← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 105

Sashe 79

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na taso tun ina karamata ban taba ganin wani Namiji daya taba Burgeni kamar Shi ba,Tun tasowata shi kadai ne Namiji kwara Daya daya ke Burgeni Sannan na kamu da sonsa da kananun shekaruna batare dana sani ba,Sa"idu ya shiga raina yayi kane kanen da bazan iya rayuwa ba sai da shi Tun Lokacin suna Gusai kafin barowarsu chan su dawo nan Gumel da Zama saboda Sa"idu yasa ban taba Daga kai na kalli Samarin Dake kara kaina akaina ba ina ganin kamar zai so ni watarana sannan kuma Hankalina da duka Tunani ya karkata akansa shi kadai.
Sai dai me..?sai da girma ya fara kamani Sa"annina suna aure sannan na Fahimci bana gaban Sa"idu bai taba min wani duba ba sai na yan"uwanta duk da kaunar da nike ta Nuna mai a Fakaici in yazo garin yazo Gidanmu Tunda ni ina matsayin Diyar abokin wasan Marigayi Baba Aminu ne,yazo kaida Babani Lokacin Tana Raye bana iya sukuni na Dinga Bare baren jiki kenan a kansa bani da wani Sauran sukuni ammh bai Taba Daga ido ya kalleni ba ballatana yasan Halin da na Dade aciki alokacin har Babani sai da ta Fahimci ina son Sa"idu so kuma bana wasa ba.
Hankalina bai tashi ba sai da naji Zencen auransa ranar sai da nayi karamin Hauka Babani Allah ya jikanta ta Dinga Tausata ta bani Hakuri akan nayi hakuri na Cire Sa"idu a raina na bama wani Cikin Manema na Dama tunda dai Sa"idu bai Juyo gareni ba na Hakura dashi alokacin kamar in make Babani haka naji Sai dai ban nuna mata ba ammh a wannan gabar gaba nake kullawa ga Duk wanda yace na Rabu da Sa'idu ko waye shi kuwa..!
Auran Sa"idu da Hadiza kadan ne ya Rage bai kaini kushe wata ba Saboda Bakinciki da Zafin kishi har sai da na Fara Tunanin na kamu da ciwon zuciya ammh duk da haka ban makara ba sannan ban cire rai ba.
Ana cikin wannan Halin Babani ta amsa kiran Allah ta rasu dani a bakinta da Fatan na yi aurre kada na jirasa ammh ban jita ba Tunda ni kadai ce tare da ita bayan bakwai dinta sai kawu Salisu ya maidani babban gidanmu ina zaune a wajensa..!
Saboda Sa"idu da Soyayyarsa sai da Kaf sa"o"i na suka tafi gidan mazajensu har kannen baya na ma an fara aurar dasu a wanchan Lokacin ana auran wuri ammh ni nafi Shekara ashirin ko Tsayayyen mgana bata akaina Saboda bayan Sa"idu har Abada bana jin zan iya bama wani Namiji Dama.
Kwatsam Naji Labarin Haihuwar yaya da yadda Sa"idu ya dinga rawan jiki akanta da abunda ta Haifa sai Gyambo na ya Dawo sabo naji bazan iya Hakura ba,Da taimakon wata kawata Samira da mukayi Primary tare na Zayyane mata Damuwata tace ta kwana gidan Sauki ita ta Daukeni ta Fara kaini gidan wani malami ko Boka zan ce wanda ke mata aiki akan mijinta acikin garin Tsafe na ZAyyanemai Halin da nike Ciki ya Tambayeni me nake so nace Sa"idu nake so..Ya aureni ko ta Halin kaka ne yana so ko baya so ni ban Damu ba kawai Burina na ganni agidansa a matsayin matarsa..!
Yace an gama ammh zan zube kudi masu yawa na karin aiki ban Damu ba Daman ta Fadamin na Tanadi kudi alokacin wajen Biyan Bukatata komai zan iyayi Zoben Zinaren da na gada wajen Babani na Saida na yi amfani da kudin wajen jawo cikar Burina.
Kamar wasa sai ga karamar mgana ta Zama babba kawu Salisu ya Kira Sa'idu akan yazo yayi auran zumunci Dani alokacin ko gaddama bai yi ba ya Karbi mganar Daganan na Fahimci zama ba nawa bane samira ta Budemin ido da shiga malamai Domin Cimma Burina ban shiga Gidan Sa"idu ba sai da na saka aka kafani sannan aka Saka soyayyata da kaunata a zuciyar kowa banda ta Sa"idu domin bai kaunace ni Fiye da yadda nayi nazo ba,yafi kaunar yaya da Jafar d'anta data Haifa.
Wannan shine Bakinciki na Biyu dana taba Fuskata agidan Sa"idu bayan aurena dashi,Da Farko ina ganin Komai ya kare tunda na auresa ammh Daga baya sai na Fahimci zama bai ganni ba Duk da kuwa Daga Su mallan har ya"yansu suna so na da Girmamani Uwa uba kuma Yaya itama ta Sakarmin komai kamar yadda na nuna Dayan fuskata ta Salihai.
