda ya fito rike da Jakarsa sharkaf yake da ruwa,har diga yake yi sai rawan sanyi yake kudi ya bama mai adaidaitan baisan ko nawa bane Saboda yayi mai Hallaci tunda suka sauka atashar Gumel aka fara Ruwa shi yana da Allagis din Ruwa ya tabasa komai kankantarsa sai yayi mura da Zazzabi in ma bai kwantar dashi ba yayi ta taran masu adaidaita suna cewa baza su shigo Cikin gari ba Dakyar wannan ya Daukosa ganin yana rawan sanyi Ganin irin kudin Daya basa ne yasa ya Leko yana fadin"Nagode yallabai Allah ya kara Budi..!
Da kai ya amsamai lokaci daya ya wuce zuwa Bakin get din gidansa ya kwankwansa har sau Biyu shuru Wayarsa ya ciro a aljihun wandonsa yaga ta Mutu daman ba chaji tun suna Filin jirgi Take buga Battery low,sannan kuma ga ruwa ma ya tabata domin sosai ta jike,Kara buga Get din yayi Allah yasa Buzun megadin yaji ya fito da sauri ya leko lokaci Daya yana haskasa da Fitilansa mai Haske ganin Danmallam da kansa yasa Cikin mamaki yake kallonsa bai Damu ba yace ya Budemai get da Sauri ya Budemai karamar kofa ya shiga gidan megadin ya bisa yana tambayansa bai samu tafiya bane..?
Eh kawai yace mai lokaci Daya ya Nufi Kofar da zata sada sa da Falon gidansa so yake ya samu yayi wanka da Ruwan zafi ya kwanta,jikinsa kamar ba Nasa ba.
Sai da yana shiga Duhu ba Haske abun ya bashi mamaki yana Tunanin ko Sakina ta kwanta ne kafin a Dauke Wuta ba"a kunna Solar ba,Isa Cikin Falon yayi ya isa inda makunnin Solar yake ya kunna Haske ya gauraye duka gidan falon yake bi da kallo ganin sa Tsab ba kuma Hayaniyar kowa Bai Damu ba ya kama Hanyar Dakinsa sai dai kuma me..?Sai yaji sa a rufe Mamaki ya kara kamasa sai ya Nufi Dakin Sakina yana kiran sunanta nan ma yaji kofa a Rufe bai kawo bata nan ba ya fara mata knooking yana Kiran sunanta ammh Shuru..!
Chapter 13 · 0% Book details