← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 105

Sashe 47

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Sati Daya da Tafiyar Amina Abuja acikin Satin Dayan data yi a garin Abuja karo na farko tun da take ta fita garin gumel taje wani waje da sunan Zama na wani dan lokaci.
Alokacin da Hajiya ta mata mganar zuwanta Abuja ta shiga Damuwa,Da kuma Tunanin zatayi zaman kadaici ba hanne ba Hamida sannan inda bata Saba ba sai gashi kuma Cikin kwanaki da zuwanta Abuja ta Saki jikinta sosai da garin Musamman ma da Yakaka data kasance mai kirki da Dattako Sannan Aisha ma na iya Bakin kokarinta sosai akan Amina abaya Amina tasan ya Aisha bata da Hayaniya sosai da yawan mgana ammh yanzu haka zata zauna tayi ta jan ta da hira suna tuna irin Rashin ji da su kayi ita dasu hanne Tana bama Yakaka Labari itama Dayake sunan Amina gareta ake ce mata Yakaka tace ai masu suna Amina haka suke yarintarsu an sha kwallo sannan haka suke basu Daukan raini su taru da Amina su yita yabon masu sunansu Nan da nan Amina ta Saki jikinta Dakin Yakaka ma take kwana yanzu Saboda bata son kwana ita kadai yakaka tace ta dawo Dakinta su Zauna tare itama ta samu abokin zama.
Haka kuwa akayi sai da ya Aisha taga Amina ta kwashe kayanta takai Dakin Yakaka suna Zamansu lafiya batayi mgana ba saboda ko bakomai yakaka Zata kula da ita sannan ga Ciki ajikinta tana Bukatar wani a kusa da ita.
Usman mijinta ya Dawo ya ga Amina har sun gaisa saboda yasanta abakin ya Aisha lokacin tana amarya in kewar gida ya isheta sai ta Zauna ta rika basa labarin kannenta Amina da Hamida da Hanne sannan yasan mganar auranta da ya Danmallam din Tunda sukan yi mgana da shi Lokaci bayan Lokaci haka Itama Aminar tasan Usman sun taba ganinsa Sanda yazo wajen ya Aisha kafin auran sannan sun gansa ranar Daurin auran shiyasa dukkansu basu Tarbi juna abaki ba..
Achan gumel kuwa Hanne da Hamida sun gaji da tambayar Hajiya ina takai Amina..! Sun kyaleta saboda bata gayamusu sai dai tace Amina na nan Dawowa insha Allahu sun Damu Matuka,Ammh kuma Dole suka hakura sai dai kana ganinsu kasan sun rage walwala Sannan a makaranta ko an tambayi Amina cewa suke yi tayi tafiya,Hamida har mamanmu tama mgana ko tasan inda Hajiya takai Amina..?
Mamanmu tace bata sani ba tadai san Hajiya tace ma Aba bata wuce Tsakanin gidajen yaran gidan nan ko na gidan mallam ba,ita duk a Tsammaninta bata wuce Tsakanin gidan Jawahir ko Jalela ba tafi ma Tunanin Jalela saboda tayi mgana da yan Gusai kuma bataji Labarin Zuwan Amina ko Hajiya abakinsu ba ita bama wannan ne agabanta ba shiyasa bata Damu da tasan Inda take ba,Saboda kada azargeta da rashin kula da Jawad yasa ta jawosa ajiki ganin yana neman yaki Zama wajenta ya koma wajen Hajiya Hamida kuma ganin ba Amina sai ta Dawo kwana agidansu tana kula da kanta da jawaad tunda Daman Amina ta bar mata Amanarsa to shima ganinta yasa bai Damu ba Duk da shima ya gaji da tambayar ina ya Amina..?
Sai dai Hamida tace mai tayi tafiya ammh ta kusa Dawowa..
Sun kusa fara jarabawar Fita nan da Sati uku hanne da Hamida suna Zaton Amina Zata dawo kafin su fara jarabawa Tunda Hajiya bata sanar dasu komai ba.
Sakina ta koma gidanta mallam yace Tunda taji Sauki ta koma Gidanta ta Jira Mijinta Dole ta tattara tatafi ammh Sai da ta roki mallam ya bata Sa"adatu tatafi da ita sai yace sai dai Tatafi da Sabeeha tunda ta gama primary zata shiga Jss1 kafin a sakata to da Sabeehan ta koma bayan mallaminsu ya Kira Anty Amarya ta koma wajensa ta Zubaimai kudi ya bata wani kullin mgani yace Sakina ta sha da Ruwan Zafi duk abunda Uwani ta bata taci ko ta sha Zatayi amansa ko Tayi kashinsa Domin ya tabbatar ma da Anty Amarya wani abu ne Aka bama Sakina taci acikinta..
Haka kuwa akayi ranar data sha mganin kwana tayi tana Zagayawa har safe ta Kira Anty ta Sanar da ita Tana jin haka Cikin farimciki tace in Sha Allahu nasara tasu ce.
Tsakaninta da Haj Uwa kuma ko mgana basa yi sai agaban idon da bai san tsakaninsu ba kamar mallam da Hajiya da Suke Dauka bata san boyayyin Fuskokinsu ba..Ammh in suka hadu su Biyu su harari juna sannan kuma kowacce ta wuce tana ikirarin sai taga bayan yar"uwanta.

