← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 105

Sashe 92

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yazo da ita sai ya shafada wajen Hajiya kamar yadda akayi Ranar shiyasa ya zauna ya lallabata Dakyar da Sharadin bazai Dade ba Sannan ta barsa ya fito. Sai da suka Idar da Sallar Isha"i sannan Suka gana da mallam a Falonsa mallam bai nuna mai ya san wani abu ya tambayesa zaman me Saratu take bata koma gidansa ba..? Sai ya karantamai yadda sukayi da ita Mallam yace"Wannan ba Hujja bane Umaru..ita macece kai kuma Namiji ne Shugaba..Kada ka manta adalci ne aikinka Tsakanin matanka..Kada ka bari Daya ta Rinjaye ka domin Ranar Lahira zaka tashi da Barayinka daya ne yana Rinjayan Daya. kada ka Duba wai Tare kuke achan duk wannan ba Hujja bace..Zaka raba musu kwana ne har Lokacin da zaka koma shine adalci..! Danmallan kansa na kasa yana gyada kai bai ce komai ba Mallam ya Cigaba da fadin"Na kira ta na mata mgana saboda haka yanzu ka Dauki matarka ku tafi gidanku..Allah ya zaunar daku lafiya..! Danmallam sai Lokacin ya Dago kansa yana Fadin"Naji Duka mganar ka mallam..Sai dai ina so kamin afuwa Zuwa gobe da zan cika Sati Daya awajen Amina sai na koma wajen Sarood din..!. Mallam ya kallesa kafin yace"Shikenan daman na Tunasar Dakai ne..Itama akwai Hakkinta akanka Umaru kuma ina yi maka kwadayin Zama mutum adali Allah yayu muku albarka ya wajen ita mamar tawa..? Fata dai ba wata Damuwa ko..? Danmallam yace"Lafiya lau mallam..! Daga haka shuru ya Biyo baya sai Danmallam din ne ya gyara zama yana Fadin"Mallam daman ina so nayi ma Hajiya mgana..Yakaka kakar mijin Aisha da bata koma ba tunda sun shaku da Aminar me zai hana ta koma chan Gidan Aminar su zauna tare..Ga Halin Datake ciki sannan in ina gidan Sarood bazan dinga Fargaba ba..! Mallam acikin Ransa Hamdala yake yi Saboda yaga kaunar Mamar tasa a cikin Idanuwan Umar. Kai Tsaye yace"Kayi Tunani mai kyau..Kada ka Damu zan yima Hajiyar mgana gobe sai ta saka Idi yakaita Yakaka akwai kirki da karamci Sosai shekaran jiya ta na nan har Dare muna ta hira da ita..! Danmallam yayi godiyar har ya mike zai tafi Mallam ya saka Baki ya ka kirasa ya Dawo ya Durkusa a gabansa Mallam ya kallesa Kafin yace"Ya mganar Ka Da Sakina..? Naji har yanzu baka ce komai ba..Sannan kana jin labarin Halin Datake ciki domin an ce ta kara rasa wannan cikin shima..Allah ya kyauta na gaba..! Danmallam kansa na kasa yace"Mallam ni bansan komai ba tadai Kirani Sau biyu shekaran jiya ban Dauki kiranta ba..! Mallam ya gyada kai kafin yace"Kaje kayi Tunani Umaru..Duk abunda ka yanke sai ka sanar dani..Ammh ina so ka Sani ka Bude zuciyarka Dakyau ka gani ko zaka bama Sakina Dama har ga Allah ina Tsausayinta domin Sharrin Marliya ne ya koma kanta Barin Ciki ga mace abun jin Zafi ne..Sannan abubuwa Dadama ba Laifinta bane..Kayi tunani kagani ko zaka iya yafe mata..Ban takura maka ba..Shawara ce Tsakanina Dakai..! Danmallam kansa na kasa yace"Nagode Mallam Insha Allahu zan karbi mganarka..! Daganan ya sakamai albarka sukayi sallama ya fito,Shashen Hajiya ya Shiga suka gaisa da yakaka da Hajiya nan yaga ma ya"yan Goggo Yagana sun zo wato yan"uwan Anty Hadiza sun kawo mata kayanta dake chsn da wasu Dake Dake daga mahaifiyarta Dazu da rana suka iso shiyasa bai Dade ba suna gaisawa yayi musu sallama ya fito a haraban gidan suka Hadu da Aba suka gaisa sun dan Taba Hira