← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 105

Sashe 5

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Afusace ta Buga kofar ta shigo Tana bin Dakin da kallo lokaci daya tana wani yamutsa Fuska nan kasan Cafet ta Hango Amina ta Dunkule waje daya acikin Hijabinta,Ga ghanas dinta nan inda ya ijiyemata ko kauda su batayi ba Ranta ya kara baci Cikin kufuluwa tace"Kee...!
Cikin Tsswa Amina bata jita ba Domin barci ne na wahala ya kwasheta bata sani ba Jiya yadda taga rana haka taga Dare bazata kwatanta kwana awajen da ba Hanne ba Hamida ba bata taba tsamanin wannan ranar ba ballatana ta Shiryama zuwanta Tunda ta shigo Dakin ta zube anan kasan Cafet ko motsi bata karayi ba tayi kukan har ta gaji ga Tsoro Daki ita kadai abunda bata saba ba,Bata iya barci ba Tsoro da Fargaba da kewa basu barta ba Dakyar ta Rarrafa da Asuba ta shiga Toilet din Dakin tayi alwala tazo ta Rama Sallar Isha"in da ake Binta jiya da kuma Sallar asuba shine fa tana nan zaune bata ma san barci ya kwasheta ba.
Sakina jin tayi banza da ita kuma taki Motsi yasa ranta ya baci a Tunaninta da gangan tayi mata yasa ta isa kusa da ita ta saka kafa ta Shureta daya sa Firgigit Amina ta farka Daman a Tsorace take cikin muryanta da Bata Fita sosai saboda kuka tace"Wayyo..!
Sakina ta saki Tsaki kafin tace"Baki ce wayyo ba sai nan gaba..Badai kin ce dani Zaki kishi ba yarinya..Ai wayyo Salamu Alaikum..!
Amina ta bita da kallo da kumburarrun Idanuwanta Hancinta ya Toshe da majina sai ja take ga kuka ga sanyin Dakin Domin A.C a kunne kuma fanka ma haka ita kuma bata yi Hausan tashi ta kashe su ba.
Sakina ta koma da baya tana mata wani kaskantattacen kallo kafin tace"Kazama kawai..Sai ki taso yana kiranki..!
Amina ta kalleta da mamaki kafin tace"Shi wa..?
Cikkn Shakewar murya Sakina ta ga tama raina mata wayau yasa ta juya tana fadin"Uban ki ba..!
Amina ta bita da kallo har ta fita itafa bata gabanta ita yanzu kokuwa take da wannan Sabuwar rayuwar shiyasa Zagin Sakina bai ma Dameta ba kamar bazata je ba Domin jiri take gani in ta mike ammh Tuna Kalaman ya Danmallam yasa ta mike jiri na Dibanta ta fice Daga Dakin zuwa Falo Daidai sanda Sakina taja kujera ta Zauna Dammallam na zaune bai ce mata komai ba sai ga Amina ta fito tana Layi Cikin hijabinta kamar zata fadi Daga nesa ta Tsaya tana kallonsu kafin tace"Gani..!
Daga sama har kasa yake kallonta alamu sun nuna ko mai yarinyar nan batayi ba tunda ga jiya kenan ganin yadda Fuskarta ta Kumbura ne ya bashi mamaki Sakina kuwa Kamar ta yi Tsaki haka taji da taga yana kare ma Amina kallo bata ma lura da kallon kyama yake binta dashi ba..!
Saboda mugunta sai da tafi minti Goma a Tsaye tana neman faduwa sannan yace"kizo ki ga abun kari nan.!
Amina da Tagaji da Tsayuwa tace"Ni na koshi..!
Ko kallonta bai yi ba ya maida hankalinsa wajen cin Doyansa Sakina ta juya tana kallonta ta Harareta bata ma ganta ba ta juya tana Faman Kama Hijabinta ta koma inda ta Fito nan inda ta baro ta koma ta zauna ta Hada kai da gwiwa ta fara Rera sabon kuka Allah sarki sai yanzu ta kara Tabbatama da kanta da cewa tayi maraici tazo inda ba mamanmu ba Hamida ba Hanne,Wadanda sune ita in basu Rayuwar Amina bazata taba cika ba Aminu ne ya fado mata arai ko wani Hali yakeciki..?
Tasan da shi ta aura ta tabbata zai lallasheta zai mata komai Saboda yana sonta ammh kalli inda Kaddara ta kawota inda ba"a san Darajanta ba Daga megidan har matan gidan basu da Imani Allah ya isanta wlh bazata taba yafe musu ba mugaye kawai..!
Tun daga Lokacin Amina ko motsinsu bata sake ji ba tun tana Daurewa har ta kasa Cikinta ya kulle yunwa take ji ga jiri ga rashin barci sai mulmula take saman cafet dafe da Ciki tana faman kuka ita kadai Zata mutu acikin wannan gidan wayyo ita Amina..!
Chapter 5 · 0% Book details