← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 105

Sashe 19

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsawa tayi ammh bata Dago ba shima bai Damu ba cikin Taushin lazafi yace"Abunda ya faru Tsakaninmu Sirrinmu ne ko..?
Yafada yana kallonta kanta na kasa bata yarda ta Dago ba ta gyadamai kai Cikin jin nauyi shima ya cigaba da Fadin"Yauwa to kuma kinsan duk wanda yake fadan sirrin aure Allah zai kona sa ko..?
Ba kyau nasan an fada muku a islamiyanku ko..?
Nan ma kai ta gyada mai kafin ya cigaba da Fadin"To ina so abunda ya Faru Tsakamin mu ya tsaya iya mu Biyu..Kada ki sake ki Fadama kowa kin jini ko..?
Sai alokacin ta Dago ta kallesa suna Hada ido tayi saurin maida idonta kasa shima Fuskewa yayi kafin yace"Kin ji ko baki ji ba Amina..?
Cikin sanyi tace"To Allah fa..?
Ai ya sani ko..?
Mamakinta ya kamata sai bai nuna mata Cikin yanayinsa yace"Eh Dagani sai ke sai Allah..Daman ai shi yana Sama kuma yana kallon Duk abunda muka aikata..!
Bana so ki fadama kowa..Koda Hajiya ce ko mallam ko Aba ko Hannatu da Hamida. !
Kai tsaye tace"Harda Mamanmu..?
Da Sauri yace"Har da ita kada ki Fadamata in kuma kina so Allah ya Konaki Ranar Lahira shikenan..!
Yafada da sigan ya Tsoratarwa Amina mamakinsa ya kamata me ya maidata ne..?Sauma kiramana shashasha kenan..! Da bata san me take yi ba da zata bama wani wannan Labarin mai kunyar Fada ita ba Haka take ba ko da ya ganta yarinya tana da wayau..!
Shi a dole zai mata wayau sai abunda ya bata Dariya har sai da ta Murmusa kafin tace"naji insha Allahu bazan Fadima kowa ba..!
Jinjina kai yayi Cikin jin Dadi kafin yace"Good naji Dadi..Ki kula da kanki kinji ko..?Kirika wanka sau uku ko Biyu arana sannan ki rika shan mganinki kin ji ni..?
Nan ma kai ta gyada mai ba Zato kawai taji ya saka mata kudi a Hannunta ganin yan Dubu Dubu yasa ya Zare ido kafin tayi mgana ya mike yana fadin"Ki rike su a hannunki..Ni yau zan koma..!
Zaro ido Amina tayi kafin tace"Ina..?Madina..?
Kai tsaye yace mata"Eh tafiyar ma bata yuyu bane da Tuni na tafi..Jafar zai kawo miki waya zamu rika mgana ..!ina dai gargadinki kada ki Fadama kowa..!
Amina bata ma jinsa Tunaninta na kan yadda zata zauna ita kadai agidan nan gashi bata san ina gajeran matarsa taje ba tun ranar bai kara mganarta ba..kafin ya ankara Amina ta Fashe da kuka cikin mamaki yake kallonta kafin yace"Kukan me kike yi..?cikin kuka tace"Wlh bazan iya zama agidan nan ni kadai ba Tsoro nake ji ka maidani gida..!
Kai Tsaye yace"Nima  naso hakan sai dai  Hajiya da maallam bazasu bari ki koma ba..!
Amina na Jan majina tace"Gidammu zan koma bazasu sani ba..!
Dariya mganarta ta basa da sai ya Dara kafin yace"In jiwa..? ai da gidanku da gidan mallam Duka Dayane Dole zasu sani..Ki daina kuka zan kira Hajiya ko Hannatu sai tazo ta Zauna Dake kafin Sakina ta Dawo..!.
Jin sunan Hanne Daya ambata yasa ta bar kukan ta Dago tana kallonsa kafin tace"Da gaske..?
Kai ya gyada mata wani mikewa tayi kafin tace"Yauwa harda Hamida don Allah ya Danmallan kaji..?
Ashe tasan sunansa kallonta yayi kafin yace"Wato ku hadu ku fara rashin ji ko..?
Kin san dai yanzu ba da bane ko..?
Da Sauri Amina tace"eh wlh babu abunda zamu yi..!
