← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 105

Sashe 75

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Mamanmu na tsakar gida suna ta Hidima akazo da labarin Hajiya tace suzo ga Amina ta dawo Mamanmu sai taji kamar bataji da kyau ba badai Amina ba,in ma Aminar ne bata taba Tunanin ganin abunda zataje ta gani ba Saboda mai Fadar bata Fadi cewa Amina da tsohon ciki ta dawo ba. Ana fadin ga Amina ta dawo kowa da kowa ya zura Hijabi har da goggo Husai da su ya Jawahir domin sun yi kewar yar kanwar tasu tarr da mutanen Gusai,har da matan su ya jafar dake gidan tunda chan gidan su Abida suka bar ma gidan su suna nan ana ta aiki dasu. Mamanmu ko Hijabi bata tsaya sawa ba,Zanin goyon Zulfa ne Dake kan igiya ta Rataya sai gidan Baba mallam itace kan gaba so take taga da gasken Aminar ne..? Domin har alokacin gabanta bai Fadi ba bata sare ba ballatana ranta ya kawo mata yau ranar Tonon asiri ce. Sai dai me suna shiga falon sai kallo ya koma kansu Mamanmu bata lura da ko su Anty Amarya ba ballatana Uban kayan lefem Dake zube a falon Hajiya Burinta kawai taga Amina domin ta gasgasta abunda aka Fadamata yasa tana shigowa ta Daga Murya tana Fadin"Ina Aminar da akace ta Dawo..? Amina..! Ta fada da dan karfi domin ita a zatonta karye ne ba wata Amina,Sai dai ga mamakinta wata ta gani kamar Amina ta mike tsaye Dakyar har Yakaka na Taimakamata ta mike Sai ga Cikinta ya bayyana Cikin Ido tana kallon Mamanmu cikin wani yanayin Da ta kasa Fassarashi tace"Ga ni nan Mamanmu..! Tafada da wani Sauti na Rauni Sai taji bata ji kunyar cikin dake jikinta ba Ko Hannunta bata saka ta kare kamar yadda ta saba ba so take taga yadda Mamanmu zatayi in ta ganta da Ciki. Aikuwa Mamanmu ido ta Zaro Jikinta ba inda baya rawa ido ta murza ta kara Murza,kamar yadda su Ya Jalela suka saki Baki suna kallon Amina sun ma kasa mgana. Goggo Husai ce Cikin mamaki tace"Amina..! Tafada tana takawa gabanta Amina sai taji kunya kanta na kasa tace"Ina yini goggo..! Sai goggo Husai ta rike baki ta kara Leka Fuskar Amina kafin ta kalli Cikin jikinta ta rike Haba tace"Ikon Allah Zainabu duk yaushe haka ta faru ba Labari ina tunanin ko Sa'idu bai Tabamin zencen Amina ba Domin da Jadwa ta fadamin bata a gida dana masa mgana yace min kinsan inda take bai taba Fadamin Halin da yarinyar nan take ciki ba..! Hajiya na Tsaye ta murmusa Kafin tace"Ai ko shi Sa"idun bai sani ba..Dagani sai mallan Sai mijinta kadai muka san da wannan cikin Husai..! Gogggo Husai ta kara jinjina kai kafin tace"To ina tayi renon Cikin..? Hajiya tace"Abuja..wajen Aisha na kaita..! Goggo Husai sai ta samu waje ta Zauna tana Fadin"Ikon Allah..! Saboda abun ya bata mamaki ne dayasa kalamanta suka kare,Mamanmu kuma kamar suman Tsaye tayi daga inda take ko motsi ta kasa kamar yadda Anty Amarya da Haj.Uwani suke Dansare a tsaye sun rasa ma wani Tunani zasu yi duk yaushe hakan ta faru..!? Su ya Jawahir kuwa karisawa gaban Amina sukayi suna kiran sunanta sai ta amsa tana gaishesu har da su ya Zulfa ya Zahra suna ta kallon Amina mamaki yasa sun ma kasa mgana ya Zulaihat ne sai da ta Rumgume Amina tana fadin"Allah Sarki Aminene..Aminene ta kusa zama uwa. ! Amina batace komai ba kanta na kasa,nan da nan falon ya kwace me da Hayaniyar mata yan