← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 105

Sashe 30

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajiyar zuciyar daya sauke har sai da ta jisa a kunnenta Dayaji muryanta sai yaji Salama da natsuwa Cikin Taushinsa yace"AMINA...!
sai taji kamar yafi kowa iya Fadar sunan nata jin yadda ya kirata ita bazata iya tuna ko yama taba kiran sunanta ba Haka ba, jin tayi shuru yasa ya kara cewa"Amina kina lafiya..?
Cikin Sanyin Jiki tace"Na"am..eh lafiya kalau..!"

"Ya jikin ki..? Ina fatan kin warke babu kuma inda ke miki ciwo..?
Ya fada kai Tsaye domin baya Fatan ace wani abu kuma ya tashi bayan Tafiyarsa kunya ta kama Amina ta Dukar da kanta kamar yana ganinta ta kasa mgana sai gabansa ya Fadi da Sauri yace"Ko da wata matsala ne..?
Da Sauri tace"A"a na warke..!
Afili ta Furta"Alhamdulillah..!
Kafin yace"Naji Dadin haka ina Fata kamar yadda kikamin alkawarin baki gayama kowa ba ko..?
Sai da ta gyadamai kai kafin tace"Eh ban fadama kowa ba..!
Cikin jin Dadi yace"Dakyau naji Dadin Haka..Ya karatu fata kina maida Hankali wajen karatu..?.
Da Sauri tace"Eh yau ma mun yi Hutun Hadda..Gobe ma zamu Fara Jarabawa a boko..!
Kai ya gyada kafin yace"Allah ya bada sa"a..ki rika maida hankali kinji ko..?
Ta gyada kai ya cigaba da Fadin"Sannan ban da wasa ban da Fada ban da gujeguje ke yanzu ba yarinya bace kin tashi Daga su Hamida ke matar aure ce ba Daya kike Dasu ba kina jina ko..?
Nan ma kai ta gyada mai yace"Baki da baki ne..!
Ba nace ki daina min mgana Da kai ba .!
Da Sauri tace"Naji insha Allahu..!
Ajiyar rai ya Sauke kafin yace"Kina Bukatar wani abu..?
Tace bakomai kai Tsaye yace"Ki rika gaida Sakina in kun hadu tana gaba Dake kinji ko..?
Amina ta Tura baki kafin tace"Ni fa in na ganta batamin mgana sai tayi ta Hararana har zagina ma tanayi..!
Cikin mamaki yace"Ita Sakinar..?
Amina tace"Eh shiyasa nafi son zaman nan fiye da chan sannan achan ina jin Tsoro da Daddare bana iya barci don Allah ka Fadama Hajiya ta rika barina ina kwana anan in ka Dawo sai na koma achan..!
Kawai sai ta sakamai kuka sai yaji Hankalinsa ya tashi meke Damun yarinyar nan ne Cikin Tausasa Murya yace"Naji ki daina kuka zan mata mgana..Daman baki daina Firgita cikin barci ba..?
Tace mai eh sai da yayi shuru kafin yace"Ki samu mallam yau da Daddare in ya natsu ki Fadamai abunda kike jin in zaki Firgita kin ji ko..?
Tace"Na Fadamai..?
Yace"Eh ki Fadamai sannan mganar Zagin ki da Sakina ke yi kada ki Fadama kowa har su Hajiya zan mata Fada insha Allahu zata Daina ke dai in kin koma gidan kun Hadu ki rika gaisheta saboda ko bakomai Tana gaba Dake kuma a islamiya an koya muku yin biyayya ga na gaba da ku ko ba Haka ba..?
Tace eh ya cigaba da fadin"To ki rika bata girmanta kin ji ko..?.
Ta amsa da toh bai Tsawaita mganar ba yace"Zan ce ma Jafar a Cefanan wannan watan ya siya miki Goldenmorn da Cornfkles Saboda Saukaka miki Wahala sai ki Rika sha in zaki tafi makaranta..!
Tace "To nagode..!
Ya amsa ta da Fadin"Kada ki damu komai kike Bukata kada ki tambayi Hajiya ko mallan ki yi ma Jafar mgana ko kuma ki Dauki wayar Hajiya ki kirani kinji ko..!
Nan ma tace mai da toh tagode Dagnan yace ta maida Hankali a karatunta ta amsa mai Daganan ya mata sallama ya kashe wayar.
Tabi Wayar da kallo Tana Tura baki wai ta rika gaida Sakina Tab wannan mara mutumcin ne zata gaisheta..
Shi kuwa sai da sukayi mgana yaji Hankalinsa ya kwanta har ya natsu ya Cigaba da Duba Takardun Dalibansa da sukayi gwaji.
Da suka gama wayar kunya ta Hana Anina fitowa sai da Hajiya ta Shigo Daukan abu ta ganta zaune tayi shuru tace"A a Mamah tunda kun gama wayar ki fito falo hanne na jiranki mana sai ki zauna ke kadai..!
Jin haka yasa ta mike ta mikama Hajiya wayar, ta karba ta Fice da Sauri Hajiya ta bita da kallo tana Mirmishi a Cikin aranta tana Fatan addu"an su Allah ne ya karba na amitar da Ruhin Amina da Danmallam waje daya.

