← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 105

Sashe 26

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shigowarsa kenan Cikin kayataccen Office dinsa mai girma da Fadi yana Hawa na Hudu ne a bangaran ofishin Malaman makaranta ta Madina bangaran Shashin Qur'an and islamic Studies babban Shashi ne mai Dimbin Tarihi a cikin babbar Jami"ar ta Musulunci Dake madina.
Littafan hannunsa ya zube bisa Babban Tuburin dake cikin Ofishin kafin ya samu waje ya zauna Hular kansa ya cire Lokaci daya yana shafa Sumar kansa data fara Tohowa.!

Gajiya ce ajikinsa domin yau tun Safe ya bar gida yana da ajin karfe takwas na Safe zuwa goma sannan bayanan ya shiga na goma zuwa sha biyu daganan kuma suna da meeting da zasu yi na malaman shashin Dayake koyarwa gabadaya
Sakamakon yau Alhamis ya tashi da azumin Lada kamar yadda ya saba so yake ya tashi ya isa babban masallacin Cikin makaranta yayi karatun Qur"ani kafin lokacin Sallah yayi ammh ya kasa tashi kasala Tare da Gajiya sun Taru sun lullubesa.
Kansa ya kwantar kan kujeran Dayake zaune idanuwansa suna lumshe kamar mai jin barci nan kuwa ba barci yake ji ba Tsabar Tunanin abunda ya faru tsakaninsa da Sarood jiya da Daddare ne ya Addabesa
Shi bai taba Daukan matsalan sa da Sarood mai girma ba sai jiya daya kara jaraba Kusanta ta abu yaci tura kamar dai baya da ya riketa ajikinsa tafiya ta fara tafiya sai yaji komai ya koma ya kwanta a duba da abunda ya faru tsakaninsa da  Amina ya Dauka Komai zai yi daidai tsakaninsa da Sarood sai kuma yaga akasin haka,Bai taba Daukan abun da Serious ba sai jiya Saboda abun kamar zai yuyu sai kuma abu yaki yuyu shiyasa wani Lokacin baya son rabarta kar yajamata matsala tunda ita macece Tana da Rauni Fiye dashi sannan shi yana da wata matar ita fa..?
Shi ne kadai mijinta kuma Wanda zai Biya mata Bukararta in ta taso.
Ajiyan ya dauka komai yazo karshe Ganin yadda abun nasu ya fara kamar gaske sai dai ina Yana zuwa gabar sai komai ya kwanta yaji bai iya Tabuka komai abaya ya Dauka Sha"awan ce ke Daukewa shiyasa girman nasa bata Mikewa alokacin ammh Daga Jiya ya fara Zargin da wani abu Saboda shi kanshi yayi mamakin yanayin da ya shiga jiya da Taimakon addu"a ne kawai ya iya Sarrafa kansa.
Sarood kuma kwana kuka tayi bai ga Laifinta ba tayi hakuri wajen wata bakwai ba wani labari Tabbas akwai Cutarwa acikin zamansa da ita Dakyar ya samu ya lallasheta bayan ya mata alkawarin zai Binciki kansa Domin ya sama musu mafita da wannan Tunanin ya barta agida ya fito zuwa makaranta ya kasa samun Mafita,ya rasa da wa zai Tattauna wannan matsalan da Farko kamar ya Kira Mallam kunya da nauyi bazai barsa ba yayi Tunanin Baba Sa"idu kuma sai ya fasa Tuna yanzu ba Da bane..In abaya yana yayansa ne yanzu har da karin Surukanta Tunda ya aura masa yarsa ta Cikinsa da Kunya ya Kirasa yana Fadamai bai iya kwanciya da wata mace Abokiyar zaman yarsa duk da yasan Waye Baba Sa"idu auran Amina bazai taba Chanza Tsakaninsu ba Sai dai shi din ne Bazai iya ba yana jin nauyi,Hajiya kuma ba wannan Sakewar Tsakaninsu,koda ma akwai ita uwa ce bazai taba iya fadamata wannan mganar ba Aliyu ne ya fadomai arai aboki kuma Amini garesa da shi kadai ne ya kamata ya Tattauna wannan matsalan dashi.
Shawaran kiran Aliyu ya Zauna aransa bai Tsaya ba ya tashi Zaune Dakyau ya Fiddo wayarsa cikin Aljihun Wandon Pakistan din Dake jikinsa kafin ya kira lambar Aliyu layin Amina ya kara kira wanda Jafar ya Turo masa ammh kamar kullum ana Kara fadamai wayar tana kashe ne. damuwarsa ba Daya bace har da Damuwar rashin jin Aminaa har Jafar ya sake kira a jiyan yana kara tambayansa ko ya kaima Hajiya wayar..?
Jafar ya kara Tabbatar mai da wlh ya kaima Hajiya wayar ta kuma Ta tabbatar mai  zata bama Amina wayar sai dai baisan meyasa har yanzu bata bata ba ammh zai je ya mata mgana sai Danmallam din ya hanasa yace zai kirata da kansa shi kanshi Jafar yayi mamakin yadda Danmallan din ya Damu da sai an bama Amina waya wannan yarinyar da baisan yaushe zatayi Hankali ba ko Shekaranjiya ya ganta sun dawo islamiya suna tafe ita su Hamida sai Mgana take cikin ihu Suna bakin masallaci kofar gidan Baba mallam har sai da Nasir ya kada baki yace Amina in aure bai gyara ba to bazata taba yin hankali ba shima ya yarda da mganarsa..!