gusai suma suna ta Tofa albarkacin Bakinsu,yan"uwan Amina kallonta kawai suke yi kamar wata Hallita ya Jadwa Mirmishi take yi a kasan ranta Lokaci Daya Hawaye suka kawo idonta afili ta Furta"Yau ina Yaya take..? naso tana raye taga yadda Amina ta koma..Yau Amina ce da Cikin Haihuwa Sannan uwa uba Amina tayi hankali ba mgana ba fada ba tsiwa ba kunkuni madallah da uwa irin Hajiya madallah da Uba irin Baba mallam..Sannan madallah da Gwarzom Miji irin Yaya Danmallan..! Ya Jaleela ta share kwallah ta rike Amina tana fadin"Amina naji Dadin ganinki haka naji Dadi..! Kawai sai ta Fashe da kuka itama Aminar daman kiris take jira sai kuka Yakaka ta riketa ta koma ta zauna tana Fadin"ku daina sakata kuka tana da Lalura sannan kusanta akwai Daman arhan kuka..! Kamar an ce ta kara ne haka Amina ke kuka su Jaleela ma suna Tayata su suna kukan yadda Allah ya inganta Rayuwar Amina ne da kuma kukan Rashin Uwa garesu ita kuma Amina Wani Daci ne acikin ranta in ta Dago tana ganin Mamanmu a gabanta. Mamanmu kwata kwata kamar kunnuwanta sun Dode haka taji Hajiya na lura da ita tayi Mirmishi acikin Ranta kafin ta karisa gabanta ta Dafa Kafadarta kamar wacce Shooking ya taba haka ta Zabura sai kuma taga Hajiya Daga ganin yadda tayi Firgai Firgai sai ta baka mamaki Hajiya tace"Balaraba ki karisa mana ki gaisa da yar naki..Sannan ga kayan Lefenta nan nace baza"a bude ba sai kin zo ke da sauran yan"uwanta..! Mamanmu sai taji kamar Bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana Hajiya taja Hannunta har gaban Amina sannan ta Saketa Mamanmu kafafunta ne suka kasa Daukanta ganin wani irin kallo da Amina ke Binta dashi da shigargun Idanuwanta kawai sai ta Zube agaban Amina ta saka kuka sai kallo ya koma kanta Kuka take yi sosai tana rike da Hannun Amina Fadi take yi"Amina yanzu Ciki kike dashi bansani ba..? Nice fa Mamanki Amina duk duniya ko kowa baisan Halin da kike Ciki ba Ni bai kamata na Sani ba..? Tafada Cikin Karaji da nuna yadda abun ya Dameta Goggo Husai ce tayi mgana tana Fadin"Ke Balaraba to wa ya sani..!? Kina ji ai ko Sa"idu bai sani ba..! Mamanmu sai ta rumgume Amina ta na kuka Fadi take"Amina waya yi miki Ciki..? Cikin waye ajikin ki..? Mganar ta fito ne kamar ma bata san Sadda ta fito ba sai kallo ya koma kanta Cikin mamakin kalamanta Haj.Nasara ce ta kalleta tana Fadin"Ke kam Balaraba da wata mgana kike yi Amina ai kinsan tana da miji..Cikin jikinta kuma ai Jikan mallam da Hajiya ne..! Mamanmu sai ta Dago gabadaya ta Rude idanuwanta ta fara wurgawa Cikin Falon karaf suka hada ido da Anty Amarya Dake tsaye gefenta Sakina ce da Sadiya sai Aliya sai wasu Dangin su Daga Dutse. Kallon kallon sukayi ma juna,kallon da basu taba yima juna ba Mamanmu ta kara tsurewa cikin wani yanayi ta kauda kanta kafin ta kalli Haj Nasara tana Fadin"Ba...Ba sun rabu ba. ? Sai kowa ya Zaro ido yana kallonta Mamanmu sai ta rude ta fara inda inda Tana fadin"A"a na dauka da Hajiya ta Dauketa anan ne..Auren ne ya lalace..! Sai kuma ta kara saka kuka tana Fadin"Amina kece kika koma Haka..? Allah Sarkin kyauta da kari..! Sai kuma ta kara rike Amina wacce in ta riketa kamar wani abun kyama ya Tabata yadda ta Tsani mutuwarta haka ta Tsani ganin Mamanmu shiyasa sai binta da kallon mamaki take yi kamar