← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 105

Sashe 52

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yadda Aisha tayi ma Hajiya alkwarin ta kuma ta gayama Amina bata  sauya Shawara ba Haka take tasa keyar Amina Kitchen in suna Girki da Saude ta rika gani tana koya mata Saukakkun girke girke,Tun Amina na Tura baki tana kunkunin tana barcinta ya Aisha na takura mata har tazo ta saki ta Fara maida hankali To Saboda ko ta koma Daki Yakaka ke Fatattako ta dole ta Dage tana maida Hankali ballema ya Aisha data koyi Fada tunda tayi aure.
Haka Zata Zaunar da Amina tana koyamata yar shagwaban nan da yadda zata rika ma ya Danmallam mgana da karaiyaya Amina sai ta Dinga Dariya aranta tana Fadin a ina ya Aisha ta san wasu abubuwan agidan kamar in ka samata Hannu abaki bazata Cija ba Kamar ya Aishan tasan abunda take Tunani ta Dunkure mata kai tana fadin"Ban son iskanci ana koya miki yadda zaki zama Tauraruwa wajen ya Danmallan kina Iskanci ko..?
Nasan kina mamakin ina duk nasan wadanan abubuwan ko..?
To ai gidan aure makaranta ne Amina sannan tunda ya siyamin babbar waya nake dan shige shige ina koyan wasu abubuwa sannan Addini ma ai ya koyamana yadda zamu yi mu"amala da kowa har da gidan auranmu..!
Amina ta jinjina kai Domin tana ganin  yadda ya Aisha ke yi in ya Usman yana gari kwalliya da salon mgana da kwarkwasa duk tana gani kuma tana Dauka Domin a Zahirin gaskiya itama tana so ta zama mace sannan tunda ga inda kaddara ta kaita ai sai ta Dage Uwa uba kuma taci Uban Sakina ta nuna mata nasu ba irin nata bane Sannan bazatace ta fara son ya Danmallam ba ammh sun fara Shakuwa da juna tunda koyaushe suna Tare a waya kullum Cikin Tambayar baki da wani Damuwa ko.?
Yau da gobe bata bar komai ba sannan ita ai Zuciya tana son mai kyautata mata Amina tana da Budaddiyar zuciya ne shiyasa nan da nan mutum ke Shiga ranta abunda bata sani ba shi ya Danmallam ai jinin jikinta ne shi da take Dauke da Kwansa acikin jikinta,Sannan kuma ba kamar Soyayyarsu da Aminu bane,da ba Sakewa Cikin Tsoro da Fargaba tayi ta wannan kuwa a sake take sannan in suna waya sai tarika jin wannan fa ai mijinta ne wani abu ke shiga ranta batare data sani ba.
Sannan abunda ya Faru Tsakaninsu ya Haifar da wani bond mai karfi wanda Bawa bai isa ya hasaso farkonsa ba ballatana karshensa ba abu Daya ta saani tana jinsa aranta sannan tana Kishi da Sakina daman chan tana jin haushinta balle yanzu da suka Hada miji ko sunanta taji sai ranta ya baci bata ma Damu da balarabiyar nan yadda ta Damu da Sakina ba.
Ko kwana Daya yayi bai kirata ba ta Dinga fushi kenan tana Tura baki in ya Kira taki Dauka Sai Yakaka ta mata Fada da cewa"Tsiya na Dake Sarkaci Takwara..Haka ake karban miji a Hannun kishiya..?
Amina na hura Hanci tace"To bashi bane Jiya fa bai kirani ba..!
Yakaka ta aika mata da Dakuwa tana Fadin"Kin ga naki nan..?
Don bai Kiraki ba sai me..?
Ai kinsan yana da uzuri ko..?
Kada ki Dauka sai ki barma ita balarabiyar ki koma baya ke ko yan Dubaran nan na yaran Zamani da suka iya su Tadama Mazajensu hankalinsu in suna nesa saboda su zo wajensu da wuri baki iya ba,Sai Sakarci da Kunkuni kadai kika iya..!
In yakaka ta fara fadanta bar mata Dakin Amina ke yi abunta ranar kuwa sai taja mai aji Zata Daga kiransa in kuma ta Dauka yana mgana ta basar dashi yasan Laifinsa sai yayi mirmishi yace"Amina kiyi hakuri..!
Sai ya fara fadamata Uzirinsa sannan Zata Hakuri koda yaushe Cikin Tambayanta lafiyanta yake yi tana Bashi amsa ba wata matsala bawani Hira suke ba na ma"aurata ba sai dai suna Hirar abunda ya shafi mganar da Amina ta Fadamai koda yaushe sai tace mai yaushe zai taho Ranar dai yace mata"Cikin karshen watanan..Sannan yana so yazo da Sarood su yi Sati Biyu sai su koma Tare da Sakina..!
Ai Har suka gama wayar Amina bata kara Dariya ba wani Tukikin Takaici take ji wato zai zo da wannan balarabiyar sannan ya koma da Sakina ita ko Oho..?
Sai kuka da Ya Aisha tazo ta ganta Tana kuka Har Hankalinta ya tashi ta Zata ko jikin ta ne take jin wani abu..?
Sai Amina na kukan ba Hawaye tsabar Takaici tace"ba ba..ya Danmallan bane yace wai zai zo da balarabiyar matarsa ba..Sannan in sun tashi tafiya su koma da wannan gajerar matar tasa..!