Bai kira Aliyu ba kamar yadda ya kudira daga farko sai ya maida akalan kiran nasa ga Hajiya, mallam sun yi mgana dashi da Safe agogon Dake kafe a afishin nashi yabi da kallo yaga karfe 12 da wani abu na rana yana Tunanin achan Nageria yanzu Tara ne da wani abu na Safe.
Wayar Hajiya ta shiga gabda zata katse ta Daga kiran cikin Sallamarta ya amsa mata Cikin Ladabinsa kafin ya Fara gaisheta ta amsa tana Fadin"Lafiya lau Danmallan ya madinar da wajen aikin ka..?
Ina Saratu ina Fatan tana lafiya..?
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"Duk muna Lafiya Hajiya..aiki kuma alhamudulillah cikin Nasara da addu"arku..!
Hajiya tace"Masha Allah Allah ya taimaka..Allah ya kare ka Dammallam ya baka Zuru"a Dayyaba..yadda kake mana Biyayyah Allah ya jikan ka ya baka mai jin kanka kaima..!
Addu"a hajiya yasa yaji kamar yayi kwallah kaunar Mahaifiyar tasa na kara shiga ransa.
Cikin muryan sa mai cike da Zati da Haiba yake amsa mata da Ameem Ameen.
Mallam da mutanen gidan ya tambaya tace duk suna Lafiya kafin yace"Hajiya yau she ne tafiyarki maiduguri.?
Hajiya tace"Satin na sama ne zan tafi inaga Ranar Laraba..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kaimu zan turo ma Jafar sako..Ki kaima Goggo ta kara Allah ya bada zaman lafiya..!
Hajiya cikin Farinciki tace"Angode Allah ya kara Wadata Allah ya Dafa maka..!
Ya amsa mata da Ameen kafin su yi shuru na wani Lokaci jin shurunsa yasa sai ta Fahimci yana so yayi mgana ne.
Cikin Dattakonta tace"Danmallam me kake so kace ne..?
Ya sosa kansa kamar tana gabansa kafin yace"Hajiya jafar yace ya kawo miki waya ko..?
Hajiya tayi yar Dariya kafin tace"Eh wlh ya kawomin tun kwanaki na Shafa"a ne ban bama Aminar ba..Dayake bata zama Da sun Dawo makaranta abinci kadai suke ciki sai su tafi islamiya da sun dawo kuma nake sawa akaita gida ni kuma Shaf na manta..Ammh bari in ta Dawo yau zan bata insha Allahu..!
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"To nagode Hajiya Allah ya kara girma..!
Ta amsa da Ameen Daga haka sukayi sallama Hajiya ta zauna gefen gadonta Tana kara nazarin meyasa Danmallam ya Damu da Amina ta rike waya Daga baya alhalin ita ta kawo Shawaran siyan waya Daga baya da suka Tattauna da mallam sai ya nuna mata illar hakan saboda Har yanzu Amina yarinya ce sannan Karatu ne agabanta,in ta rike waya yanzu zai Shagaltar da ita daga karatunta in Saboda su rika mgana da Mijinta ne ga wayarsa ko ta Hajiya duk wacce shi Umarun ya kira zai yi mgana da Amina shiyasa bata maida kanta kan bama Amina wayar ba ko ayanzu ma Datace mai zata bata tadai cemai ne kawai ba domin zata Tsallake Shawarar da mallam ya bada ba.!

Danmallam kuwa suna gama waya da Hajiya sai ga kiran Sakina ya shigo Yana ma kokarin kiran Aliyu ne kamar bazai Dauka ba sai kuma ya Kashe ya Kirata Tuna yau kwana Biyu basu yi mgana ba Shifa har yau Haushinta yake ji kan abunda tayi mai In ya tuna yadda ta kulle ko"ina ta tayi tafiyarta shi abu daya ya Damesa yadda ta tafi ta bar yar Mutane acikin gida in da yunwa ya kamata ko kuma wani abu ya Sameta ai da ya shiga uku wajen Hajiya da mallam kila sai sun kusa mai baki.
Sama sama daman yake da ita in ya kirata shima saboda sauke Hakki da Nauyin Dake kansa ne ba da domin haka ba sai ta kara Raina kanta.
Chapter 26 · 0% Book details