Na Dade ina Fama da kuncin zuciya da Bakimciki kauna da wannan Tsausayin da bana ganinsa akan kowa sai akan yaya ni kuma sai dai Zaman Tsausayi da yan"uwanta ka ban taba ganin wannan kaunar da nake son gani atare dashi ba Sannan sai na Fahimci Duk wani Buri na Sa"idu yana kan Jafar ne bashi da sukuni in yana gida yana Tare dashi ko da Ranar ni ke da girki sannan duk kokarinsa na yaboye wannan kaunar bata Boyu awajena ba Dalilin Dayasa Idona ya Rufe da Kishi kenan da Bakincikin yaya da ya shiga raina na har Abada.
Hankalina ya kwanta dana Samu Cikina na Farko ina Tunanin Namiji zan Haifa nima Sa"idu yayi rawan jiki akaina da abunda na Haifa sai dai kuma ina hakan bata Faru ba haihuwar ZULFA sai ya koremin wannan Burin nawa sannan kuma sai na Fahimci kamar Sa"idu bai yi murna da wannan Haihuwar ba Duk da yadda ya dinga min Hidima yaya da Hajiya na Tsaye kaina ban taba Gani ba Saboda gani nake yi Itace ta Hanani Samun abunda nake so tun Farko Sannan tasha gabana a zuciyar Sa"idu.
Na yi ta neman Samira domim mu koma wajen mallan sai na samu Labarin mijinta ya tafi da ita Lagos inda yake Neman kudinsa sai hakan ya katsemin hanzarina ban koma wajen maallam da wuri ba har Tafiya ta Cigaba da tafiya alokacin Yaya ta Haifi Jadwa da Jaleela ni kuma ina Goyon zahra kaf alokacin ni nake rainan duka ya"yan da yaya ta Haifa Saboda na kara jawo Hankalin kowa da Tunanin kirkina akansu kuma naci Nasara na zama ban damu da komai ba a Bayanne a boye kuma ba wanda ya kaini Bakinciki.
Hankalina bai kara tashi ba sai da naga na kara Haihuwar Zulaihat ban samu Namiji ba sannan ga Jafar ya girma sai nake ganin yaya ita ke da gida ni kuma ta barni bani da Tsuntsu ballatana ta tarko sai nayi Shirin komawa wajen mallam sai dai nayi Rashin Sa"a an ce ya tashi Daga nan kuma ba wanda yasan inda ya koma Hankalina ya tashi Saboda alokacin na kasa Hakuri so nake ko ta Halin yaya ne na sami mafita na gaji da Kunsan Bakim cikin Sa"idu da yaya.
Hakanan na Dawo gida tunda bansan wani Malamim ba sai dai kafin na Samu mafita zuciyata ta riga ta gama kekyashewa Tsanar yaya da ya"yanta ya gama Cikamin zuciya wannan Bakincikin Tun aurena da Sa"idu yake Cikin Raina bai Taba gushewa ba Sai Ranar da YAYA ta bar gidan Duniya..!
Mamannu ta karishe Fada tana gunjin kuka Mallam ya girgiza kai Cikin Wani yanayi yana Fadin"Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..!
Kafin ya karisa ya samu Daya Daga Cikin kujerun falon Hajiya ya Zauna Rawaninsa duk ya jike da zufa Aba kuma yana Durkushe inda ya Sulale kansa na kasa ba wanda yasan Halin Dayake ciki su Nasir da su Nazir kuma duk kasa suka sulale suka zauna jin wannan labarin mai kama da al"amara.
Su ya Jadwa da su Jaleela suma kafafunsu ne ya kasa Daukansu suka zube nan saman cafet suna Faman kuka kada su Zulfa su ji Labari gabadaya kowa da abunda yake sakawa acikin ransa Amina kuma na Rumgume jikin Danmallam Tana kuka yana faman share mata Hawaye yana Shafa bayanta Jafar kuma kansa ya Dukar kasa Hannunsa Daya Dafe da kan nasa ya kasa yarda da abunda yake ji kuma yake gani
Gabadaya kowa acikin Falon ka kallah sai ka Hango tashin Hankali da al"ajabin wannan abunda dake Faruwa.
Mamanmu ta Dago Jajayen idanuwanta ta Sauke kan Anty Amarya da jikinta ya fara rawa sai alokacin ta Fahimci Komai fa ya kare sai dai babu wani tsumi ballatana Dubara.
Cikin Muryan kuka da Nadama Mamanmu ta Cigaba da Fadin"Ban taba Sanin bayan ni agidan Baba mallam akwai mai irin Halina ba Sai daga baya..Har ga Allah da Farko bansan Haka marliya take ba sai da watarana na jita tana waya da malamin Dake mana aiki kan Hajiya da mallam alokacin nasan itama irina ce..muna neman abu Daya agida Daya sannan alokaci Daya..!
Ban nuna mata na jita ba Sai daga baya,Na koma na nuna mata fuskata na bayyana mata Duka Burina da Fatan zata bani Hadin kai mu cure waje Daya wajen Cikan nmu burin..!
Tafada tana kallon Anty Amarya da kallo ya koma kanta komawa tayi ta Zauna Dabas saman Cafet sai kuka Cikin wani yanayi ta cigaba da fadin"Alokacin da Balaraba ta zo min da wannan bayanin na tsorata Saboda ko ni ban taba Tunanin haka take ba..Ammh data zauna ta warwaremin komai sai na Fahimci Rauninta nima ina Cikin irin haka..Sannan in muka Hada Hannu zamu cika namu Burin atare..!

Mallam Dake zaune yana jin abun al"ajabi ya Bude Bakinsa Cikin wani yanayi yace"Ke menene naki Burin..?
Burin daya sa kika fifita Duniyarki Fiye da Lahirarki marliya. ?
Chapter 79 · 0% Book details