Amina na fita Hanne ta taso tana Tambayanta da wa tayi waya Amina ta balla mata Harara kafin tace"Bansani ba..!
Hanne na Dariya tace"Nasani Ya Danmallam ne..ko..?
Amina ta mata wani kallo kafin tace"In ma shine sai na Fada miki..?
Sirrin miji da mata..!
Hanne ta saki Dariya kafin ta Ja Hijabinta tana fadin"Bari naje na gayama Hamida..Sabon Update..!
Amina tayi Tsaki kafin tace"Ai ke Hanne mijinki ya shiga uku..duk wanda ya aureki ya auran ma kansa sai kin hada Fada a Family din mijinki Saboda munafuncinki..!
Hanne bata bi ta kanta ba ta fice Amina tayi zamanta Falon Hajiya chan sai gasun dawo Tare Hamida sai kara maimaita abun da Hanne ta gayamata take yi Amina ta musu wani banzan kallo kafin tace"kusan dai ni yanzu ba Sa"arku bace ko..?
Igiya uku ne akaina..Taimaka muku ma nake yi ina yawo da yara. !
Hanne da Hamida suka saki baki ganin haka yasa ta Musu gwalo tatashi da gudu ta Fada Dakin su Hanne Tana Dariya suka mara mata baya suna fadin yau sai ta gayamusu su waye yara..?
Ranar dai anan suka wuni Shashen Hajiya suna abunda suka saba sai bayan sun dawo islamiya ne Hajiya ta saka aka maida Amina gida tana kunkuni Tana komai bata samu yima Baba mallam bayani ba sai washegari da suka dawo makaranta ta Fadamai ya Dade yana mamaki ya tambayeta yaushe ta fara tsorata tace tun tana karama ta dade mallam ya Dinga Fadin Sakacin mamanmu da Aba da Amina na Fama da wannan Laluran ammh bsu sani ba Hajiya ce ma ta Lallasheshi ya bar mganar da yace har Aba din sai ya kira da mamanmu ya musu Fada.
Shi ya Rubuta mata addu"o'i ya bata yace ta Rika karantawa Duk Dare in zata kwanta Tare da Sauran addu"an barcin da Annabi ya koyar damu.
Amina yadda Taga Mallam ya Dau abun ne yasa itama bata Dauka da wasa ba sannan Danmallam ma sun sake mgana da wayar Hajiya Data Fadamai yadda sukayi da mallam ya mata Fada kan ta Dage kada wasa ya Dauke mata Hankali ta rika kwanciya bata karanta su ba.
Shiyasa ta Dake bata kwanciya sai ta karanta sai gashi kuma Cikin ikon Allah tunda ta Dage sai ta samu Saukin Firgita din sai abunda ba"a rasa ba Danmallam har da mallam sun yi mgana Mallam nata fada yana Fadin da Haka Umaima ta Fara gashi nan suna so su taba mata kwakwalwa Dannallam yana so ya Fadama Mallam bayan haka ma yana Zargin akwai wani abu Tattare da Amina sai dai kuma bai da Hujjan hakan ammh yana so sai in ya kara Dawowa ya Zauna ya Fahimci matsalanta Domin Ranar da abun nan ya Faru tsakaninsu da Washegarin nan da Safe yaga tana wasu abubuwan da Dole tana da wani abu a Tattare da ita.

*******

Kwantashi ba wuya a wajen Allah su Amina har sun gama Jarabawarsu sun yi Hutu taso ta zauna anan tayi Hutunta Hajiya ta hanata sai ta Roki Baba mallan kan su Hanne su Bita ko Sati Daya su yi da Farko Hajiya ta Hana sai da Mallam ya saka baki Sannan ta amince suka Tattara suka koma chan da Niyar Sati Daya zasu yi Saboda islamiya basu yi Hutu ba.
Mamanmu bata Damu ba da akace Hamida zata je gidan Amina Domin alokacin tana Tsakar Cin Duniyarta ne Domin komai tace Aba ya bata baya Gaddama Kudi yake sakar mata bana wasa ba ta zama Tauraruwa a wajen sa Mamanmu ta samu Cikar Burinta Fiye ma da yadda take fata shiyasa ta manta da kowa da komai ko Anty Amarya ta kirata bata ma kaunar Hakan gani take tana neman Takura mata Shiyasa Amina ma bata gabanta Ta barta da Anty Amarya chan itace Zatayi mganinta ita yanzu Sa"idu ne agabanta yanzu shawaran komai sai yayi da ita sai abunda tace koda yace Jafar yace kaza ya kamata ko Hajiya sai tasan yadda tayi ta Kushe mganarsu ta sauya da nata Shiga kawai take tana fita Daga kayan alfarma kamar wata Yarinya sannan Malaminsu tana sakarmai kudi sosai Domin ta yaba da aikinsa
Anty Amarya kuma tana nan tana Jiran gawom Shanu domin ta yarda da aikin Malam ya sanar da ita Nasara tatace shiyasa bata Damu ba ta koma ta Zauna tana jiran tsammani kamar yadda ta basa duka yardanta Shiyasa ko Sakina ta kirata tana mata Korafi take mata Fadan bata da Hakuri aiki nawa suka basa kuma ya Biya musu Bukata..?
To wannan ma ta Zauna ta Jira komai zai zama Daidai da yardan Allah abunda basu sani ba Daga wannan Lokacin aikin ya kuskure musu sannan zasu cigaba da jiran majirata ne Jiran da zai kai su ga Ranar Nadamar su da Tonon asirin su..!
Chapter 30 · 0% Book details