yadda Hajiya ke gefe tana yi Lokaci Daya tana Sakin mirmishi. Kafin wani yayi mgana su Hanne sun shigo da Ihu suna fadin ina Aminar take..? Amina na jin muryan su Hanne ta Bangaje mamanmu ta mike Cikin Fara"a da Tsantsan murna bakinta kamar zai Tsage tace"Gani nan Hanne..Hamida..! Sai kuma Hawaye Hanne ne kan gaba sai Hamida sai su ya Abida dasu Sa"adatu idon su ya rufe ko Mutanen Falon basu tsaya kallo ba ballatana Cikin jikin Amina suna ganinta Hanne ce ta fara Buga Tsalle ta fada mata Sai Hamida da Zafira wacce dazu tazo Suna murnan ganinta. Kadan ya rage su kadata Yakaka da Hajiya har suna Hada Baki wajen fadin"Ku kula fa..Tana da Lalura..! Sai Sannan sukaji wani abu mai Tauri ya Tokaresu suka Dagota suna Binta Da kallo Daga sama har kasa,cikin mamaki da Budewar Baki Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka kalli Amina Dake sharan kwallah tana kallonsu cikin Annuri fadi take"Nayi kewarku..Nayi kuka nayi kukan kewarku kamar ba gobe..! Tafada tana dora kanta saman kafadan Hanne Lokaci Daya tana rike hannuwan Hamida Zafira dake gefe Ta leka Amina tana fadin"Amina..? Amina ta kalleta tana yar Dariya tace"Na"am zafira..Zafira..!. Tafada Cikin dariya da Hawaye zafira ta jingina da kafadan Amina tana Fadin"Itace.Wlh Amina ce..! Tafada tana Dariya,Amina ta rikesu kamar ta samu salama bakinta yaki Rufuwa Hanne ta Taba Cikin Amina tana kallon Hamida kafin tace"Hamida Wlh Ciki ne ajikin Amina..! Taba kiji..! Hamida itama ta taba Cikin kafin ta kalli Hanne tana fadin"Ciki ne..Amina Zaki Haihu ne..? Sai Amina ta kasa mgana ta Buge hannunsu tana fadin"Bansani ba..! Tana hararansu Lokaci Daya kawai sai suka Bushe da Dariya ga hawaye na Binsu suka hada Baki wajen fadin"Wlh Aminene ce..! Suka koma suka rumgume juna gabadayansu suna Hawaye suna Dariya kowa afalon sai da yaji kamar yayi musu kuka ya Abida ce da ya Zeenatu suka matso kusa ya Abida ta Dafa su Hanne tana Fadin"Dillah ku matsa ai Aminar bataku ce ku kadai ba..Har damu..! Suka saki Amina suna Dariya Amina ta Daga baki Cikin Murna tace"Ya Abida..! Tafada Cikin murna kawai sai tace"Na"am Aminene..! Sai suka rumgume juna suna mai Farinciki haka ma da ya Zeenatu ta Shafa kumatun Amina tana fadin"Allah mai iko Amina ba Fada ba tsiwa..Agaida ya Danmallam..! Amina ta sunne kai tana Dariya Goggo Husai tace"Ai rabon dake tsakanin su ne yasa auran yazo Cikin gaggawa..Allah ya Rubuta wannan Rabon ajikin Amina yake..! Mamata mahaifiyar Zafira tace"Kwarai Rabo ai bai bar komai ba..! Yakaka ta amsa da cewa"Ai yana ma kisa..In aka hanasa bayyana sai ya kashe rai..! Hajiya na gefe tana ankare da motsin kowa tana dan Mirmishi sai alokacin tayi gyaran murya tana fadin"Ku Dakata da wannan murnan ga lefen Amina nan da kayan Haihuwarta..Sannan akwai gidanta da Mijinta ya siyamata an zuba komai aciki Yana Babura Road zuwa gobe in an watse taron Amare sun mika za"a raka Amina Gidanta nan zata Haihu tayi Jegonta kafin tayi Arba"in Mijinta ya Dauketa su koma inda yake aiki..! Hajiya Nasara ta zabga Kabbara ita dasu ya Abida,Ya Aisha na Dariya jin Yakaka na fadin"Kwarai Hajiya. kafata kafar Takwarata sai garin ma"aiki..! Hajiya nasara ce ta fara Bude kayan su ya Jalela na Tayata su hanne na kamkame da Amina
Chapter 75 · 0% Book details