*****

Achan Madina kuwa Danmallam dai da Sarood balarabiya suna ta gwangwajen amarcin su sosai fa ya Saki jiki yana Morewa Saboda ai ya Dade Rabonsa da mace tun Kan Amina wannan kuma ai ya Daukesa a matsayin Rabo ne shiyasa daya samu wannan Damar yake ta amfana da ita Domin Daman Daurewa kawai yake yi Yana fama da azumin Litini da alhamis saboda kariya da Tsare kansan.
Ita kanta Sarood din sai alokacin tasan ta yi aure sai kuma ayanzu tasan tana kishin Mijinta ada kamar bata Damu da kishin Sakina ba ammh yanzu da tasan waye Umar sai taji har Sakina ma tana matsanancin kishi da ita ballatana Amina datafi Tsayamata arai ganin itace yarinya sannan kuma Amarya.
Sosai take ta shagwabanta shi kuma yana lallabata Dalilin haka ne ma yasa har yau bai kira Amina ba Saboda ai sun yi mgana da Hajiya washegarin Ranar data koma Gumel a wayar Nazir Saboda ya cika alkwari yaje ya kwana Daya Ranar Litini da Safe ya hau Jirgi ya koma hankalinsa ya kwanta daya ga Hajiya lafiyanta kalau Cikin koshin Lafiya.
Da farko kafin Bullowan Cikin jikin Amina har ya fara Cuku cukun nema mata Takardan Zama madina sannan har sun yi shawara da Aliyu kan zai shigar da Takardan kan zai karbi Gidan malamai na makaranta Saboda gidansa yayi musu kadan sai ya saka Amina ana Cikin makaranta,Sai kuma ga wannan al"amarin da hajiya tace ya Dakatar da komai Shiyasa ya dan Samu Sauki ya fara shirin Tahowa saboda Sakina sannan uwa uba Amina yana son yazo ya ganta Tunda ya tafi bai fi sau hudu sukayi mgana ta waya ba sannan Sakina duk sanda sukayi mgana ta Dinga mai kuka keman tana fadin yazo ya tafi da ita Tsausayinta yake ji ganin halin Datake Ciki yasa yayi mata alkawarin zai zo nan da wata Biyu zai zo sai su koma Tare Umra yake so yayi shiyasa ya Dakata da Tafiyar Sannan Sarood ma tayi Damara sai taje kuma in yace bazai je da ita yayi rashin adalci ko Iyayanta sai sun ga rashin adalcinsa...!
Tunda suka yi mgana da Hajiya tace kada ya sanar ma kowa ko Aliyu bai Fadama komai ba yadai Fadamai laluran nan tasa Allah ya basa waraka da Taimakon shawarwarin mallam Daganan kuma sun ma Dade basu yi mgana ba daya kirasa sai ya Fara mai Tsiyan ya barsa ne yaci amarcinsa da yar Balarabiyarsa Danmallam Tsaki kawai yake yi da Dariya domin ba karya yana fa shan amarci.
Sai da Amina tayi kwana Goma A Abuja sannan ya nemi wayarta da lambar da Jafar ya Dade da Turomai sai kuma ya kara jin wayar a kashe bai ji Dadi ba in yace Amina bata aransa yayi karya abubuwa ne suka sha mai kai sannan da Tazaran Dake Tsakaninsa da ita da rashin shakuwa da kuma Basu wani saba da juna ba.
Aisha ya kira kawai saboda ko ya Kira Hajiya bata kusa da Amina.
Daman duka kannensa suna kiransa awaya suna gaisheshi lokaci bayan Lokaci Haka suke basu yar da tarbiyan gidan mallam ba ko da yayyinsu basa kusa dashi suna Kiransu a waya suna Zumunci dasu Lokacin Ba'rin Sakina sun ta Kiransa suna mai Jaje.
Lokacin da yake tambayan Aisha mganar yaji wayar Amina akashe ya Aisha tace bata sani ba ammh Zata tambayi Aminar taji tunda ita tama manta da mganar wayar sannan batama Taba ganin Aminar da wayar ba.
Yace to ta fadama Amina yana son mgana da ita ta kuna wayarta Ya Aisha ta amsa da insha Allahu zata Fada mata ya tambayeta ya jikin Aminar..?
Ta sanar dashi lafiyanta kalau sai godiya Zazzabin Dare dai take fama dashi sai amai sannan bata iya cin kowani abinci sai Tea sai Kuma wainar Fulawa,Komai Taci baya Zama sai ta Amayar dashi sai yaji Tausayinta gata yarinya ga shi ya Dora mata nauyi sun yi mgana da ya Aisha sosai ya sanar da ita suje asibiti tace eh Usman ne yace ta bari ya Dawo yaje Kaduna wani aiki Da haka suka rabu..
Suna gama wayar Aisha ta nufi Dakin Yakaka tana shiga ta iske Amina Zaune saman Cafet tayi Daidai tana cin wainar Fulamai mai manja da Saude mai aikinta tayi mata Tun Safe bata ci komai ba Tea din ma yau taki sha ita sai Wainar Fulawa Shine Yakaka tace Saude tayi mata Wainar Fulawan har Sauden tana Dakin ne suna ta Hira Yakaka na basu labarin Cikin kakan su Usman har ta Haihu kanwa ne abincinta sai da bakinta ya Lashe saboda Cin kanwa tana Fadama Amina ta godema Allah tayi ma Ciki mai kyau tunda batayi mugun laulayi ba sannan ta iya shan Tea da Cin wainar Fulawar tayi kyan ma Laulayi.
Amina sai cin abunta take yi tana Dangwala yaji tana Sanye Cikin Bakar Doguwar riga cikin kayan ya Aisha ne da ta bata take sakawa tunda kayanta sun Daina Shigarta Cikin fa Kiba kawai da Budewa yake saka Amina ta bari ne Usman ya dawo su je asibiti da kasuwa ta siyo ma Aminar Dogayen Riguna tunda duk ta bata na wajen nata sannan sun ma Aminar karanci.
Chapter 47 · 0% Book details