Kai ya jinjina mata kafin yace"Shikenan sai su zo..!
Tsalle ta Daka tana Hawaye tana Dariya zafi taji a kasanta yasa ta Duke tana Wash wash Kallonta yayi kafin yace"Ki rika kula da kanki fa..Kina da Sauran Rauni..!
Bata Dago ba ta mikamai kudinsa tana Fadin"Babu abunda zan yi da kudi..!.
Shi kuma yace"Ki rike a hsnnunki. zaki koma makaranta Dis Coming monday ki rika yin kudin Break sannan in kina Bukaar wani abu in Sakina ta Dawo ita zaki rika tambaya kina jina ko..?
Kai ta gyadamai ammah aranta tace Tab wannan matar muguwa din.
Afili kuma cewa tayi"Allah ya kiyaye hanya..!
Ya amsa da Amen yana kallonta kanta ya Dafa kafin yace'Allah yayi miki albarka..Na tafi sai in kuma na Dawo..!
Sai kuma taji kamar kar ya tafi yana mata Kirki na kwana Biyu wayarsa ya Dauka anan wajen kayan kallo ya Fice ta rakasa da kallo sai da ya Dade da Fita sannan ta koma ta Zauna da kudi a Hannunta tayi Tagumi haka kurum taji kamar kar ya tafi sai dai kuma taji Dadin da su Hanne zasu zo Dadi ya isheta.!
Shi kuma yana Fita Tasha ya wuce Direct Allah ya taimakesa ya samu Motar kano ta kusa cika ita ya shiga kuma Motar nada Lafiya sun yi gudu kuma koda biyar tayi yana Filin Jirgin Aminu kano,bayan yayi sallah ne ya kunna wayarsa ya Kira Hajiya..

******

Hajiya na Cikin Bedroom dinta tana Duba littafin 40 Rabbana Hanne na Tsaye awajen Wardrope dinta tana gyara mata kayanta Jiya mai wanki da guga ya kawo wayar Hajiya Dake kan madubi ta fara kuka alamun kira Hanne tafi kusa da wayar yasa Hajiya tace ta miko mata.
Tana Dauko wayar tace"La Hajiya ya Danmaallam ke kiranki..!
Hajiya ta ijiye abunda ke hannunta kafin tace"To ya natsa kenan tunda ya kira..!
Bata Tsaya Duba lambar ba ta Daga Kiran Lokaci Daya tana amsamai Sallamarsa cikin Sanyinsa ya gaisheta ta amsa tana Fadin"Kun sauka lafiya..?Mallam nata kiran ka bai samu ba Nima har da Safe na gwada layinka nachan ban samu ba..!
Cikin Taushinsa yace"Hajiya ai ban tafi ba..Sai yau ne zamu tafi jirgimu zai tashi da karfe takwas na Dare. !
Hajiya ta Bude baki kafin ta Dago wayanta tana kallon Lamba sai Lokacin ta Lura lambarsa ta nan ne saboda ta chan Danmallam2 ta sakamai.
Cikin mamaki tace"Ikon Allah to meya faru ba wanda yaji labari don ko da Safe Jafar ya shigo nan nake tambayansa yace shima bai samu wayarka ba..!
Umar yace"Matsalan hazo ne Hajiya shiyasa tafiyar bata yuyuba aranar..!
Hajiya tace"To Allah yasan hakan shi yafi Zama alheri..!
Ya amsa mata da Ameen kafin yayi shuru itama jinsa shuru yasa bata yi mgana ba sai da taga bai da niyar mgana sannan tace"Danmallam lafiya kuwa..?ka kira kuma kayi shuru..?
Ya sosa kansa kafin yace"Hajiya ina Filin jirgi kanon tun dazu..!
Hajiya tace"Madallah Allah ya Tsare..ya wajen su Aminar ina Fatan Lafiya ko..?
Cikin Kasa da Murya yace"Suna lafiya Hajiya..Daman zence ne in ba Damuwa Hannatu da Hamida su tafi yanzu su je su zauna da ita gidan ba kowa..!
Hajiya tace"Bangane ba kowa ba Sakinar fa..?
Kai Tsaye yace"Bata nan Hajiya..!
Bata Damu da tace ina taje ba tace"Allah ya kyauta..To yammh tayi kuma mallam baya gida sannan Gobe jumma'a suna da makaranta Danmallam..