sama sama kafin ya shige motarsa ya bar gidan shi kuma Aba Falon mallam ya shiga. Koda ya koma Amina ta cika kiris take jira tayi kuka,Allah ya tsaresa da Jidalinta shiyasa ya kasa gayamata Zai koma wajen Sarood har washegari Suka je asibiti da Duka Fayel dinta na Aaibitin datayi awo a Abuja wajen Dr.Ghali suka je inda ya Taba kaita Farko al"amarin. Dr.Ghali nata mamakin wannan al"amarin Sha"awa suka basa har ya kasa Dauke ido Daga kansu ganin yadda Amina ke shagwaba Umar na Biye mata ya Dubata yace ba matsala Sai dai Jininta yayi Low sosai taci kayan ganye,Daga asibitin Da suka Dawo suka sake fita da kafa suka Zagayen anguwan saboda kafaduwan Amina su Saki suna Dawowa ba Dadewa sai ga Idi ya kawo Yakaka Murnan sai ya Dauke Hankalin Amina har ya sake wanka ya fita bata Damu ba. Koda yaje abakin Hajiya Yaji abunda ya Faru da Maamanmu da Labarin yan"uwanta yau sun zo sun Dauketa tana Fadamai irin yadda Duniya ta juyama Mamanmu abaya har ga Allah bai wani Tsausaya mata ba,Aransa ma yasan Kadan ta fara gani Da yammah ya Dauki Sarood suka koma gidansu batare daya Fadama Amina ba saboda bai son me zai ce mata Amina yadda take da kishi ya Tabbata in ya Biye mata sai ya shiga Wuta. Ganin yanayin Sarood din itama tana Fama da Laulayin jiki yasa ya Zage ya taimaka mata suka gyara Gidan suka share ko"ina Girki kuma yace kada tayi ta kwanta ta Huta zai taho mata Dashi Daganan Gidan mallam ya koma sukayi sallar Isha"i sannan yayi musu sallama ya nufi gidan Amina ya Iskesu afalo ta baje suna ta Faman Hira da yakaka Sai Hankalinsa ya kwanta.. Yana shiga Daki ta Biyosa Lokacin yana ta Tunanin abunda zai ce mata tana shigowa tace mai bari tayi Fitsari ya Bita da kallo Tana tafiya Dakyar ta Shige Tiolet sai ya fita Falo ya samu Yakaka ya roketa tayi ma Amina bayani ya kasa Yakaka tace kada ya Damu yayi tafiyarsa zata fadamata Tsorin Jidalin Amina yake yi shiyasa Daganan bai koma Falon ba ya Fice Tana Fitowa taji karan Rufe get dinsa ta kalli Yakaka tana Fadin"Hubby ya Fita ne..? Yakaka tace"Ya koma gidan Yar"uwanki chan zai kwana..! Tafada tana Hade rai tasan Halin Amina gwara a mata Zafi Zafi Amina taji dan Cikinta ya motsa da Sauri tace"bangane ba..? Ina kenan..? Yakaka tace"Mallam yace ya Dauki matarsa su koma gidansu wannan balarabiyar kinga ai tunda suka zo tana gidan mallam ke kuna ba kuma Tare da shi anan ba..? Sai Amina ta koma ta Zauna akasan Cafet ta Rushe da kuka tana Fadin"Shine ko yagayamin..Ya kama Hanya ya tafi wajen wannan banzar matar tasa..? Yakaka ta saki Baki kafin tace"Yau naga Tsiya..ke da zaki godema Allah miji na sonki Yan"uwansa kowa naji Dake..Ita wacce kike kishi akanta uban wa ma ya Damu da ita Labarci nan dai kinsan ba kowa ke jinsa ba..Bata da wani Sakewa kamar mujiya ki godema Allah bawan Allah nan na tafe rawan jiki akan ki ke bakya gani kina wani shanshanci ke kika sani..! Yakaka ta karishe da juya mata baya tana cire naman Daya makale mata a Hakori da tsinke domin Amina ta bata na zamani tace ta rabata tayi da wanda ta sani Amina mganar Yakaka bai sa ta Daina kuka ba Domin wani Kishi ne ya Rufe mata ido har wani Duhu Duhu take gani sai da ta gaji da kanta ta Daina gani kuma Yakakar tayi mata banza ta cigaba da Harkokinta yasa ta tashi da Turtsetesn Cikinta ta koma Dakinta ta kwanta tana Sauke Numfashi Yakaka ta Bita da kallo kamar tayi Dariya
Chapter 92 · 0% Book details