← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 105

Sashe 28

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

hajiya bata samu Tafiya Biki ba sai Ranar alhamis idi ya kai su ita da Hajiya uwa datace zata rakata ba wanda yayi mamakin hakan daman in dai sha'ani na Hajiya ne Hj.uwa tana gaba gaba sanin tasu tafi zuwa Daya da Hajiya babba ba kamar su Nasara da Anty Amarya ba kafin su tafin Jafar ya kawo mata 30k in ji Danmallam ta kar ba tana ta godiya ta nuna ma mallam ya saka albarka shima ya bada kudi da kayan abinci suka tafi dashi Kwana Daya idi yayi ya juyo sai sun gama Biki zai Dawo ya Daukesu
Su Amina sun so Hajiya tatafi dasu tace su yi Hakuri su zauna Saboda makaranta sannan kwana Daya Tsakani Ranar jumma"a Mamanmu ta tafi Gusai Biki Amina da Hamida da Hanne sun so su bita Tunda Hajiya bata tafi dasu ba ammh itama tace su Zauna Saboda makaranta Daman Amina ta ma mallamm gana ya basu Hakuri yace su bari wani Lokacin saboda karatunsu,Dole suka Hakura ammh Tundaga Ranar ganin Hajiya bata nan Amina ta share Kafa Tayi zamanta Daganan suke zuwa makaranta da Aba yayi mgana Mallam yace ya kyaleta watarana ba sai an mata mgana ba zata san muhimmancin gidan auranta har yanzu Amina yarinya ce.
Amina kuma Harkan gabanta take yi kamar ba matar aure ba in ba gidan ta koma ba mantawa take yi da wani aure ballatana Danmallan ko Sakina Abu Dayane bata manta dashi ba Har yau shine Abunda ya Faru Tsakaninsu Ko barci ta kwanta sai ta Tuna abun kunya take ji da nauyi in ta Tuna abunda ya Faru Ranar yau itace kan gado ita da Danmallam har wani babban lamari ya faru Tsakaninsu sannan bazata manta da yadda yagama gane mata jiki bakincikinta Daya yan nonuwamta Daya gama gani Tasan ya gama rainata Haushi take ji nata sunki girma ga Hamida Da Hanne har Hajiya ta siya musu Braziya ita kuma sai vest saboda ba su da wani girma sosai in ta tuna Haka sai ta Tura baki tana kunkuni kamar yana jinta ko yana ganinta.
Yanzu Ta rage tsoro tunda Tare da su Hamida take kwana sannan koda aka shiga Damina ko ana ruwa Tsakar Dare ba ruwanta tana makale bayan Hanne ko Hamida hankalinta kwance.

A jidalinta kam babu abunda ta Rage sai Dambe ne kadai ta Daina ammh Fada a makaranta da siyan fada ko bada ita akeyi ba sai abunda yayi gaba Ballatana gata ga Hamida ga Hanne bata da wani Danuwa ranar ma A Hadda suka yi fada da Samira ta kan kujeran zama Amina ta mike ta Chakume Wuyan Hijabin Samira zata Jata da Dambe Mariya ta kada baki Tace Amina yanzu fa kin girma tunda ke matar aure ce wannan abun da kike yi bai kamata ba..Ku su hanne ku Fadamata gaskiya in zataji to..!
Amina sai taji ta Muzanta Ido ya Dawo kanta sai taji kamar ta Shake mariya ta kalleta ta murguda mata baki kafin tace"Ubanki na aura ammh ko..?
Wannan mganar yasa mariya ta kai kara wajen Mallam Datti akan Amina ta Zagi babanta Case din da sai da ya Jafar yazo makarantar mallam ya aikosa ya kashe mganar Tunda Mallam Dattin ya kira mallam awaya ya Fadamai.
Ranar ya Jafar yaso ya Daki Amina sai Mallam ya hana ya kuma yi musu gargadin  har Abada Amina ta wuce Duka awajensu..ko ba domin darajan auran Dake kanta ba Domin Darajan Danmallam Dake mijinta bazai ji Dadin su daketa ba in yaji Labari.
Ya kuma fada musu suma Amina Uzuri Amina har yanzu yarinya ce dole ya kyaleta ita kuma sai ya Bita da Nasiha tamai alkawarin Insha Allahu bazata kara ba,Daga dai ranar ta kulla Gaba da mariya sannan Sa"adatu ta sha Habaici kala kala Domin ita ta yada Labarin Hanne da Hamida su dai yan bada Hakuri ne Amina bama jin mganar su take yi ba suna dai bata Bakinsu ne.

Hajiya sun yi mgana dashi Danmallam din tana chan maiduguri yana so ya kara mata mgana  ammh kuma ya kasa ita kuma tana Sane ta bari ne sai ta Dawo tamai bayanin abunda mallam yace.
Har Haj.uwa sai da ta Fadamawa itama tace shawaran mallam tayi saboda Kada a rabama Amina hankali Daga karatunta,aranta kuma Tana Tunanin meyasa Danmallan ya Damu da Amina alhalin kowa yasan wannan auran ga yadda yazo sai dai ta kasa sanun amsa.

Sati Daya Hajiya sukayi Idi yaje ya Daukosu suka Dawo Mamanmu kuma sai da tayi kwana goma sannan ta Dawo Amina kuma Hajiya na Dawowa ta Tattara ta riga komawa gidanta tana kwana sai su hadu da Sakina ammh basa ma juna mgana Sakina gabadaya Tsanar Amina take ji Saboda gani take yi komai ya Faru ita ce sila Anty Amarya tace ta cika gajen Hakuri ta Daina kiranta in bata da mgana mai Dadi Ita kanta Anty Amarya a Rude take abubuwa duk sun shagule mata Tafiyar mamanmu Gusai sun hadu a Dutse sun koma wajen malamaminsu ya Tabbatar musu da cewa Umar zai dawo ya tafi da Sakina Sannan Burinta zai cika itama mamanmu ya Fadamata Sa"idu na hannunta sai abunda tace suka Zubemai makudan kudi Anty Amarya ta koma Gumel ita kuma ta koma Gusai saboda kada a Fahimci Tafiyarsu Daya.

********

Umar sunyi mgana da Sarood itama ta yarda kila shafan Aljanun ne suka fara amfani da mganin da ya siyo mata a Islamic Chamet na irin abunda suke Hasashe shima ta bangaransa ya Dake  da Addu"a ammh bai kara Jaraba kusartar ta ba ya bari sai ta gama amfani da mganin sannan.

*Janafty*
[10/31, 8:07 PM] +234 814 039 1977: *TFZB2011*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*
Chapter 28 · 0% Book details