Kai Tsaye yace"Hajiya kiyi hakuri su bar makarantar ta gobe su je su kwanan mata Biyu..In sakina ta Dawo Shikenan sai su dawo gida..kinga tayi kankanta da Zama ita kadai.. sannan ita ma Ranar monday sai ta fara zuwa makarantar..!
Hajiya tace"Shikenan bari na Tura su yanzu Daman na bari ne sai Asabar sai su hakura da Haddar su je mata tunda kuma ga wannan laluran bari na nemi ko Uzairu ne ya kai su sabod maallam da idi ya fita..!
Danmmallam yace"Uzairu ya Dawo ne..?
Hajiya tace"Eh jiya ya Dawo..!
Kai Tsaye yace"Hajiya ki basu keys din gidanan su tafi dashi..!.
Hajiya bata da bin Diddigi kai Tsaye tace shikenan daganan sukayi sallama ta bisa da Fatan isa Lafiya..tana gama wayar Hanne data kasa kunni taji ta cikin jin Dadi tace'Hajiya wajen Amina zamu..?
Hajiya ta mike tana fadin"Eh da naso sai jibi ne ammh yace kuje yau sakinar bata nan..!.
Hanne ta Daka Tsalle tana Murna Hajiyw tace"Daman na gama Hadamata komai jiya ma kinsan a kawo Dinkunanta da mallam yayi mata Sabbi yanzu shiga gidan Sa"idu kice ma Balaraba zaku wajen Amina in tana sako ta bada..!
Ai da gudu Hanne ta fita Tana murna Hajiya kuma ta fara Hadaa Sabbin kayan da mallam ya Dinkama Amina kala goma da Hijabai sai ita kuma ta mata Turaran wuta da Humra sai Dambun nama dasu Samosa duk an yi package dinsu sai kamshin girki kala kala har da curry har da su Cake sannan ta Siya mata Sabbin panta da sikat da Vest.
Ba jimawa sai ga Hamida da Hanne kamar bakinsu zai Tsage saboda murna Hamida ta Dauko kayanta kala Biyu Hanne ta bama Hajiya Turaran Tsinke guda Daya a ledansa wai inji mamanmu akai ma Amina..
Hajiya mamaki ya kamata ko jiyan nan Sa"idu ya sake fadaa mata ya bama Balaraba kudi ta yi ma Amina siyayyan abun Bukata shiyasa ta aika mata ammh sai taga wannan abu haka..?
Abun ya bata mamaki ace wajen Amina fa za"aje koda Sa"idu bai ce ya bata kudi ba ta Dauka kayan da zata Hadama Amina sai yafi ma wanda ta Hadamata ammh sai bata saka kokonto aranta ba ta barshi a kila bata siyan mata bane tukunah sai Daga baya..!
Hajiya batace komai ba ta Hada Cikin kayan sannan ta Dauko musu keys din gidan ta basu sannan tace Hanne ta Diban ma Amina sinasir din da sukayi da Miya su kai mata jiki na rawa suka Diban mata a coolers suka saka miya Dabam sai murna suke yi Hajiya ta Jaddada musu ranar  Lahadi idi zai Zo ya Daukesu sannan taja kunnensu da su natsu da sakon su gaida Amina..bata yi gaban kanta ba sai da ta kira mallam sukayi mgana da Farko cewa yayi"Hajiya yara nan su kadai agida kina ganin zai yuyu.?
Kodai Aminar ta dawo gida kawai har Sakinar ta dawo..!
Hajiya tace"Hakan ba mafita bace in mukace haka bazata saba da gidan auranta ba gwara ta zauna watan watarana zata saba..!
Da haka mallam ya yarda da Hujjanta yace su Hamidan su tafi da kanta ta Kira uzairu yazo ya kaisu da Daya daga Cikin motocin gidan Daman tun jiya daya Dawo key din motar ke hannunsa.
Har suka tafi Hajiya bata Daina mamakin Balaraba ita sai kawai taji abun yayi mata wani iri.
Sai da ta koma shashen nata ta ga Sinasir din datace su hanne su dibar ma Amina saboda sauri sun manta dashi kawai ta girgiza tana mirmishi suna ta zumudi dole su manta.
Chapter 19 · 0% Book details