Galala Aisha ta Saki baki tana kallon mgana kafin ta Tsintsire da Dariya Amina ganin haka yasa ta kara bare Baki ya Aisha ta buge bakin tana Fadin"Kefa ko ya'ya Dubu Zaki haifa na tabbata wannan iskancin naki bazai barki ba..Miye na bare min baki kmar na yankaki Salon yakaka Dake Daki Taji tace nayi miki wani abu..!
Amina ta hura Hanci kafin tace"To bake bace ina gayamiki mgana kina min Dariya ba .!
Ya Aisha ta matso ta kama Hannunta tana Fadin"to na bari kanwata gayamin yaki keso ayi..?
Amina tace"To ni kada ya tafi da Sakinar nan gaskiya..ni fa kadai zai bari anan kuma sai ya Dade kafin ya Dawo. !
Ya Aisha tace"Yanzu waya isa ya hansa tafiya da matarsa Amina..? Ai bamu isa ba matarsace kuma kinga Daman achan take sannan duk keki keda matsala ina nan ina Koya miki irin  kissar da zai saka Miji yazo gareka bai sani ba kin ki Dauka nace miki watarana ki sakamai kuka kice cikin ana Miki motsi ke zaki mutu ki Tadamai hankali yayi lallashi ki kinyi Shuru Da gudu zai taho ma Lokacin Tafiyarsa bai yi ba ammh sai ki kalleni kina Dariya..,!
Amina tace"To ai kunya nake ji..Kuma kuma..!
Ya Aisha tace"Kuma me..?
Amina tace"to ai naga shi babba ne. !
Dariya ya Aisha tayi kafin tace"to ai ke kin ji Dadi ma baki san sirrin auran irin su ya Danmallan ba..?
Gaki da kuruciyarki Amina da Shagwaba da Yarintarki zaki sacemai Zuciya shi kuma ya lalace akanki Wlh irin ku an fi sonku kiyi ta Jidalinki yana lallabaki shiyasa na Fada miki shima wannan Jidalin naki aikwai Inda ZAI miki amfani balle nasan shima ya Danmallam din ai yana son soyayya..!
Amina tayi Dariya "To kuwa matarsa bata iya ba..bandai sani ba ko wannan Sarood din..!
Ya Aisha tace"Ke ya akayi kikasan bata iya ba..?
Amina tace'Tab ai na Zauna da su..!
Aisha tace"ai bata iya komai ba sai Fadin rai ita kuma wannan Sarood din naga kamar ta Biye mata sun maida ta wata wawiya ma..!
Amina tace"ai kamar ma wawiyar ce..!
Dunkure mata kai ya Aisha tayi tana Dariya tana Fadin"Tunda ke kin iya sai ki Dage ki rikitamana yayanmu.!
Amina taji kunya ta kasa mgana.
Tundaga ranar ta Bude kunne tana kwasan Abubuwa awajen ya Aisha Da gaske take yi duk sai ta nuna ma su Sakina basu iya komai ba Aminene ai Ta musu Zarra.
Bangaran karatu kam sai da ya Aisha tasha mamakin Amina ba inda baza"a bude mata a Qur"ani ta karanta ba Hadisi kuwa tunda ga na farko har na bakwai suna kanta sannan ta haddace Arba"una Hadith sira ma haka Tajwid wasu Littafan Ya Aisha mamakin Amina ya isheta sai da ta Furta mata tace"Yanzu daman Amina kin iya wannan duk abubuwan kike iskanci a makarantar islamiya da Haddda..?
Amina Dariya kawai tayi tana Fadin"ai ya Aisha ba kowani Hali muke sani na mutanen da muke Tare dasu ba..Muna sanin wanda suka bayyana mana ne..!
Ya Aisha ta jinjina kai tace ba Shakka ko bangaran Boko sai da ta Kusa raina kanta sun yi kunsan mintinaa Talatin suna hira da Usman Cikin Harshen Turanci Amina bata kage ba sannan ba Turancin yan koyo ba Turancin ya Zauna abakinta sosai har Usman sai da yayi mamaki yace mata"Amina fa tana da kwakwalwa..In ta samu cigaba da makaranta sosai zata Zama wani abu watarana. !
Ya Aisha ta jinjina kai tana Fadin"Agida ko sai kace bata gane komai..Bama Damuwa tayi da karatun bafa..!
Dariya yayi yace"ai irin su sun fi raina ma mutane hankali da basa ganewa nan kuwa sun fi kowa Dauke komai Lokaci Daya..Muma lokacin muna Secodary sch muna da wani Dan ajin mu haka mai suna yahaya kamar wawa fa ana karatu yana wasa wlh a Exam shine Overoll..!
Ya Aisha tace"irin Aminace..A aji Dakikiya a Result sai kaga ta Doke kowa ko su hanne Dake maida hankali Tana gabansu..!
Usman yace"Da yawam irin masu baiwar nan basa samun masu Courage dinsu ne in ana kushe su ana cewa basa yi sai su boye baiwarsu sun fi bayyanasa wajen wanda ya yarda suna da ita kanta baiwar..!
Ya Aisha ta jinjina kai domin tagamsu da hakan yanzu sannan baba mallam koda yaushe Cikin Fada yake Uwata yar baiwace nan gaba sai mun baku mamaki aiko gashi ta bata yau wlh Bata Taba jin Amina tayi Turanci ba Duk azatonta batajin komai sai Tsinta tsinta.
Daman haka Lamarin Allah yake Tsammanin Abunda baka Tsammani ba..!

*******

Bayan kwana Shida..!
Chapter 52 · 0% Book details